KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Hamida abin na taɓa ta a zuciyar ta amma ta rasa ya zata yi da kishin ƴar uwar ta da ya mata dabaibayi a zuciyar ta sai kawai ta kawar da tausayin da ya ɗan bijiro mata ta gayawa fifi mgn son ran ta haɗe da rufe ƙofar ta a fuskar Mufida..

Da rashin jin dadi Mufida ta juyo zata fara kukan sai ta ga mijin ta na ƙarasowa da zuwan sa ya riƙo hannun ta bai ce da ita ƙala ba dama da sutura a jikin ta ya kai ta hanyar shiga motar sa tana bin sa bata ce mai komai ba har ya buɗe mata ƙofar ta shiga bata fahimci komai ba shi kuma ya zaga ya shiga..

Tada motar yayi sai ta ga yayi hanyar fita a sannan ta tmby sa ina zasu cikin kuka sai ya amsa mata da..

“Somewhere far from here”!!

daga haka ya ja bakin sa yayi shiru itama tayi shiru amma kukan zuci take yi mai ciwo haka a zahiri takan goge hawaye time to time,har suka yi doguwar tafiyar da a ƙa’idance ya isa ya saka mutum bacci sbd nisan sa amma da yake ba a cikin normal self ɗin ta take ba sai bata ga nisar tafiyar ba..

Wani gida ne babba ya tura motar nasa ciki bayan an buɗe gate ɗin gidan yayi parking ya kashe motar ya dube ta yana faɗin
“Shall we”?gyaɗa mai kai tayi sai ya fito itama ta fito sai ta ga ya bada umarnin a buɗe booth a fito da kayan dake ciki nan ta ga akwatunan ta har biyu aka zo aka wuce da su ciki suna tsaye..

Daga bisani ya mata jagora zuwa cikin main house ɗin tana bin sa a baya zuciyar ta na mata wani iri kamar ba ita ba…

Mamuh27

Tun da fifi ta gama maganganun ta ta tafi kaf jikin su yayi sanyi sun rasa ya zasu yi sun san su suka lalata komai kuma suna nadamar abubuwan da ya faru a sanadiyar su dan sun bada gudunmawa mai karfi a faruwar halin da ake ciki..

  Hajja ce ta fara zama kan kujera tana mai dafe kan ta in soyayya na siyar komai da sun yi amfani da shi sun siyowa fifi soyayyar Hamida amma duk gatancin da suka nuna mata bai haifar mata da komai ba sama da nisanta ta da ƴar uwar ta da yayi ina amfanin irin wannan gatar da soyayyar?..

  Ammy ce ta zo ta zauna kusa da Hajja itama tana nata nazarin da yadda zasu ɓullowa lamarin dan Hamida ta hau dokin fushi da su sam bata sauraron su ko sun tafi kuma sun san laifin su ne.

  Abin ya masu yawa sai Ammy ta kirayi layin Khalid dan abin ya ishe ta haka nan duk laifin kan ta da Hajja yake dawowa..

  Bugu uku Khalid ya ɗaga sai ta ce mai ya zo Hamida yanzu tana son ganin ta..

  Ko da ta sauke wayar sai da aka ɗau lkc kafin Khalid ya dawo gidan sakamakon rushing da yayi ya dawo daga asibiti ya je ya tasa Hamida a gaba dan su zo nan ɗin..

Rai a haɗe ta shigo tana kawar da kan ta dan kar ma ta ji wani batun daga bakin Ammy ko Hajja game da fifi..

  Gaida su tayi kamar an saka ta dole sai suka amsa mata suna kallon ta,Ammy ce ta fara bata haƙurin abinda ya faru sannan Hajja ta saka baki but duk wannan abinda suke yi bai ɗara Hamida ba so take su kai aya ta tashi ta tafi ta gaji da jin fifi fifi,imagine yardar ta da ƙaunar ta ma fifin kasa nemar sa tayi sai da ta zo ta haɗa da su..
 
  Hajja na gama nasihar ta Khalid na sauraron su Hamida ta ce ta gode ta miƙe ta fita ta bar su da jimami,kasa haƙuri Khalid yayi ya tashi ya bi bayan ta rai ɓace ya same ta a parlor zata shiga kitchen ya fizgo ta suna kallon juna rai ɓace ya ce
  “What was that Hamida”?kallon ƙwayar idanun sa tayi ta ce
  “A ina”?wani scoff yayi na raina mai tunanin da tayi sai ya kuma matso ta da ƙarfi ya ce

  “Hamida ki min duk abinda kika ga ya maki amma don’t u ever include my mother and my grandmother,ashe haka kike?har kina iya rufe idon ki ki ma waɗannan mutanin wannan abin?duk girman laifin da aka maki baki saukowa ki dawo yadda ake so ki dawo?ke da su wa ke nemar albarkar wani dan gama da duniya lfy?ke ko su?wacece ke da har za a maki laifi a rinƙa bibiyar ki ana baki haƙuri amma kina turjewa?
.
zatayi magana ya dakatar da ita yace

Hameeda wai meye laifin Mufida a wannan abin?ita ta maki laifin ta hana kan ta sukuni ta rinƙa zarya a nan sashen dan baki haƙuri but kullum da ɓacin ran ki take komawa yet bata haƙura ba ta cigaba da zuwa wai kuma baki ji tausayin ta ba,,my god Hamida ko wanda ya halicce mu a ko wani daƙiƙa muna masa laifi kuma da baya yafe mana ko numfashin da muke shaƙa ta iska da ba zamu shaƙa ba toh dan me ke ba zaki fahimci ƴaruwar ki ki yafe mata ba”?kallon idon sa Hamida tayi tana jin zafin yadda yake son ɗora mata laifin komai alhalin ya san ba yin kan ta bane su suka ingiza ta yin hakan..

  “Khalid ka je ka auri Mufida in ya so sai ka yi defending nata da kyau a idanu na amma wannan ba zai yi ba”! tana kaiwa nan ta buge hannun sa daga jikin ta ta wuce sa ba tare da ta juyo ba..

  Abin ya ɗaure mai kai,wannan wace iriyar tsana da kishi ne ya ɗarsu a zuciyar Hamida game da Mufida?ta fara rasa tunanin ta dan tana furta kalaman da ya fita daga na masu hankali..

  Ɗaga kafaɗun sa yayi ya juya ya shiga motar sa ya tada dan komawa bakin aikin sa zaman sa gidan nan bai da amfani sai dai ɓata abubuwa da zaman zai jawo dan Hamida tayi nisa ba fahimtar sa zata yi ba..


  A natse take ta kallon parlorn kamar bata taɓa ganin gini mai kyau da tsari da ya kai wannan ba sai ya kalle ta ya mana iso zuwa wani ɗaki inda nan ma ƙarshe ne a kyau dan ya tsaru yayi kyau..

  Kayan su ne a cikin ɗakin sai ta zauna bisa sofa ɗin ɗakin ta rinƙa kallon ɗakin komai maroon and cream colour tana ta kallo shi kuma yana mata murmushi..
  “It’s beautiful”!ta furta sai ya mata murmushin gamsarwa ya gyaɗa kan sa sannan ya koma waje dan ɗauko wasu abubuwan sa ita kuma ta cigaba da kallon ɗakin tana yaba sa..

  Har ya dawo bata tashi ta ɗaga komai ba sai da ya fara gyara kayan dan kan sa sai ta tashi ta fara taya sa..

  Kamar kurame suka yi gyaran ɗakin ta kalle shi tana son tmbyr sa kitchen dan ta samo masu abinda zasu ci..

  Nuna mata kitchen ɗin yayi ta shiga ta ga komai na nan kamar dama akwai mace a gidan..
  Nemo abinda zata dafa tayi ta fara aiki,duka duka bata ɗau awa ba ta haɗa jollof pasta da garnishing vegetables ta zuba masu a plate biyu ta saka folk da abin sha da kofuna ta fito da su zuwa parlorn..

  Baya nan sai ta shiga cikin ɗakin ta mai mgn akan ta kammala girkin,barin abinda yake yi yayi ya biyo ta zuwa parlorn..

  Zama suka yi a ƙasa kowa ya fara cin abincin sa,shi dai yana ci yana mamakin dama ta iya girki ne,shi yayi tunanin duk girkin da take yi ana zuwa taya ta yin sa ne toh amma yau da babu wanda ta sani a nan ɗin kuma tayi girkin sai yayi ta mamaki har ya kasa ɓoyewa ya tmby ta..

  Dariya ta yi dan tmbyr ta bata dariya sai ta dube shi ta ce
  “Ni na dafa da kaina”gyaɗa kai yayi ya cigaba da cin abincin har suka kammala babu wanda ya ce komai..

  Kwashe kayan tayi ta gyara wurin ta dawo tana gyara kayan ta dan ya fita zuwa masallaci…

  Da ta gama ta dawo parlor ta zauna ta kunna kayan kallo tana yi tana kallon wani ɗakin dake wurin yana fuskantar wanda suke ciki ta rasa me ya sa bai buɗe wannan ɗakin ba amma in ya dawo zata tmby sa..

Bayan wani lokaci

Bacci ke damin ta sosai sai dai bata san ya zata yi ba dan yana cikin ɗakin kuma bacci zai yi toh ita kuma bata san inda zata kwanta ba sai dai ta daure ta tmby sa..
  “A ina zan kwanta”!?kallonbta yayi sau ɗaya ya gyara kwanciyar sa haɗe da nuna mata inda zata kwantan da hannu,wato gefen hagun sa sai ta zaro idanun ta waje tana duban sa..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button