KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

“Kun ga wannan wayar da ta tarwatse a wurin nan”?gyaɗa mata kai suka yi sai ta girgiza kan ta ta ja hanci sannan ta cigaba da mgn

Tace “nima Haka zuciya ta ta tarwatsewa,haka rayuwa ta ta tarwatse,haka dreams ɗi na ya tarwatse its all because of u people,ku kuka bada gudunmawa mai ƙarfi a lalacewar komai da ya lalace a rayuwa ta,nayi tsammanin da zuciya ɗaya kuke so da ƙauna ta har na saki jiki da ku ashe ba haka bane,kuna nan kuna koya min abinda ku kuka san ba daidai bane,menene laifi na?yarinya ce ni ban san komai ba ku ya kamata ku nuna min hanya mai kyau a layin rayuwa ta amma baku min haka ba,kuna ji kuna gani na rinƙa aikata laifi amma abinda kuka kira da “So” sai ya hana ku nuna min laifi na?

duk akan ku komai nawa ya zama wani iri na rasa abu mafi girma a rayuwa ta,gani nan ina rayuwa a duniyar nan amma kamar ban da zuciya a ƙirji na,komai nayi dan gyara kurakuran ku bai yi sai taɓarɓarewar da al’amura ke ta yi,a dalilin ku…ƴar uwar ta,jini na wacce take a matsayin komai a gare ni ta guje ni ta tsane ni ta tsani gani na duk wani abu da ya shafe ni bata son gani ko ji,kuma ku kuka jawo hakan,da gudunmawar ku kuka nesanta ni da ƴar uwa ta,da sanin ku tsana ta ya ɗarsu a zuciyar ƴar uwa ta,a yanzu,a yau Hamida ta dubi tsabar ido na ta faɗa min ta daɗe da manta ni a rayuwar ta a matsayin ƴar uwar ta ta jini kuma tana umarta ta da in manta da ita nima,wa ya janyo min??

wa ya janyo min wannan abin?me ya sa kuka min haka?kunsan soyayyar ku na iya rikiɗewa ya dawo ƙiyayya a gare ni a idon ƴar uwa ta me ya sa baku ankarar da ni ba kuka rinƙa nuna min so da bambanci a gaban Hamida?

babu abinda ni na sani akan wannan abin amma ƙiyayya ta ta gama mamaye jikin Hamida is this just?ya dace?for all those years bata taɓa nuna ɓacin ran ta ba ku kuma baku taɓa nuna damuwar ku akan ta ba sai ni ni ɗaya what if i die right now zaku iya gyara guraben da kuka ƙirƙira ne a zuciyar Hamida?

zaku iya dawo da ni ku cigaba da bani kulawar taku ne dan kar in mutu kuma?no u can’t do anything kun rigada kun ɓata komai kun ɓata min matsay na a wajen ƴar uwa ta kun dasa mata baƙin tambari a game da ni a zuciyar ta da zai yi wuyar goguwa,yau an zo ƙarshe.. idan har ba zan iya gyara alaƙa ta da ƴar uwa ta ba toh i see no reason why i should continue leaving on this earth kun san me??ku manta da ni kawai i don’t need u all in my life..

babu abinda soyayyar ku ta janyo wa Ƙaunarmu ni da Hamidata yau bamu da wata rayuwa sai acikin ƙiyayyar mu.

dan haka ku bar ni ku rabu da ni ni na san yadda zan yi da rayuwa ta”..tana kaiwa nan ta juya da gudu ta fita..

Tana fitowa daidai balcony ɗin su Ammy sai ta ga Saheeb tsaye da alama ya ji komai,kallon sa ta tsaya yi tana numfarfashi da sauri da sauri tana jan iska da ƙyar dan ba ƙaramin nauyi zuciyar ta ya mata ba ji take kamar zai faɗo ya fito amma bata so ta cigaba da tsayuwa a sashen su Ammy bare har ciwon da take ji ya bayyana su gani su kawo mata agaji danbata nemar taimako ko kulawar kowa a halin da take ciki..

Kallon sa take yi tana kokawa da numfashin ta dake sama sama kamar zai ɗauke,ƙarasowa kusa da ita yayi sai kawai ta hau girgiza mai kai ta faɗa jikin sa cikin daƙiƙu kaɗan nan take kukan ta ya fito fili sosai sai ta sake jiki tana ta yi..

Kasa cigaba da tsayuwar wurin suka yi ta lalaɓa ya taimaka mata suka koma sashen su tana ta kuka..

Kuka sosai fifi ke yi sa sai da ruɗar da Saheeb dan bai taɓa ganin mace ma kuka irin haka dake fitowa daga zuciyar ta ba,tana a jikin sa tana kukan kamar ba zata daina ba ta rinƙa tmbyr sa

“Ina da laifi ne?sun saka tsana ta a zuciyar ƴar uwa ta ta ce bata sonta sake gani na,ta ce ta daɗe da goge ni a rayuwar ta a matsayin ƴar uwar ta i swear it wasn’t my fault ya zan yi da rayuwa ta”!?da shesheƙa mai ƙarfi ta ƙarasa mgnr sai ya ji tausayin ta dama yakan lura da shigi da ficin ta kawai dai jiran lkcn da ya dace ya tunkari abin yake yi..

A jikin sa zazzaɓin ta ya tsananta dole ya nemi Dr ɗin su ya zo cikin gaggawa dan har kamar ta fara convulsing,da zuwan Dr kuwa ya ce abin ya fara tsanani dan any moment tana iya samin cardiac arrest na biyu kuma dan ta ɗan jima tana danne rashin lfyr..

Wannan abin sai da ya saka zuciyar Saheeb bugawa ya kuma duban ta tana bacci sakamakon allurar da aka mata dan yayi calming nata..

Tambayar Dr yayi ko wani abu za a zaman yi mata da zai taimaka kar ya janyo rashin lfyr nata,nan dai doctorn ya ɗan yi briefing mai abubuwan da suka dace a rinƙa yi mata..

Godiya yayiwa doctorn ya raka sa shi kuma ya dawo ciki ya tasa ta gaba yana kallon ta yana tunane tunane a zuciyar sa game da yadda zai magance wannan abin..

4 hours later

Daidai 6pm fifi ta farka daga doguwar baccin allurar da aka mata sai ta ɗan zauna tana tunanin abinda ya faru da ita nan kuwa ta fara tunowa sai hawaye ya cike mata ido..

Kamar ya sani dama yanzu ya shiga wanka a ɗakin sa sai ya fito da ɗaurin towel ɗin ya nufi ɗakin ta,da shigar sa hawayen na dropping daga idon ta..
Kallon ta yayi sai suka haɗa ido take ta ji kamar an ingiza zuciyar ta sai ta fara sabon kukan..

Ɗan ajiyar zuciya ya sauke ya ƙarasa ciki yana mai gyara ɗaurin towel ɗin ya zo har gadon ya zauna haɗe da jawo ta jikin sa ya rungume ta tsam dan ya san tana wani hali mai wuyar fassarawa..

Kukan ta cigaba da yi a jikin sa ta manta a inda take kuma a situation ɗin da shi Saheeb ɗin yake na rashin sutura a jikin sa,haka ta yi ta rusa kukan ta shi kuma yana rarrashin ta har ta ɗan tsagaita sai ya ɗago da ita ya dubi fuskar ta dake dab da nasa ya haɗa ido da ita suna kallon juna har na wasu lokuta sannan ya fara mgn cikin sanyaya murya a hankali
“Am sorry i couldn’t understand ur pain”.

cigaba da kukan tayi tana shesheƙa sai da tayi mai isar ta sannan ta ɗaga daga jikin sa tana share hawayen fuskar ta..

Yana kallon ta sai kuma ta ruɗe ta fara yunƙurin kawar da kan ta a yanzu da ta dawo hayyacin ta,murmushi kawai yayi ya tashi ya bar ɗakin zuwa nashi..

Around 8pm na daren still ya dawo daga masallaci ya ga bai gan ta a nan parlorn ba sai ya shiga dan duba ta,nan ya ga yadda take rawar sanyi ƙudindine cikin blanket tana ta numfashi sama sama..

A hanzarce ya ƙaraso ya zo ya taɓa goshin ta ya ji zafi rau,duba magungunan ta yayi ya ga bata sha ba sai shine yau yayi jinyar nata ya kawo mata warm tea ta sha kaɗan sannan ya ɓallo mata magungunan ya miƙo mata ta sha..

A jikin sa tayi baccin bayan wuyar da ta sha a cikin jikin ta,jingina da gadon yayi yana tunanin mafita ɗaya sahihiya dan wannan lamarin nata ya munana..


Da safe ya riga ta tashi yataimaka mata ta yi wanka ta sauya kayan ta dan jikin nata da sauƙi,ya koma ɗakin sa da zumar zai je ya dawo sai ta kama hanya ta fita kamar dole tana kakkame jikin ta dan sanyi sanyin da take ji ta nufi sashen Hamida..

Yau kam Hamidar da kan ta ta buɗe mata ƙofa,tana ganin ta sai tayi wani irin murmushin is this girl for real sannan ta riƙe ƙofar nata tana duban fifin har na wasu lokuta..

“Hamida ki yi haƙuri jiya ban ji daɗin jiki na bane na so in zo da dare but ban da lfy ne shi ya sa ban zo ba”ko da Hamida ta ji fifi ta ce bata da lfy sai ta kuma duban ta a ɗan tsorace amma ta basar ta cigaba da kallon ta har ta cigaba da bata haƙuri tana tuno mata yarintar su yadda suke komai tare akan tayi haƙuri yanzu ma is not late zata gyara komai sai su dawo kamar lkcn suna yara ba tare da wasu sun masu karan tsaye a rayuwar su ba kuma..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button