KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

“Hey,..Do not touch Again, ko ce miki akayi ban iya ba?

Tace,ai baka da Gashin…ya za’ayi
Ma ka iya?..Ni daI zan taba ta turo bakiA fakaice ta dubi mirron ta ga yadda ya gyaro ta tayi kyau Daya dan juya zai nufi wardrobe

Itama A sace ta lafe tana kallon sa,har cikin ranta taji ya burge ta sosai wani ssbuwar son shi takeji aranta

Wani pink shot marar nauyi ya hada da wani mini half vest mai siririn hannu ya taho Mata da shi…”cikin ranta cewa take yau dai naji jiki..

Haka ya matsota Cikin salo shi ya saka mata Kayan yana yi hannun shi na aiko mata sako har cikin kwakwalta lumshe ido tayi Ta Kame Sa

Yace
Kinyi sallah ko?dazu nazo kina bacci..Ya tambaye ta sai ta gyada kai batare da ta bude idon ba

Sungomota yayi ya ajiye ta akan gado a mike ta gaba flat bayan ta yana resting tana kallon shi,hannun shi ya mIka kan lamp ya rage wutar dai dai yadda take bukata

haka ya dinga mata yawo da yatsun sa a ciki har bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita Dan kadan ya juya ta gefen dama yana mai gyara mata kwanciya

Bayan shafe ta aduoi..Kiss ya dora mata a goshi sannan ya janyo Comforter ya rufe ta da shi Sannan ya koma room dinsa.

mamuh33

Lokaci na tafiya kwanaki na ja watanni na matsawa rayuwar cikin gidan su Ammy komai na samin sauyi,yadda lkc ya ja,haka abubuwa suka yi ta faruwa dan kuwa bayan sa’insar da Saheeb yake samu da matar sa Muhibba a boye ta kuma dago wani rikicin da sai da dan dole ya saka ta tafiya asibiti dan a duba ta.

Da ta shirya ta tafi sai ta kasa aiwatar da komai dan dama uterus din nata yayi weak ne amma bai lalace ba kamar yadda take ta ririta laifin Saheeb akai ba..

Sai da ta kira Hamida a waya ta fada mata abinda ake ciki sannan suka yi kuleleliyar su suka samo mafita wanda Muhibba ta yi na’am da mafitar har ta hau kan koyarwar mafitar..

Ko da ta isa ga doctor,ra’ayin ta ta fada mai sai suka yi abinda zasu yi ta karbi maganin karya na depressant wanda inta sha zai taimaka wajen nunawa kamar bata da lpyar da wani shiryayyen written document lafiyar ta lau ta dawo gidan da shi tun shigowarta take masa bayani.

Da fari Saheeb bai so ya saurare ta irin sosai din nan ba dan shi kan sa abubuwa sun mai yawa ya rasa ta ina zai fara tunkarar abin but seeing and reading her health profile sai ya ji wani karamar tsoro ya shige sa,abinda ke ciki shine wai ta sami matasala da mahaifar ta ya lalace ba zata taba iya daukar ciki ba sannan samun wannan matsalar zai iya haddasa mata damuwa sama da shekaru but ayanzun ma damuwar bai kai wani mataki mai tsanani ba

har sai a ƴan kwanakin nan da saheeb bai nuna damuwar sa akai sosai ba,tasha maganin saka damuwa sosai dan haka ta zama kamar me boyayyen brain trauma kuma she is affected emotionally and psychologically tace masa akan haka za’a bata magungunan da zasu taimaka mata ta sami natsuwar zuciya dan batun haihuwa babu shi a gare ta dan ba yi zata yi ba…

Fifi tana laulayi sosai dan haka take rigata fitowa tayi aikin komai badon Allah ba saidan ta cusa ma saheeb jin cewa ta zama abar tausayi mara amfani a tsakiyar su

Duk iya nuna rashin kulawar sa sanda abun yazo yana damun sa sosai

Muhibba ta faɗa cikin mata masu matsala tana buƙatar kulawar mutane musamman shi da ya ɗora laifin a kan sa kusan completely tunda shine mijin, tun farko da bai bada yardan sa ba da babu abunda zai faru.

Bayan wata uku ta turo likitan ta wajen sa da bayanai masu tsoratarwa burin ta baifi ta datse tarayyar dake bunkasa cikin sanyi tsakanin sa da fifi ba

Da Saheeb ya gama ganin doguwar sharhi sai kawai ya rusuna kai gaban Muhibba dake ta kuka mai tsuma zuciya tana nuna nadamarta da ciwon rasa gurbin haifar nata dan a duniya,rasa me zai ce mata yayi sai kawai ya rungumo ta ya hau bata haƙuri da nemar yafiyar ta sannan ya nuna cewa laifin sa ne ya kuma yi mata alƙawarin ba zai taɓa barin ta ita kaɗai tana jin raɗaɗin wannan rashin haihuwar ba dole su yi sharing tare dan ko masana da suka yi mgnan su akan family function ba iya ga mai cikin suke nufi ba actually akan family burden da matsala suke nufi shi ya sa suka ce responsibilities of a pregnant woman is shared between all sundry toh ba mai ciki kaɗai ba har da member dake cikin matsala kenan

tun wannan rana Muhibba abin nema ya samu,ko girkin ta ko ba nata ba zata san nayi har sai Saheeb ya kulata yanzu baya son ganin tana cikin damuwa dan haka bai cika yin nesa da ita ba,hakan ya mata daɗi dan ko ba komai tana samin attention ɗin mijin ta..

A fannin fifi dayake saukin kai da sassaukan zuciya ne da ita sai bata dauki abin komai ba,gashi ya saba mata komai da kanshi sai kuma ya zo a daidai lkcn da ta fi buƙatar shi sama da kowa a duniyar shi kuma ya fara juya mata baya.

A kullum tana ƙara son sa tana ƙara ƙaunar babyn su dake tare da ita sai dai tun abin baya damin ta har ya kai ya kawo abin ya fara ɗaga mata hnkl..

Kishi ne me zafi yake cinta, A ganin ta ba komai Saheeb ke nuna mata ba sama da tausay,dan tana ganin yanzu matar sa ta dawo so bai da lkcn ta ita sai na matar nasa,dan har a wurin cin abinci yana kafa kafa da Muhibba wannan dalili ya sa ta rage zuwa wurin cin abincin dan kar ta rinƙa ganin abinda zai riƙa ɗaga mata hnkl..

Takan zauna tayi kuka ta roƙi Allah ya yaye mata wannan damuwa nata haka zalika takan zauna ta rinƙa tmbyr kan ta ko laifin me tama Saheeb ɗin da ya daina kulawa da ta sosai haka..?

Sai yanzu take gane zafin son da baida amfani,ciwon dake cikin kyaliya sharewa juya baya da wahalan dake cikin nuna fifiko wayanda ta saba da sabanin su tun farin rayuwarta..

Wani lkcn zataji kishi sosai, zuciyar ta kan bata amsa da ai tunda kin fara nauyi hala shi ya sa ya daina sauraron ki dama fah kar ki manta auren haɗi aka maku ke da shi ba soyayya kuke yi ba..

A kullum in ta tuno hakan sai ta ji zafi a zuciyar ta ta kuma rinƙa ganin laifin zuciyar ta da ya bar ta tana makahon soyayyar da bata san kansa ba..

Dai dai da rana ɗaya Saheeb bai taɓa yunƙurin zama da fifi dan sanar da ita komai ba musanman akan current health situation ɗin Muhibba,dalili kuwa shine shi yana da miskilanci da ganin in mutum ya ga abu ya faru ai ya san da dalili ba sai ya bi mutumin ya mai bayani akan abinda ya farun ba kuma,sannan yana ganin shi ɗin ba yaro bane da zai yi ta bibiyar yara kamar bai san me yake yi ba..

So duka waɗannan tunanin su suka taru suka bada gudunmawa mai ƙarfi wurin nesanta muamalr su sannan zargi mai ƙarfi ya ɗarsu a zuciyar ta ta yadda take ganin kamar yana so ya ci amanar soyayyar ta ne dan ta daɗe da gane ƙarya yake mata ba son ta yake ba wani abu yake so a tattare da ita da ya janyo sa gare ta…

Duk kuwa yadda su Ammy da Hajja ke bata kulawa da kariya daidai gwargwado hakan bai ishe ta dan duk daɗin ka da mutani in har kana da matsala da gidan auren ka toh babu wani daɗi..

Tana nuna jin daɗin hakn amma aranta ta fi buƙatar shi mijin nata kusa da ita sama da kowa da komai sai dai hakan bai yiwu ba dan ganin sa ma sai yana so ya zo ya zame mata da ƙyar.

Rannan tana zaune a garden ɗin gidan tana aikin kullum wato tunanin sa da rayuwar su sai hawaye ya fara zubo mata dan bata saba da rashi ba,kamar tana son abu amma ta rasa sa,sam bata saba ba komai take so ana mata shi saidai a yanzu auren da tayi tana buƙatar abubuwa da dama daga cikin sa amma an kasa sama mata shi ta kasa samin waɗannan abubuwan dama da gaske in har mace tayi aure gatan ta ya ƙare dole ta fuskanci gidan ta ita kaɗai?in haka ne ita zata bada lbrn faruwar hakan dan dai gata iya gata babu wanda bata samu but cikin gidan ta ya zame mata kamar wuta bata iya kashe wutar sai dai in guje mai da ta yi dan komawa sashen su Ammy da zama tayi ba kasafai take zuwa nan nata sashen ba sbd gudun ɓacin rai…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button