KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Ta fara ne da nuna Ma muhibba yadda kowa
Da komai yake komawa na Fifi,ta hanyar Bata labarin yadda kowa agidan yake daukakata ake Fifita ta ake son ta fiye da komai.

Tace dama wannan ciwon shine makamin ta wajen kwace komai na jin dadi a ryuwar wani nikaina danake yar uwanta Saida ‘ta kwace min nawa rayuwar,na wajen iyayen mu kakanin mu kawayen mu ke har mijina ma Saida taso ta juya masa kwakwalwa,arayuwa Fifi tafison kowa da komai ya zame nata ne ita daya
..koda akayi Auren ai mijinki bai kwatanta cin amananki ba Ina lura ya kama kansa duk dama yasan lankaya masa ita akayi,amma yarinyar Nan waini take so tayi amfani Dani Dan cimma manufarta akan saheeb sabida na nuna musu cewa na gano mugun halayyarta na son Kanta da son Zuciyarta,inkina so kiga munafukar mace inkika hadu da Fifi kinsamu kankat.. duk yadda naso ace su ammy sun gane menake nufi Amma sun ki, gani suke kamar karya nakeyi bansan meye asali a Zuciyar Fifi ba,ba gashi Nan a bayyane ba?kawai tasan nafi Karfin ne shiyasa take nuna kamar tayi nadama but ni nasan da ciwon Nan nata take harin gamawa da mijin ki Shima.

Ko ke baki gane bane? in har dagaske akaina take cikin wancan damuwar da Zama zatayi Dani Dan In Yafeta bawai tace mijin ki xata bi wani waje ba,to wayasan Me taje ta aikata Masa ko wani irin karya ta shimfida Masa Dan ta shiga rayuwar sa ta janye ra’ayin sa makanta ita daya.

Kedai kiyi hankli da ita ni kadai nasan halayyar fifi daga ta cimma burin ta akan saheeb to babu me sake kallon ki ko jinki,sannan a gidan nan for 23yrs ana nunamin cewa fifi bata lefi bata kuskure kuma duk abunda take so nata ne, ina guje miki shiga kunci da damuwa irin nawa,compare to me aike tamkar bare ce in har anmin to kowa ma za a masa,dan haka bana cire tsammnin cewa duk wata mace me tsananin kishin mijin ta kamar ki zata iya rayuwa a tarkon fifi.

“Nice tawainiyatta kuma nice nafi kowa sanin komai akanta ln kina son kanki da lpy sai ki bani hadin kai wajen kwaco yancin mu da farincikin mu,nikam na kwace miji na a tarkon ta saura ke,in bazakiyi wani abu ba wannn ya rage miki.
.
Wayannan munanan maganganun Muhibba take juyawa aranta ayayin da dukanin hanklin ta gaba daya ya koma ga kan su fifi da ammy da shikansa saheeb daya tsoma baki a hirar su ta yanxun dake hirar ya shafi lapiyar fifin ne

Banda boyayyen kallon kallon da sukeyi a sace Wani shiru muhibba tayi tana kan fahimtar gaskiyar maganganun hamida data sha gaya mata akan fifi, ta dade cikin wannan yanayi
can tayi boyayyar ajiyar xuciya ta tabe baki a hankali bata ce uffan ba.

Fannin fifi kuwa tun Daga yanayin bayanan saheeb da tambayoyin da ake mata tana amSawa Khaleed ne ya soma fahimtar cewa ciki ne ya shige fifi.

Bayan sun koma sitting room duka akan za’ayi musu nasiha Cikin salo sanda khaleed yasa kowa ya fahimci hakan su ammy da hajja ina Kasaka da murna,alkwarin so da kulawa babu wanda basu bayyyana shi ba fifin dai batace uffan ba ayayin da saheeb ya sulale ya bar wajen dan dama shikam ya gane abun tun jiyan datake ta laulayi.

Yana barin wajen muhibba tabi bayansa

Ita kuwa fifi a Duk murnan da akeyi hanklin ta nakan yar uwanta ne,sakamakon wani bangaren zuciyatta yana alfahari da cikin wani kuma yana kinsa da jimamin kada yar uwan ta ta sake alakanta hakan da samun fifikon da zai sake haddasa wani kiyayya da damuwa aran yar uwan tan.

Tana cikin wannan tunanin hamidar ta mike bayabo ba fallasa tayi musu sallama,a gurguje fifin ta mike tabi bayanta tanata kirar sunan ta gasunan daf da daf amma hamida ta sakai bata juyo ba bare ta amsa hakama ta rufe kofarta agaban idanun ta batare da ta ce mata uffan ba.

A sanyaye fifi take kallon kofar wani karayar xuciya da gabobin jiki su suka lullube ta sai tayi shiru bata dawo hayyacin ta ba sanda taji gyaran muryan khaleed ta bayan ta

Yace yadai Mufida baki shigaa ciki bane?

Matsawa baya kadan tayi cikin boye damuwarta tace

“ah’a yanxu na fito..im just abt to leave.

Ajiyan zuciya ya sauke
yace “ohh to shikenan..

kwayar idanun su suka hada atare tayi saurin kawar da nata gefe kureta da idanun sa yayi yanata kallon ta bakinshi da zuciyar sa cike da ababen cewa

“gudnite.. ta furta slowly batare da ta jira amsar sa ba ta bar wajen da sauri bayan ta yabi da kallo yana me lumshe ido can ya sauke ajiyan xuciya ya shiga room din su.

Kwance ya tarar da hamidar idanun ta a lumshe tayi shiru dan haka ya shirya da sauri shima ya biyota kan gadon.

Wani wawan runguma da zafafan smooches ya bata wanda yasa tuni suka dulmuye juna cikin shaukin so da raya daren su cikin kyakwar shakuwa

Can Bayan sun kimtsa ne yake tambayarta ko dagaske sun gana da fifin,eh kawai tace masa batare da nuna masa komai ba.

Yasan matsayin fifi a zuciyar hamida dan haka yaso yaji ko maganan cikin ma ya dame ta amma haka fir taki ta bayyana masa komai.

Fifi kuwa tana barin wajen su ammy suka rike ta da sabuwar hira da tarairaya dan samu tayi har hajja ta kira daddyn su tana kai masa gulman

Sosai tayi farinciki dan acewarta murnan ta kashi biu ne,musamman in ta tuno da yadda akayi auren,da tunanin cewa yau ko fifi ta mutu abunda ke cikinta zai zame musu sassaucin jin zafin rashinta a duniya da zasu zo suyi

itama fifi karban wayar tayi tafi awa suna hira me dadi da shi su hajjan na tayasu musamman da kowa ya san cewa by now saheeb yana tare da muhibba ne so Anan site dinsu ta kwana.


Bangaren saheeb
Suna shiga dakin muhibba ta hade rai ta kau da fuska tayi zaman ta a bakin gado batare da tace masa uffan ba,kallon ta yakeyi direct dan gaba daya alamomin fushi da zafin kishi sun bayyana a fuskan ta amma dake halayyar sane kamewa da shan qamshi sai yaki yace mata uffan
shima,wani zaman kurame akayi a dakin shiru ne ya ratsa tsakanin su ko minti biyar basuyi cikin hakan ba ta mike fuuu ta wuce bathrum tana me buga kofar da dan karfi kayan jikinta ta sauya zuwa towel ayayin da kuka me tsuma da cin rai ya kufce mata kan gwiwarta ta sauka tana zubda hawayenta sosai tana kuka tafi awa guda a hakan

saheeb dake zaman jiran fitowar tan Tun baijin sautin kukan har ya tsinkayo Da kamar bazai je ba can dai ya daure ya kai kansa bakin door din bayabo babu fallasa ya kira sunan ta amma ko sau daya bata kulasa ba

Sunfi mintuna talatin ahakan har abun ya dame sa sosai dan dolen sa ya Soma halayyar maza na rarrashi wanda sam bai saba ba.

Wai meke damunki haka ne?
“Can u please come out lets talk?

Wai miye hakane muhibba,i hate wen u act childish…open the door

Tanajinsa tayi shiru abun ta Da can kamar zata amsa sai kuma ta tuno da cewa ranta a matukar bace yake a yanzu,tana bukatar nitsuwa da samun kyakkyawar ganawa da hamida kafin ta san matakin da zata dauka me gaba daya.

Jin har yanxu bata kula sa ba yasa ya harxuka tsaki yaja ya bar mata dakin ya nufi nasa yayi kwanciyar sa se can ta fito ta kimtsa ta hau gadon ta ta kwanta abunta

Juyi take acikin ranta cikin tunani me xurfi babu wani abunda take s akawa face yadda zata bullo masa da Shi da matar sa ta hanyar da zata fi iya cimma burin ta cikin sauki.

Mamuh

[8/12, 12:08 PM] Nadady: 32

Washe gari da safe koda ya dawo duba muhibba ya samu kofarta a kulle Tsaki yayi Bai sake dawowa Nan ba direct ya nufi sashen su ammy ya gaida su tare da duba lapyar Fifi wacce take Nan lafiya lau Dan bakaramin kulawa da ita yau akayi ba tsaban zumudi har sun shirya lokacin da zasu je asibitin Dan Khalid yace zai duba ta acan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button