KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS
8am suka farka a tare suka shiga bathroom sukayi wanka half gown tasaka mara hannu milk color saita zubo da gashin kanta har gadon bayanta sosai tayi kyau Duk dako powder bata shafa a face din nataba sai kalolin perfumes data feshe jikinta dashi tana gamawa tawuce kitchen cikin 30min tagama hada musu abun breakfast,
Arabian meal tahada musu Wraps, sandwiches and manakeesh tana son kalolin abincin larabawa sosai shiyasa ta iya dukkan nau’o’in abincin su, anan dinning table na kitchen din ta jera komi tana juyawa zata fita daga kitchen din Marshall nashugowa sanye yakeda kananun kaya black jeans da white T-shirt yayi kyau sosai har batasan ta kafeshi da idanu ba saida yakaraso gabda ita sannan tayi saurin sunkwi da kanta tana sakin murmushi me cike da ma’anoni dayawa ita kanta ta shaida Marshall hadaddan namiji ne ita kanta tasan tayi sa’an samun gwarzon namiji kamar Marshall tana kuma jin shauki sosai a kansa,
Hannun sa yakai kan face dinta yashafa hade dacewa
“You look so cute Mon amour I like ur dress” saida takara murmusawa akaro na biyu sannan tace, “I like urs to” sannan tayi saurin karasawa taja kujera tace, “Seat” baiyi mutsu ba yakarasa ya zauna saidai Duk abunda takeyi idanun shi yana kanta harta kammala serving dinshi ta ajiye mai komi a gaban shi sannan tasaka nata taja kujera ta zauna,
saida yakalli Breakfast din sannan yakalleta sai yasakar mata murmushin gefen baki sannan yace, “so you know how to cook Arabian meals?” saida takai cinnamon tea bakinta tadan kurba sannan tayi nodding kanta tace, “Arabian Meal yana daya daga cikin favorite dina I will cook Arabian meal for dinner if you like it” tayi maganar da dage mai gira saidai kanta a duke yake,
“yeah I like it bakisan ina son abincin larabawa ba” hira sukeyi har suka kammala cin abincin a tare suka wanke dishes din suka maida komi inda yake sannan ta goge kan dinning din, yana rike da hannunta suka fito daga kitchen din a three seater suka zauna sai tayi pillow da cinyar shi suka fara taba hira kadan kadan anan yake kara sanin halinta itama tuni tagama fahimtar halinsa sabida anan zaman da sukayi ta fahimci yanada dadin zama sosai kuma baida matsala,
A cikin yan kwanakin wani shakuwa ne me karfi yakara shiga tsakanin su dan tuni Fifi tazubar da Duk wani abu tafara nunawa mijinta tsantsar soyayya shima anashi bangaren hakane dan har mantawa sukeyi da akwai wa’insu mutane a duniya bayan su sabida zallan soyayyar dasuke nunawa junan su.
Mamuh[8/12, 12:04 PM] Nadady: 31
Turo kofar tayi a gajiye tana maida numfashi Bata jima ba ta nemi waje a gefen gadon ta xauna a kasale,fuskar matan ne yaki fice mata arai wani irin yanayi ta tsinci kanta a ciki Wanda batayi tsammani ba.
A Sashen su ammy saheeb ya jima by 8pm kusan kowa ya fito za’ayi dinner Allah Allah Fifi take ta samu damar ganawa da su ammy gashi har cikin ranta take matukar jin muradin ganin hamidarta.
Ayanzu ji take kamar Zuciyar ta yayi sanyi,wani sashi daga abubuwan da suke yawan damun ta game da tarayyar su da hamida ba laifi sun ragu mata,bathrum ta shiga tayi wanka kasalan data ke yawanji shi ya sa ta sanya doguwar Riga pure red material and masa design da wild rose hipup belt wanda ya Dan sake ta yau batayi wani kwaliya sosai ba
Babban sashen gidan ta nufa inda Tasamu duk an zazzauna a dinning wani sanyi ne ya mamaye Zuciyar ta ayayin da take kallon su kusan kowa fuskan sa dauke da murmushi musamman hamida da Khalid Wanda Babu wani Abu daya rage ayanayin su na nuna tsananin so da shakuwa dake wanzuwaa a zukatansu.
Purple atampa ta sa Mai kyau Wanda ya dau kalar fatan kusaan kala daya da tsadadiyyar yadin vice chair man Wanda ya amshe jikin Khalid ya masa kyau sosai Shima.
Agefe da shi ammy ne da hajja wani
murmushi me sanyi ne ya kufce mata ji tayi kamar taje ta rungume su Dan bakaramin zazzafan kewarsu takeji aranta ba,a hankli ta maida kallon ta kan saheeb Wanda kallo daya ya isa yasa kasan bai Saba zaman cikin su hakanan ba dago kanta ke da wuya caraf Suka hade idanu da muhibba agefen sa irin kallon datayi mata yasa tayi saurin dauke kai gyaran murya tayi sannan ta karaso ciki a yanayin fara’a da basarwa.
” Salam alaikum”
Tace da muryan ta na da can Wanda shi kowa ya fi Sanin ta dashi, hamida ce ta soma juyo ta kalle ta cikin dakakkiyar murmushin da ya kufce mata baxata
Ammy ce ta soma mikewa sannan Hajja tabi bayan ta wani rungumar ta sukayi atare ayayin da suke gaisawa
Fifi Fifi tuni waje ya kaure da sabuwar surrutayya.
Saheeb ne kawai baice uffan ba”fifi kuwa har ta xauna Bata wani samu cikakkiyar nutsuwa aranta ba Dan rasa gane inda zata ajiye tunanin tatayi,wani bangare yanaga hamida wani Yana ga mijin ta saheeb da matar sa dataa Sha uban kwalliya tana serving kowa a nutse wacce Babu alaman kasawa ko yaranta a fuskan ta.
Normally wajen ya dau shiru kowa ya nitsu ya maida hanklinsa akan dishes dinsa ana hira sama sama,Banda hamida data fiye bada hanklin ta a kan Khalid kadai Dan in ba shi yayi magana ba Sam Bata cewa komai.
Ganin Fifi Ras fiye da yanayin yadda suka bar gidan yasa su ammy shagala,waccan yanayin zazzafan so da nuna tsananin kaunar da kulawa da suka Saba mata shiya ke fallasa kansa a duk sanda sukayi magana awajen
Babu tantama tun zamar su anan hajja take ta mata tambayoyi da wasan gata irin na tsoffi sakalci da kauna duk da ma Fifi tana basarwa Amma hamida ko ajikin ta,gani take inda sabo to ta Saba muhibba ce Abun ya mata banbarakwai sabida ji kawai tayi Abakin hamidar Amma Bata tabbatar ba Sai yau dataga cewa kusan hanklin kowa akan dinning din akan Fifi yake
Hirarrkin ma It’s all about her, duk abubuwan da fifin tayi sabo sanda basa Nan seda sukaso suji duk dama ita fifin tana hankalce da furucin ta na rashin son bayyana wani Abu daxai sake kawo wani tsabanin fahimta tsakanin ta da yar uwantan.
hakan yasa taki Jan magana kwata kwata baifi Tace eh aa ba ko ma tayi dariya ba.
Duk da hakan ba shi ya Hana hamida Sanin cewa fahimtar juna ya samo mafaka tsakanin su da saheeb ba Allah Allah take Subar wajen ta samu ganawa da muhibba Dan tun xuwarta gidan suke kulla maganan a tsakanin su batare da kowa yasani ba
Tun ranar da su ammy suka sanar da muhibba cewa tana da kishiya Hamida ta gane cewa muhibbar mace ce me tsananin kishi musamman reaction din ta nuna lokacin da akace mata tare sukaje hutu
Kwanan muhibba biyu agidan Amma Babu Wanda ya gane kanta face hamida da tasanya mata idanu tana karantar abubuwan dake wanzuwaa a zuciarta na fushi da tsananin kishi hade da boyayyen damuwa.
A da can ko gaishe da su ammy Bata son fitowa tayi,tanan ne hamidaa ta shige ta da sigar nuna cewa tana tausaya mata duk dama muhibbar Bata amshe ta lokacin guda ba Sanin cewa ita taawainiyar kishiyaartan ne
Amma daga bisani hamidar ce ta wayar Mata da kai,ta cusa mata wani rufaffiyar ra’ayi me shiga har Zuciya a dunkule…
Duba da cewa Auren rufin asiri akayi ma Fifi da saheeb yasa su ammy basu bude ma muhibba komai da komai ba Sabanin nuna mata da akayi cewa Auren dangi kawai aka musu wanda aka barshi a matsayin Qaddara ne ya hada.
Hamida kuwa fede Mata biri tayi har wutsiya tayi cikin salon yaudara sanda ta cimma wani boyayyen manufarta.