KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Ƙwarjini ya mata ba kaɗan ba ai tuni tsoron haɗa fuska da shi ya ɓace mata sai ta shagala da kallon sa har sai da ya ɗan girgiza mata keys ta dawo duniyar mu ta fara kame kame sai ya miƙo mata yana faɗin
“Ga keys ɗin sashen nan ki rufe in na wuce in kuma zaki shiga sashen su Ammy ne fyn ni zan tafi wni wuri ba zan dawo da wuri ba kar ki yi abinci da ni,sai na dawo”!!.

da salon gentle man ya mata bayanin sai ta ji wani abu a zuciyar ta bata san ma ta furta ba sai ji ta yi ya ce

“Amin”!!wai ashe ce mai ta yi Allah ya tsare shi kuma ya dube ta sannan ya amsa ya fita…

Bayan ya fita ne ta fara leƙen sa ta windown kitchen ɗin tana kallon sa ya shiga motar sa ta Land cruiser asalin silver colour yayi horn aka buɗe mai gate ɗin nasu ya saka kan motar ya fita aka maida ƙofar aka rufe..

Abinda bata taɓa yi ba yau ta yi wato haurawa upstairs ɗin gidan,da sauri ta haura ta tsaya a balcony inda ta hangi yadda yake tuƙin sa so gently and maturely har ya ɓacewa ganin ta sannan ta dawo ƙasa dan duba abincin ta da niyar komawa duba upstairs ɗin in ta kammala girkin ta..

Duk tunanin sa ne ya rinƙa faɗo mata ta dai ƙarasa girkin ne amma hankalin ta na ga tunanin da bata san dalilin yinsa da take yi ba,bata san matakin da zata saka wannan abinda zuciyar ta ke ayyana mata ba akan Saheeb,so ne, shaƙuwa ce ko kusanci irin na ma’aurata?..

Mamuh26

Tana aiki tana jin wani sanyi yana shigarta saheeb ne yake yawan fado mata arai haka dai ta kammala aikin nata da kyar ta koma ta gyare ɗakin ta ta gyara mai nasa har bed wears ta sauya mai zuwa wasu maroon colours.

  Da ta gama ayyukan nata sai ta ƙi zaman cin abinci ta nufi upstairs ɗin dan binciken me ke wurin.

  Da zuwan ta ɗaki na farko ta shiga sai ta ga girman su kusan iri ɗaya da nata sai dai wannan ya fi nata girma kaɗan,komai na ɗakin mace yana nan a wannan ɗakin..

  Taɓe baki tayi tana tunanin hala na matar sa ne,da haka ta kuma duba wani ɗakin nan ma ta ga kaya kamar na ɗakin farko colour ne ya bambanta su..

 Dakin karshe dake saman ta je buɗewa sai ta gan sa a rufe,hararar ɗakin tayi ta sauko ƙasa abin ta zuwa kitchen..

  Abinci ta ɗeba ta zauna ci amma kasa ci tayi,fitar duk sai dawo mata a kai yake yi,ɗan awowin da tayi bata gan sa ba ta rasa meya sa duk taji ta dame,da ƙyar ta tuttura abincin ba dan tana jin taste ɗin sa kamar yadda ta so yayi ba…

  Sai da ta kammala cin abincin ta saka hijabin ta mai tsayi ta saka flat slippers ɗin ta ta fito,rufe ƙofar tayi ta nufi sashen su Hamida..

  Sallama tayi sai ba a amsa mata ba dan haka da hannun ta ta tura ƙaramin ƙofar ta shiga.

  Babu kowa a farfajiyar gidan ƙarasawa ciki tayi sai ta ga Hamida kwance ita ɗaya tana riƙe da remote tana ta sauya tashoshin tv..

  Tabbacin babu kowa a gidan kenan daga ita sai ita,hakan ya ma fifi daɗi dan zasu fi samin lkcn juna sosai..

  “Assalmu alaikum”kafin ta juyo ta fara amsa sallamar sai kuma da ta juyo ta ga Mufida ce sai ta ƙi ƙarasa amsa sallamar a bayyane ta amsa a ran ta.

  Ɓata fuska Hamida tayi,tayi kicin kicin tana kallon fifi daga bisani ta ɗaga mata murya tana faɗin
  “What?me kike so”?shiru Mufida tayi tana kallon ta,tsaki ta ja tana mai yi mata wasu irin kalamai marasa daɗin ji dake taɓa fifi ainun saidai ta san ita ta kawo kan ta dole ta jure duk abinda Hamida zata mata..
 
  Matsowa kusa da Hamida tayi tana sauke murya ƙasa game da bata haƙuri amma Hamida ta riga ta hau dokin fushi marar dalili kuma kishin fifi ya rufe mata ido da yawa dan har ta daina jin tausayin fifin da take jin in ta zo tana bata haƙuri,ga mijin ta dake lallaɓa ta yana ririta ta amma duk lkcn da ta ga fuskar fifi sai ta ji kamar duk ririta da Khalid ke yi bai isa ba dole sai ya kara dan gani take fifi is receiving a more intensive care a wurin mijin ta akan wanda take samu sai ta rinƙa jin haushin fifin sosai..

  “Kar ki ƙaraso gare ni tashi kawai ki fitar min daga gida,a kullum ke ce abin so komai naki mai kyau ne mijin ma sai da aka zaɓar maki mai kyau sannan aka baki ko ba haka ba?toh ki koma wurin waɗannan da suka tsara maki rayuwar ki suka rinƙa bi maki rayuwar daki daki suna nuna maki yadda zaki yi ki ce su samar maki abinda kika rasa yanzu dan ni kam kin ishe ni na gaji da mitar ki da kike zuwa kina min kullum,Hamee kaza Hamee kaza Hamee kaza,duk kalaman bakin ki Hamida ce ciki sbd kina da manufa da ni,in ba dan haka ba ta yaya ni ko zuwa sashen ki ban taɓa yi ba amma ke kin zo min ya fi a ƙirga,what are u up to?huh?fifi kin nemo soyayya da attention ɗin kowa a family ɗin mu kuma kin samu amma ki sani,lkc ya ƙure maki da zaki kirkiro wata soyayyar ƙarya dan ki sami nawa soyayyar,i can’t believe u coz u are always pretending.

haka kike haka kika taso kuma haka kike cigaba da rayuwar ki amma ki sani not any more in dai da ni ce Hamida,lies and pretence ɗin ki ya tsaya haka dan ban da lkcn sauraron su a kunne na bare zuciya da kai na

dan haka ina baki shawara da kin zauna a inda kike kin yi rayuwar ki kamar yadda aka tsara maki tun kina yarinya kin zauna da masoyan ki zai fi miki,dan ni nan da kika gan ni,,ba zaki taɓa samin yadda kike so daga gare ni ba ki koma ki yi rayuwar ki da waɗanda suke son ki dan ni ban da damuwa a baya neda ban da kowa damuwar ki ke dami na amma yanzu da nake da miji na ya ishe ni ya maye min gurbin komai,bana buƙatar kowa a rayuwa ta ki manta ma kina da wata ƴar uwa a duniyar nan dan ni na manta da ke…

na manta da an haife ni rana ɗaya nida ke daga jikin mutum ɗaya,awanni ɗaya sai bambanci mintoci biyar,kema da zaki yi hakan da ya fiye maki Mufida coz i will never ever accept u in my life anymore kin taka taki rawar for long so yanzu nawa lkcn ne my husband is all i got i don’t need u”!!

tana kaiwa nan ta wuce fifi dake tsaye cikin shock kamar an dasa ta..

Bayan Hamidar ta gama daddasawa fifi maganganu son ran ta ta haura sama faɗawa kan gadon ta tayi ta yi shiru tana tunanin irin kalaman da ta gasawa fifin ko sun dace ko basu dace ba..

Wani sashe na zuciyar ta ke faɗa mata tayi dai dai wani sashen na nuna mata rashin dacewar abinda ta yi sai dai mafi rinjaye ɗin ya fi nuna mata ai daidai tayi dan fifi ce ta jawo wa kan ta hakan..

Fifi dake tsaye tana halin shock ta ɗauki lkc a haka tana tunanin anya wannan Hamida ƴar uwar ta ce ko wata,kasa cigaba da daukar maganan fifi tayi sai ta tare hawayen da ya zubo mata da yatsar hannun ta ta juya ta bar sashen..

Hira suke yi suna dariya as family kawai ta turo ƙofar da ƙarfi ta shigo haɗe da yin jifa da wayar ta a ƙasa da ya faɗi ya tarwatse a wurin..

Take hankulan su ya dawo kan ta sai suka hango ɓacin rai mai tsanani a tattare da ita,take hankulan su ya tashi sai Ammy ta zo da sauri dan tmbyr lfy..

Ɗaga mata hannu fifi tayi cikin ƙunar zuciya da zafi rai ta kuma ɗaga ɗaya hannun ta dan ta san Hajja ce zata zo ta nan..

Hawaye ne taf a idanun ta wanda bata hana su zubowa ba ta bar su suna zubowa ita kuma tayi shiru dan zafin da ran ta ke mata in ba nutsar da zuciyar ta tayi ba kalaman da zasu fito bakin ta ba zasu yiwa su Ammy daɗin ji ba shiyasa ta ɗan tsaya na wasu lokutan sannan ta dubi wayar dake ƙasan sannan ta dubi Ammy ta kuma dubi hajja kana ta ce.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button