KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Suna ta shirmen su Dan haka Bai wani jima anan ba ya fice da sojojin sa daganan basu sake jin duriyar sa ba itama fifin anan tayi zaman ta saidai duk Abunda ake Mata na nuna tsaninin kula da gata Bai wani dame ta ba Ayanzu ba.

By 4pm suka dawo daga asibitin bayan Dan karamin yawon bude Ido da sukaje dukan su su ukun ita da ammy da hajja, khaleed yana asibitin sa ita Kuma hamida tana gida tare da muhibba Babu Abunda sukeyi yau Sai kulle kullen su na Sanin Abunda zasuyi akan fifi

Kuma duk tarayyar sun Nan Babu Wanda ya sani sabida hamida takan nuna ma kowa cewa ita Sam Babu ruwan ta da rayuwar kowa face na mijinta ta khalid Dan haka wani bin ma ko cikanki Bata cewa muhibba a fili.

Itaman muhibbar dake ba sarar su bane ko a shekaru Sai rashin kula junan sun Bai Ba kowa mamaki ba Amma a zahiri kusan hamida ce me asalin dorata akan gayyar kishi dake tsokalarta a xuciyarta

Tsaf suka kammala hade haden su ayayin da kowacce ta koma site dinta tana abubuwan daya dame ta.

fannin fifi kuwa a fili ne kawai take yawan murmusawa Amma aranta wani uban kadaici takeji me nauyi She really feel alone,har cikin zuciyarta take jin kewar rayuwarta na da can Wanda Babu fargaba ko kiyayya rayuwar da Bai nisantar da ita da soyayyar yar uwanta ba

Bayan ta idar da ishai Wanka tayi a site din hajja ta sauya shiga xuwa simple white Milano gown marar nauyi ta sakaya hular sakanta shima white wani boyayyr damuwa rashin jin saheeb tun safe shiyake cike mata kirji Yana damun ta har kwakwalwa tanajin zafin Abun Yana shiganta a hankali

Numbar San ta dada dialing daga bisani ta jefar da wayar tabi lapiyar gado tana me lumshe idanun ta sosai Jin kamar baxata iya dauriyar ba ta bude Tex messg ta soma rubuta mashi Sako’
Hy can u please come home Ina son ganin ka,Sai ta goge ta rubuta Salam,kana lafiya pls wen r u coming back? ta rubuta messages yafi sau goma tana gogewa
gaba daya sai ta rasa me xata ce Wani baccin baxata ne yayi awon gaba da ita da wayar a hannun ta hajja ce ta rabata da wayar Bayan ta Gama karance sakon ta na karshen da ta rubutu Bata goge ba murmushi tayi sannan ta gyara mata kwanciyarta.

Wajajen karfe 10 saura saheeb ya dawo sashen sa ya nufa straight ya kimtsa kansa cikin kananan kaya sannan ya taho ya same hajjan dake yau ita daya ya samu tana zaune ta toshe da medicated glass da qur’ani a hannun ta tana dubawa.

A ladabce ya rusuna ya gaida ta ta amsa Masa cikin faraa,duk daama tasan baxai wuce aiki ne ya Sha kansa ba Amma sanda tamai tambayar hakan..

Ce mata yayi muhimmin meeting ne ya ritsashi yau da ogogin sa ko lokacin kansa Bai samu ba

Tace Allah ya bada sa’a yace amen zai mike yay waje ta sanar da shi cewa Fifin tana Neman ganin sa Amma tana bacci ayanzu karamar aajiyan Zuciya ne ya kufce masa tuno da condition dinta Sai baice uffan ba yayi murmushi can yace abarta tayi baccin ta zai zo ya dubata gobe.

Sallamar su ke da wuya ya nufi dakin muhibba Wanda ya same shi a wangale Abun ya basa mamaaki Sanin cewa Bata Saba hakan ba

Muhibba mace ce Mai strict mind Ita irin matan Nan ne da suka taso cikin Sanin aikin da ke gaban su mace ce kamar maza,kusan Kowani lokaci inta xauna tunanin Abu daya ne ke xuwa a mind dinta wato business din mahaifin ta Daya Dora ta akai tana juyawa,saidai ayau labarin Tasha bambam dan kuwa bakaramin tsananin kishi ta sa aranta game da Fifi ba

Gani take Kamar ita daya ce macen da kawai zata iya rayuwar ta da saheeb batare da rayuwarta Dana familynta ya ruguje ba,ayanayin data ji labarin Fifi Sai taji aranta Sam Bata bukatar wacce zata zo ta mantar da saheeb tsawun rayuwar da suka Gina na hakuri da juna da burin ta na son xuciya data Dora Auren nasu akai.

Dan jitayi Kamar ma baxata sake iya komawa aikin ba Kuma da ta rasa saheeb wajen fifi kamar yadda hamida ta fada gani take gwara duk Abunda xai faru ya faru.

Can cikin wannan tunanin taji sallamar sa akanta,mikewa tsaye tayi batare da ta amsa ba ta kallesa cikin wani yanayi Mai nuna zafin fushin dake aranta..

Inba dan burin mahaifin ta ba da saheeb shine Abu na farko a rayuwarta
Dan bakaramin kaunar sa takeyi ba

How can she loose him?tana furtaa hakan aranta ta dada harde rai batare da ta kulasa ba ta taho xata wuce ya jawota baya suna kallon juna yace

Nayi sallama baki amsa ba and where are you going?

Kanta ta kawar gefe ya bata rai yace pls..bana son shashancin muhibba wai meye aka Miki ne?
Tun dawowarki ma munyi magana ne

Hannun ta ta fauce anashi slowly ta kallesa da wani irin yanayin dayaji Babu dadi aransa Sai taja baya dashi kadan tana maida ajiyan xuciya”ta masa kallon me zance maka?

Can Tace ok happy married life..end.

Xata fixge jiki ta fice ya dawo da ita a Dan fusace yace ohh dama Abunda ke damunki kenan?su ammy basunyi Miki bayani ba?what….bai kareba ta tsare sa

“Ba su ammy nake aure ba saheeb bazaman su nakeyi ba meyasa Kai bazaka tabayin Abun da ya dace arayuwanka ba
U asking me to act matured?baka taba gayamin kayi auren soyayya ba u Neva Care abt my feelings Mr matured.

A fusace ta furta hakan cikin bacin rai fuskanta a matukar bace

Sai ya Bata ransa sosai yayi shiru

..kuka me sanyi ta fashe Masa da shi cikin kukan Tace dama nasan Daren dadewa hakan xai faru Amma ba damuwa ta bace dan kanuna gajiyar xamanka da ni cikin sauri haka

Jajeyen idanun ta ta Dora anashi muryan ta na rawa sosai tana tsuma

Saheeb xaka haifu da wata mace?tun kan ya amsa tace oh well congrats,irin dariya Mai cin rai din Nan ta karashe da shi alokaci guda tana kan tuntudo da hawayen ta masu rauni..tace
Ashe har xaka iya min hakan saheeb?mekake Shirin aikata ma rayuwata

A dame Yace muhibba menayi?nima fa cemin akayi na taho za’a min Auren nan I Neva even know anything wai meye haka?

Tace Babu..Auren da baka sanda shi ba gashi har xaka haifu ko? nikuma matarka ka hanani haihuwa,saheeb u encourage me
To plan na dauka rashin Samun nitsuwa a matsayin muna aurata shine dalilin mu Ashe Abun ba hakaa bane,Abun Isa ne,fifiko ne da nuna bambancin dangantakar da ke tsakani Wanda ni bani da shi dakai

A hankli Ya furta ya subhanallahi,u completely misunderstood me muhibba duk abunda kikagani qaddarar Allah ne kawai I didn’t plan anything

Tace yes. U didn’t nagane ai,anawa fannin ne ka tsara komai amma Kuma ana wata Allah aka barma ya tsara

Yayi firzan iska
” ya kike magana Kamar bani dake muka tsara maganan haihuwar mu why r u blaming me now

Tace,eh nidakai mun tsara hakan amma ai haihuwa zakayi da wata yanxu kuma gani nake Kamar nawa mahaifar ya same matsala saheeb pls u can’t do this to me

“Kasan Auren ka baxai dameni ba Abunda ya dameni shine mahaifata da kabada gudumawar muka lalata sa.
I can’t bear seeing my life childless musamman in wata mace xata haifa maka da a duniya kasa hannu ka karba.

Wani runtse idanun sa yayi yana jin tambayoyin ta suna fitowa cikin rawan murya a raunane

“What abt me?bazan haihu ba kenan?ka cuceni kenan?..kuka me Karfi ta rushe da shi sanda ya ji gaba daya hankalin sa ya tashi sosai xuciyansa na bugawa.

Babu irin maganganu marasa dadi da Bata furta Masa ba,gaba daya kansa ya daure ya rasa lefin sa ne ko nata,har kasan xuciyan sa ya soma jin Babu dadin abubuwan datake furtawan

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button