KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Iyakar sa da ita shine gaisuwar safe abincin sa ruwan wankar sa sai wasu ayyukan sa da ya zama dole akan ta sai dai in tayi zaman kukan ta ya zo ya same ta ta rinƙa tmbyr sa ko tana da aibu ne shi kuma sai ya kalle ta kawai baya amsawa..

A iya zaman su fifi bata ƙara marmarin komawa sashen su Ammy da zama ba sai dai ta je ta gaida su a ɗan yi hira kaɗan da bai wuce mintuna goma zuwa goma sha ba daga haka zata tashi ta koma dan ta sakawa ran ta bata kuma nemar shawarar kowa dan inganta rayuwar ta tunda ta yi hakan a baya bata sami nasara ba..


Yau tana zaune a parlor sai ta ji taba sha’awar kwana a ɗaki dan duk wannan zaman nasu a parlor take kwana bata wuce nan ko dai dai da rana ɗaya Marshall bai taɓa yi mata tayin ta zo ta kwanta a bedroom ba ita kuma bata taɓa tmbyr sa ba amma yau ta ƙudiri kwanan ɗakin..

Akwai ranar da yake nuna mata wasu kayan coffee da ya sa aka siyo mai akan in zata rinƙa haɗa mai ta rinƙa amfani da su,a ranar take jin wai matar sa tayi extending dawowar ta zuwa lkcn da ta kammala abubuwan da take son yi..

Haka kawai Ta ɗan ji wani abu a ran ta da ta tuno cewa yana da mata,dan dama ita kam shaf take mantawa,yau da ta tuno sai abun ya mata wani iri,badon tanajin tana son sa ko zata so sa ba,tunani take ita wa zai so ta ya bata kulawan aure da kowacce mace take samu?babu khalid ga hamidarta ma ta juya mata baya.

Wani irin damuwa ne ya shigeta sam bata san dalilin wannan abubuwan dake faruwa da ita ba..

Tana zaune a parlor tana tunane tunanen ta sai sallamar Marshall ya doki kunnen ta,ɗagowa ta yi ta dube sa sai ta mai barka da dawowa kamar kullum shima sai ya mata barka da zama..

Saɓanin da yau sai ya zauna tare da ita a parlorn a kan wani kujera yana kallon ta sai ta ɗan tsargu har ta kasa yin shiru ta ce
“In kawo maka coffee ɗin ne yanzu”!!shi dai kallon ta yake bai ce ƙala ba har ta tashi dan halin ƙyaliyar sa ya rigada ya zame mata jiki tuntuni.. .mikewa tayi zata fice yace

“Dawo ki zauna mgn zamu yi”

..juyowa tayi ta dawo ta zauna a natse..

Sai da ya ɗau lkc sannan ya mata tmby kai tsaye.
“Me ke damin ki da kullum kike zama kina kuka ke kaɗai?

Sai yau ma ya san da haka?take ta ji hawaye na son cika mata ido,bai ce mata komai ba sai ta girgiza mai kai tana faɗin
“Ba komai”kallon mamaki ya mata wai har ta iya zurfin ciki tana ɓoye mai abu?ɗage kafaɗun sa yayi alamr abin bai dame sa ba ya ce ta je ta kawo mai coffee zai kwanta..

Zuciyarta na mata nauyi ta tashi Haka ta je ta haɗa mai tana tunane ta dawo ta miƙa mai a rayuwa tunda take bata taɓa fuskantar damuwa da shiga tashin hankali ba irin wannan,ta saba zama cikin mutani masoyan ta amma yau daga ita sai ita kamar marar hali mai kyau,wa zai fahimce ta ta sami yafiyar ƴar uwar ta…

Da miƙa mai ya tashi ya wuce ciki abin sa ita kuma ta jingina da kujerar tana tunanin ko ina rayuwar ta zata juya aƙala Allah ne kawai masani..

Lokuta ta asarar a tunanin nata har sai da ta ji ta gaji da zaman sannan ta tashi haɗe da kashe lights ɗin nan parlor ta wuce zuwa ciki..

Bed room ɗin is a luxurious one komai yayi daidai toh addu’ar ta ko a ƙasan ne ya bar ta ta kwanta ba sai lallai a kan gadon ba dan ta san wannan gadon ko ranar da ta hau bai mata tsawaba sakamakon rashin lfyr da yake yi ne so bata so ta fuskanci ƙasƙanci ko wulaƙancin sa akan wannan gadon ta san matar sa ce ke da damar hawa gadon..

Mamaki sosai ta yi da ta gan sa zaune saman kujera da table yana aiki ga papers nan birjik gefe ga laptop a side kaɗan ga kofin coffee ɗin sa nan..

Rasa abin yi ta yi sai ta hau kame kame shi kuma sallamar ta na fari a kunnen sa haka ya sa ya ɗago yana kallon ta sai ya tmby ta,da ƙyar ta iya furta..
“Bacci nake ji”!

funny,ya faɗa a zuciyar sa sai ya dube ta ya ƙara yana maida hankalin sa ga aikin sa kamar ba zai ce komai ba sai kuma kamar an fizgo mgnr ya ce mata
“Toh sai da safe”

da sauri ta faɗa mai a nan ɗakin take son kwanciya ba akan kujera ba batare da wani tunani ba tayi mgnr shi kuma sai yayiwa mgnr nata bahaguwar fahimta ya tsaya da ayyukan sa cak ya maida hnkl sa ga kallon ta daga bisani yayi wani tunani ya ce da ita

Ke Bazaki kwana min daki na ba
“Ga ɗakin ki nan can wannan kina iya zuwa can ki kwanta”!!

gyaɗa mai kai ta yi dan dai dai da rana ɗaya bata taɓa dunfarar ɗakunan dake site dinsa ba iyakar ta parlor
kitchen,bedroom ɗin sa in ta kai mai coffee ko in ta tafi gyarawa sai guest toilet da take buƙatun ta a ciki..

Ganin ta fita bata mai gardama ba sai ya taɓe baki yana goge bahaguwar tunanin da ya fara yiwa mgnr ta ya cigaba da aikin sa..

Ita kuwa da fita bata tsaya ko ina ba sai ɗakin da ya ce nata ne,tana buɗewa ta ga daki ne mai kyau sai ta tsaya mamakin tsaruwar ɗakin nata wato har ita ke mallakar ɗai irin wannan amma take kwanciyar parlor kuma shi bai taɓa sanar da ita ba?lallai miskilancin sa ya kai matakin izgilanci dan yayi yawa..

Abubuwan ɗakin sun yi ƙura sai dai bata jin zata iya gyara sa da daren nan ko dan sbd kar ya ce ta dame sa haka ta je ta yaye bedsheet ɗin gadon ta buɗe wardrobe ta nemo wani babban blanket ta shimfiɗa kan expensive cream colour royal bed ɗin ta ta ɗau wani na lulluɓe jiki sannan ta sauya night gown ɗin jikin ta zuwa wani daga haka ta kwanta akan gadon ta lulluɓe jikin ta da blanket ɗin..

Bazata iya tuna rabonta da ta kwanta a kan gado so yau bata jima ba baccin ya ɗauke ta


Kusan makara ta yi da safe yayi sai da ya ga bai ga giftawar ta ba a gidan sai yayi tunanin ya duba ta haka ya tura ƙofar ɗakin..

Hango ta yayi kwance saman gadon tana bacci hnkl kwance ƙarasawa ciki yayi ya tsaya a kan ta ya rinƙa kallon ta ya tada ta ne ko dai ya ƙyale ta ne bai sani ba,it was 7:10am sai da ya ƙare ma fuskar kallo sannan ya saka hannu ya fara yaye mata blanket ɗin dan shi dai bai taɓa jin ya kirata da sunan ta ba daga ki min kaza sai kai min kaza ko zo ko zauna,shidai sunan ta dai bai shiga bakin sa ba..

A baccin ta ji ana ja mata abin rufa sai ta riƙe wani gefe,kallon hannun ta yayi ya girgiza kai ya yaye blanket ɗin baki ɗaya.. .

Ganin surar jikin ta yayi,doguwar rigar bacci ce mai tsantsi kusan komi yana gani sai ya ɗan ɗaga idon sa daya kasa ɗaukewa daga jikin ta yana yi yana kallon fuskar ta sai da ta buɗe ido suka yi ido huɗu da shi..

A firgit ta tashi tana janyo blanket ɗin tana rufe jikin ta shi kuma ya kawar da kan sa a ɗan daburce ya juya yana faɗin

“Are u mad?..Ki tashi ki yi sallah lkc ya tafi”

daga haka ya fita ita kuma kunyar sa ya gama kama ta sai ta rinƙa jin nauyin haɗa ido da shi..

yau gaba daya haka ta rinƙa kauce mai dan kar su haɗu,ita me ya sa ma bata rufe ƙofar ba,shi kam gudun kar ta mai wani kallo sai ya rinƙa ɗaure mata fuska abinda zata ce ta jima rabon ta da ganin sa yana yi tun haɗuwar su ta fari sau biyu zuwa uku da ya rinƙa tamke mata fuska bai kuma ba sai yau..

Tana kitchen tana girkin ta har da saka lock sai ta ji ana juya handle,juyowar ta ke da wuya ta ga har an buɗe ƙofar an shigo..

Sumewar tsaye tayi ganin wani irin ƙerarriyar kaftan da ya saka,she can’t judge wen it comes to kayan maza amma ko ma wani iri ne wannan ta san mai tsada ne..

bayan ƙamshin da yake yi suturar ta zauna mai hular da ya saka matching colour da kayan sai ya fito da shi a asalin magidancin kamilin namiji,gabaɗayan sa sai ta ji kamar tayi capturing nasa tayi ta kallon sa.. .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button