KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

” kodai kar mu tafi naga kin kara kyau komi yakara cikowa”nan yafi dadi ko…sai yakare maganar da irin tsigan wasan nan Murmushi medan sauti tasaki dan ita abun daria yabata dan tasan ina maganan nasa ya dosa Hmm 3weeks kawai ya isa tadau cikine abunda tafada kenan acikin zuciyar ta?tanata murmushi haka kawai taji burin samun hakan ya mamaye ta Tunanin hakan ta mugun sawa aranta
Kamar yadda yace xasu tafi goben baiyuba wani sati guda suka kara inda babu abunda ke ninkuwa a tsakanin su sai sassanyar so da shakuwa
Kullum in tana jikinsa sai yayi ta tsokanan ta da cewa…”seriously bakiga yanda kika canza ba, inaga idan munkoma gida zamuje hospital a duba munke” dage eyebrows dinta takeyi tace, “ok” bata iya cewa komai
Kwance take sannan tamike tace bari taje tafara shirya kaya tun yanzu shima mikewan yayi yabi bayanta yace su shirya kayan atare
Bedroom dinta suka shiga suka fara shirya komi a inda yadace bayan sungama hada kayan nata sai suka wuce nashi closet din shima suka shirya komi inda ya dace da la’asar bayan yadawo daga masallaci suka shiga kitchen tare suka hada dinner saidai tun a kitchen Fifi tafara jin wani irin sauyi acikin jikinta dakyar ta iya bari suka gama aikin batare da ta nuna masa alaman komi ba…
suna gamawa tayi saurin wucewa room dinta tashiga bathroom zatayi wanka nanfa tafara jin tashin zuciya jim kadan ta soma kwarara Amai mai yawa mai gajiyarwa Sosai gaban ta ya fadi…
Nan take taji wani irin bakon yanayi ya dulmuye xuciyarta
tsoro da fargaba wanda bata san dasu ba taji yana dirar mata take gabobin jikin ta yayi sanyi sosai ba abunda take tunawa sai ranan mutuwar ta,tsuguno tayi agaban toilet tana haki,wasu silent tears ne ke ziriya daga cikin idanun ta marasa ma’ana marasa dalili..
Takanji kamar Wani bangaren xuciyarta ya amince da sabuwar zabin da Allah ya mata na samun wata nitsatsiyar rayuwa da saheeb amma takan gujewa rudin zuciya musamman akan soyayya dan ta riga tasan iya madakatan rayuwar ta ba wani boyayyar abu bane,mutuwa ne.
Ta dade anan cikin rudanin haka,batare da sanin me zatayi ba.
Jin shirun ta yyi yawa Marshall ya biyo bayanta da sauri yashigo bathroom din ganin yanayin ta kawai yafara jera mata sannu,uhmm kawai take iya cewa harya gama tayata wanke mata jiki yacire mata atamfar dake sanye ajikinta ya daura mata wani white towel ya daukota kamar wata baby yafito da ita yadireta akan gado,a daren ranan ba karamin wahala tayiba sabida aman da take tayi ya tsanan ta wani bin sace jikin ta takeyi tayi abun ta ta dawo..
Washe gari Koda tayi sallan asuba saita koma ta kwanta sabida baccin da batayi a daren jiya ba,har cikn ranshi ya damu sai Bai tashe taba sai wuraren 10am shima yatada tane sabida su isa gida dawuri da kanshi yayi mata komi yayi feeding nata da kyar tea kadai ta iyasha
Ciwon kai da bacci ya gama kashe mata jiki
saida yasaka Duk trolley dinsu a mota sannan yadawo ya daukota a owner seat ya ajiyeta hade dayin kissing dinta sannan yamaida door din yarufe yakoma yarufe ko ina nagidan sannan yabawa gate man keys din yashiga driver seat yatada motar sukabar compound din gidan
5pm yamusu a gida suna shiga cikin compound din gidan taji gabanta yawani fadi saidai takosa sosai taga twinnie dinta sabida she have missed her so much fiye da tunanin me tunani , a bakin apartment dinsu yafaka motar da kanshi yafito yabude mata door din motar tafito sai yace mata tashiga zaishugo yanzu uhm kawai tace sannan takai hannunta kan handle din door din tabude tashiga babban falon saheeb bakinta dauke da yar karamar sallama.
A Zaune ta tadda wata mata a daya daga cikin kujerun falon sanye take da wa’insu hadaddun riga da skirt na Atamfa English Aura wax wani irin qamshin turaren Arabians na tasowa daga cikin ahankali Yana gauraya palon.
ganin kyakkyawar dirarriyar mace a zaune cikin palon saida yafadar ma Fifi da gaba duk dama bata san ta ba,dan karamar ajiyar zuciya ta sake saita dake takarasa shiga cikin falon tanajin wani rawar jikin sanyi na shigarta da tsantsar tsoro da wani tauri nason danne mata zuciya ta kakalo murmushi harta karasa inda Muhibba din take zaune tana pressing phone dinta, “asslm alaikm Ina yini” shine abunda Fifi tace a taqaice tana sake kallonta cikin tsananin sarewa da faduwar gabanta dake tsananta,
Kallonta ta sake dagowa muhibba tayi cikeda da qare Mata kallo tana qoqarin danne abinda ke taso Mata gameda fifin sbd Babu tantama wannan itace mufeeda wadda ta auri Marshall dinta Wanda ya kasance nata ita kadai….itadai Fifi murmushi tayi dan she don’t really care
Wucewa room dinta tayi Muhibba tabi bayanta da harara mai zafi.
Mamuh
[8/6, 10:58 PM] Miss Xoxo: 29
5am ta farka da face dinshi tafara tozali sosai ta wani kafeshi da ido tana karewa face dinshi kallo soyayyar shi na huda duk wani gabobin jikinta har batasan sanda tasaki wani murmushi ba hade dakai hannunta tashafa gefen face din nashi, abunda bata saniba tun farkon tashin ta shima yatashi sai jin hannun shi tayi akan nata hannun sai tayi saurin zaro manyan idanunta hade da sauke su akan face dinshi dayake aika mata da wani rikitaccen murmushi me ma’anoni da dama saurin rintsa idanunta tayi tana boye face dinta a jikin pillow,
a hankali yakai hannun shi kan lips dinta yana shafawa lips dinta yana daya daga cikin abunda yafi birgeshi da ita Duk dashi komi nata birgeshi yakeyi, cikin yar karamar voice dinta tace, “it’s already late lokacin sallah yayi” lips din nata kawai yatsirawa ido sabida yanda take motsa bakin kamar ba daganan maganar tafito ba,
“I know” shine abunda yafada hade da daukan ta cak yakaita bathroom a tare sukayi wanka suka tsaftace jikin su still da zasu fito daga bathroom din daukar ta yayi yafito da ita yadireta akan gado, sannan yace mata
“pray nima zanje na shirya nayi nawa sallan” nodding kanta kawai tayi tana wasa da fingers dinta harya fice daga dakin saita tsinci kanta da sakin wani murmushi tabbas yanzu kam tagama yarda da soyayyar Marshall yagama kama Duk wani sashi na jikinta a hankali tamike daga kan gadon takarasa gaban wardrobe tasanya hannunta guda biyu tabude inda long abayas dinta suke tacuro wata purple color me manyan design a gaba tasaka hade da daukan hijab sannan takarasa ta dauki prayer mat tashinfida ta tada sallah,
Bayan 30min Marshall yashugo dakin zaune ya tadda ita akan prayer mat tana azkar kallon ta kawai yakeyi yanajin wani shauki akanta he loves her so much saida yakusan 5min a tsaye sannan yakarasa shiga cikin dakin yamaida door din yarufe karasawa yayi inda take hade da samun waje a bakin gado yazauna yana kallonta atare suka shafa addu’an sannan ta dago takalle shi suka sakarwa juna murmushi cikin yar karamar voice dinta tace
“Good morning” saida yakai hannun shi yakama mata nata hannun sannan ya amsa da, “Morning mon amour, how’s ur night?” sosai taji dadin sunan daya kirata dashi shafa tafin hannunta daya keyi shiya hanata amsawa dawuri dan haka saida ta dauki lokaci sannan ta amsa da
“Alhamdulillah dafatan kaima katashi lafia” takare maganar da dan dagowa tana kallon shi ta wutsiyar ido,
bata ankara ba saijin mutum tayi ya sunkuceta yayi kan gado da ita saida yakwantar da ita sannan yacire mata hijab din dake sanye a jikinta ya ajiyeshi a gefe guda sannan yacire mata long abaya din a cewarshi abayan zata takura ta itadai idon ta yana rufe har shima yacire nashi jallabiyan ya ajiye agefe sannan ya janyota zuwa jikinshi hade da rufe suda blanket, yafara wasa da long hair dinta dayasha gyara harshen shi yakai cikin kunnanta yana latsawa a haka wani baccin yakara daukan ta,