KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Sosai ta nutsa cikin duniyar tunani da sakamakon abinda ya faru a tsakanik su,shin shi zai daraja kyautar da ta mai ko zai wofintar da shi?ina nata makomar take a zuciyar sa?zai so ta ya ƙaunace ta ko a’a?dama abinda take ji game da shi wani abin ne na daban ba shaƙuwa ba?anya in ya dawo hayyacin sa zai mutunta ta ya ɗaukaka darajar ta a zuciyar sa kuwa?.
Kuma kallon sa tayi tana tuhumar kan ta da anya tayi abinda ya dace kuwa ta hanyar mallaka mai virginity ɗin ta?zai so ta ya kuma ƙaunace ta kuwa?..
Wani abu ke fizgar ta game da shi a zuciyar ta wanda da tana cikin daidai ne tana iya tantance menene wannan abin wanda ba komai bane sama da So.
Hawaye ne ya zubo mata jin yadda baƙon abin ke ratsa zuciyar ta da ko wani gaɓa na jikin ta..
“Allah ka taimake ni ka fi ni sanin abinda ke yawo a zuciya ta ya Allah ka min magani”ta faɗa a zuciyar ta tana kuma kallon sa tana jin baƙon abin na yawaita a zuciyar ta..
  Da haka baccin itama ya ɗauke ta tana jin ciwon jiki da kasala ko ta ko ina sakamakon rashin sabo…

Mamuh28

6am
Shi ya fara farkawa daga baccin sai ya kasa tashi ya ɗan jingina da gadon haɗe da rumtse idanun sa,shiru yayi yana tuna abinda ya faru a jiya..
Da ƙyar ya tuno gabaɗaya sai ya juyo kan sa ya kai idanun sa gare ta..

Ƙure ta da ido yayi yana ta kallon ta yana jin wani abu game da ita a zuciyar sa da bai san matsayin abin ba..
A hnkl ya kawo hannun sa ya shafa fuskar ta yana admiring beauty ɗin ta,kamar kar ta farka daga baccin dan wani irin kallon kyakyawar mace dabai taba gani ba yake mata..

Ciki cikin zuciyar sa gani yake kamar ya mata fin ƙarfi amma a wani sashe na zuciyar sa yana samin musayar ra’ayi.
Numfasawa yayi yana matsowa kusa da ita yana cigaba da kallon ta hannun sa a fuskar ta yana shafawa a hnkl yana yaba ta a zuciyar sa..
Tmbyr kan sa ya hau yi a zuciyar sa yana ganin kamar shikenan girman sa ya zuba a idanun yarinyar kuma ba zata rinƙa tsoron sa ko shakkar sa ba but abu ɗaya da ya sani shine shi da ita sun zama abu ɗaya tun jiya ko ya so ko ya ƙi ta san shi ya san ta..

A sannu ya matso gab da ita ya kawo lips ɗin sa ya mata kiss a goshin ta sannan ya dawo ta gefen sa ya sauke mata wani a cheek ɗin ta sai a sannan fifi ta buɗe sleepy eyes ɗin ta ta sauke su a fuskar sa..

Kallon juna suke ta musayar sa ita da shi wanda basu san ma’anar sa ba su dai sun san kallon na masu wani irin illah a zukatan su amma basu san matsayin abinda suke ji ba..

Shi ya kuma matsowa kusa da ita ya ruƙo fuskar ta,ƴar taƙaitacciyar murmushi ya mata murya ƙasa ƙasa ya ce da ita
“Am sorry for last night”lumshe idanun ta tayi tana tuno abinda ya farun a jiya haɗe da zafin raɗaɗin dake ratsa ta a hnkl..

Ɗago fuskar ta yayi da hannuwan sa biyu ya matso da fuskar sa kusa da nata ya haɗe..

Ba shiri ta buɗe idanun nata tana zazzaro idanu waje alamar tsorata da tayi da situation ɗin da suke ciki..

Murmushi ya mata yana kuma maimaita mata haƙurin sa da yake ganin kamar ya zalunce ta..
Kafe sa da ido tayi tana ta kallon sa,alarm ɗin ɗakin ya fara bugawa..
Da hanzari ya kai duban sa ga agogon bango ai ko ya ga har 6:30am ya yi..

Ajiyan zuciya yayi yana mai duban ta haɗe da ɗago mata gira ɗaya yana girgiza kai itama sai ta ji kunya ya kama ta har asubahi ta wuce suna nan kwance..
“U caused this”!ya faɗa yana sauka daga gadon a hnkli,da mamaki ta bi shi da kallo yayin da yake shigewa bathroom a zuciyar ta take mamakin ta ina ta zama sanadiyar makarar su sallah alhalin shi ya mata wannan abin..

Ƙwafa tayi ta yunƙura itama zata tashi sai kawai ta ji zafin ya ƙaru take ta sake ƙara tana kiran sunan Ammy..
.
Saheeb dake tsaftace kan sa ya jiyo ƙarar muryar ta sai ya ɗan dakata yana nazarin ta daga bisani kuma ya fito ɗaure da towel ya tsaya yana kallon ta.
Tunowa da abinda yayi a jiya ya saka sa saurin ƙarasowa yana tausaya mata dan kusan mantawa yayi da cewa jiyan budurwa ya taɓa ba matar sa Muhibba ba shi ya sa yau ɗin ya tafi ya bar ta..

Taimaka mata yayi ta tashi daga zaunen da take,yana kallon yanayin ta abin tausayi ya raka ta toilet ɗin..

Duk wani taimako na gaggawa da ya dace mace ta samu bayan irin hakan ta faru,Saheeb ya ba matar sa Mufida a wannan makararren subahi,sannan shima ya tsaftace kan sa ya fito bayan ta riga sa fita tun ɗazu..

Sauya kayan jikin sa yayi sannan ya dube ta yana mai matsowa kusa da ita ya zauna yana mai riƙo hannun ta cikin nasa yana murmushi ya ce
“Zaki iya sallar a tsaye ko sai dai a zaune”?ƙasa tayi da kan ta tana jin nauyin sa sosai..

Ɗago kan ta yayi yana mamakin wai nauyin sa take ji akasin matarsa Muhibba halayyar Mufida a yanzu yana mai wani banbarakwai dan bai san da ita ba..

“Lkc na tafiya bamu yi sallah ba amsa min”sai kawai ta girgiza mai kai tabbacin a zaunen zata yi ba zata iya tashi ba..

Rabuwa da ita yayi ya tashi tsaye ya tada sallar sa ita kuma tayi a zaune har suka idar yayi adduo’in da ya dace ya shafa sannan ya dawo inda take.
Har ta fara baccin gajiya sai ya tsaya kallon ta bai san ya aka yi ba amma kawai yana jin nishaɗi in yana kallon ta..

Kasa tada ta yayi daga baccin sai ya tsaya ƙare mata kallo ganin baccin na mata daɗi in kuma ya tada ta maybe ta sami headache sai ya bar ta shima yayi joining nata a baccin ya kwanta kusa da ita bayan ya haɗa hannun sa da nata..

Peaceful sleep ya samu da ya jima bai yi irin ta ba a rayuwar sa abin ya mai daɗi ba kaɗan ba..

2hours later

Ita kaɗai ta farka ta ga kan ta saman gado sai ta fara tunanin ina ta kwanta last,a a hnkl ta juya ta ga ba kowa a ɗakin sai ita kaɗai.
Hamma tayi tana miƙa haɗe da tashi daga kwancen da take ta duba agogo ta ga ƙarfe tara har ya gota sai ta sauko daga gadon a sannu tunanin ta zafin na nan har yanzu,sai dai ta yi mamakin jin cikin kaso mai yawa zafin ya ragu sosai..
Hamdala tayi ta sauko daga gadon completely tana takawa a sannu har ta fito ta duba babbar parlorn babu kowa sai dai hancin ta na ɗan jiyo mata wata ƙamshi ƙamshi mai kama da girki.. .
Bata tsaya ɓatawa kan ta lkc ba ta nufi kitchen ɗin tana wondering wa ke girki a gidan dan ta san daga ita sai shi ba wasu..

Tsinkewa tayi ganin Marshall da apron har da hular apron ɗin a jikin sa hannun sa riƙe da babban serving spoon ga frying pan a hannun sa yana juye wani abu da bata san menene shi ba..

Bai san ta shigo ba sai jin mutum yayi kusa da shi dan haka ya juyo sai suka haɗa ido da ita..
Shi ya riga ta mgn ta hanyar tmbyr ta ya jikin ta,sai tayi shiru tana cigaba da kallon aikin sa da yake yi na girkin,a matse take da son sanin ko me yake girkawan amma bai bari ta fahimta ba dan yana gama juyewa ya rufe ya juyo gare ta gabaɗaya..

Ja da baya tayi kaɗan tana gaida sa sai bai amsa ba yayi shiru ya juya ya kashe gas cooker ɗin haɗe da juye ruwan zafin dake tukunyar cikin kofuna biyu madaidaita..

Duk tana kallon sa kamar tana kallon abin al’ajabi wai dama ya Iya girki ne ko dai yi mai aka yi ne shi kuma yake wani ɗaga kafaɗar shi yayi..

Out of blue ta mai wata tmbyr da sai da ya ɗan dakata daga abinda yake yi ya kalle ta sannan yayi wani murmushin dole kafin ya amsa ta..
“Can u cook”?sai ya kalle ta na wasu seconds sannan ya amsa mata da
“Uhmm”bata gamsu ba sai ta kuma tmbyr sa
“I don’t understand uhmm”!!kallon ta yayi sai ya bar abinda yake yi ya tako har dab da ita ya ja ya tsaya kamar gunki..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button