KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS
Hannu ta ji a kafaɗar ta sai ta ɗago ta kalli hannun sannan ta kalli fuskar mamallakin hannun take ta kawar da kan ta tana cigaba da zubda kwallar ta..
Ta gaban ta ya zago ya zo ya zauna a kujerar dake fuskantar ta haɗe da riƙo hannayen ta yana murzawa..
Tana jin abin amma ta ƙyale sa bata tanka mai ba shi kuma bai hana ta kukan ba dan a ƴan kwanakin nan yana ɗan lura da halin rashin natsuwar zuciyar da take ciki sai ya daure ya binciko ta inda ya gan ta a nan garden ɗin ya kuma ƙudirta sanin matsalar ta..
“Me ke damin ki”?tmbyr da ya mata kenan sai ta kalle sa irin u are bluffing ɗin nan sai ta kawar da kan ta tayi shiru.
Juyo da fuskar ta yayi suna kallon juna for a while sannan ya furta
“Am sorry”a hnkl abin sai ya bata mamaki wato ya san ya mata laifi kenan..
“I truly am”.ya kuma maimaita mata sai ta cigaba da yin shiru har dai dan kan sa ya fara rarrashin ta da alƙawarin making up mata da haka dai ya kalailaye ta a sannu har ta sauko daga dokin fushin ta saurare sa.
Tsakanin Mata da miji sai Allah,kalau suka shirya ranar haka tun safe har yamma fifi ta kasance cikin annashuwa da farinciki duk da bai zo inda take ba hakan ma yayi tunda ya bata tym da attention ɗin sa a ranar…
Sannu sannu rayuwa ke ta tafiya ahakan Saheeb yayi ta disappointing fifi kullum tana saka shi abu bata samun yadda takeso haka zata gaji ta cire tunanin a ran ta shi kuma bai taɓa tunanin ya take ji ba in bai nuna mata komai ba..
A ɓangaren su Hamida da Muhibba kuwa abubuwa sai gaba suke yi kamar ba za a daina numfashi ba dan kullum sabbin abubuwa suke ƙarawa akan na da sun yi nisa basu jin kira kuma duk wannan abin babu wanda ya san suna yi daga su sai su..
A kwanakin nan ne Muhibba ta fara jin wani irin abu a jikin ta kamar dai bata lfy,tun tana ɗan daurewa da kawar da kai har abin ya fara fin ƙarfin ta dan kuwa matsanancin ciwon ciki ke tasa ta gaba ba kaɗan ba amma bata da yadda ta iya dan dole ta kuma samin attention ɗin mijin ta wanda hakan ya kuma datsawa a rayuwar auren Saheeb da fifi
abubuwan sun kacame ma fifi ta yadda hakan yake nufin tana buƙatar attention ɗin wani da shawarar wani,but wa zata fuskanta ne bata sani ba..
Tana zaune wata ranar alhamis sai ta ji tana son ganawa da ƴar uwar ta duk munin naka naka ne ko da korar ta zata yi zata tafi ta faɗa mata damuwar ta maybe ta sami mafita..
Fita tayi zuwa sashen Hamida inda da ƙyar ma ta sami attention ɗin Hamidar,abu na farko da ta fara shine kuka mai tsanani da ratsa zuciya sai Hamidan ta natsu ta fara sauraron ta inda ta rinƙa karanto mata damuwar ta..
Gwanar tausayi Tace “Hamee am not happy wit my marriage,rayuwar aure na bai min yadda ya dace komai nawa ya fitar min a hannu na rasa ya zan yi,yaya Saheeb baya bani lkcn sa,bana samin kulawar sa,Hameda ban san makoma ta ba ban san laifi na ba,haka tawa jarabtar take ni kuma?fixing aure na kan sa na kasa yi?am pregnant but the father of my baby isn’t ready to take care of me and our baby ya zan yi hakan ni kaɗai?bani da uwa i don’t have any one sai ke” bzan iya kai damuwata wajen su ammy ba hamida,Hamida ki taimaka min dan Allah..
.”da kuka mai taɓa zuciya fifi ta ida mgnr..
Sosai jikin Hamida yayi la’asar ta kasa haƙuri har ta janyo ƴaruwar nata tayi hugging nata tightly tana petting bayan ta cikin tsananin tausayi tana fidda sautin
“shhhh” a hnkl..
Kuka sosai fifi ke yi kuma kukan na ɗan taɓa ta a zuciyar ta ba kaɗan ba sai dai abinda bata sani ba shine,shin ta taya ƴaruwar ta yaƙin samin natsuwar mijin ta gare ta ne ko dai a’a ta bar ta ta cigaba ne ita kaɗai ba tare da ta taimaka mata ba?
Mamuh
34*
Murya ƙasa ƙasa kamar mai tsoron yin mgn Hamida ta fara yiwa ƴar uwar nata kalamai masu daɗi da sanyaya zuciya dan ba ƙaramin tausayin ta ta ni ba duk da yadda take ji a game da fifin bai sauya ko kaɗan ba a zuciyar ta but tana ganin kamar in ta ƙyale fifi cikin damuwar da take ciki akwai matsala..
Ɗagowa fifi tayi tana kallon Hamida dake ta rarrashin ta,mantawa tayi da Hamidar tana fushi da ita sai ta kuma faɗa mata wani sashe na halin Saheeb wato rashin kimanta adalcin da yake yi a cikin gidan tsakanin su matayen sa..
Hamida da hnkl ta ya koma kan ƙulalliyar da suke yi ita da Muhibba akan yadda zasu takura fifi sai ta ji gaban ta ya faɗi ta rasa inda hnkln ta ya tafi kawai sai ta ji ruwa ya ciko mata a ido sai dai ta danne bata bari ya zubo ba ta kuma rungume fifi tana ce mata
“Na maki alƙawarin taya ki addu’a da samin ƴancin ki a gidan mijin ki i promise u”
Ba ƙaramin daɗi Mufida ta ji ba sakamakon jiyo waɗannan kalamai daga bakin ƴar uwar ta after many months of shunning her..
Da kalamai masu daɗi Hamida ta kwantarwa fifi hnkl har ta raka ta zuwa bakin gate ɗin sashen ta ta komo ciki ta zauna tana ta tunani ita kaɗai akan abubuwa da dama..
Fifi kuwa ɗakin ta ta nufa dake sashen su Ammy ta kwanta shiru tana shafa cikin ta,cikin ya fara girma har ya bayyanu ta yadda duk wanda ya gan ta ya san mace ce mai juna biyu..
Sanyayyan hawaye ne ya zubo mata a kumatun ta ta saka hannu ta goge tana gyara kwanciyar ta,a ran ta take ayyana dama zata iya juya hannun agogo baya da ta juya ba dan komai ba sai dan ta goge sashen Saheeb dake cikin shafukan rayuwar ta.
“Ina ma a ce zan iya,ina ma a ce ni Mufida zan iya goge ka gabaɗaya a rayuwa ta yaya Saheeb,ina ma a ce zan iya ciro zuciya ta in wanke inda sunan ka ya taɓa a zuciya ta sannan a mayar cikin ƙirji na,ina ma a ce ina da iko da zuciya da zan bata umarnin daina haska min kai da take yi a kai a kai,da da yadda zan yi da na yi ko dan in yaye ka a rayuwa ta dan ni kaɗai ke iyo a zurfaffen ƙaunar ka kai baka yi,ni ke soyayyar ni ke ƙaunar haka ni ke fuskantar hukuncin Ƙaunarmu isn’t it too much for me all alone”?ta ida mgnr tana mai fidda kuka mai sautin gaske da tsantsar tausayin kan ta..
Tana ta kukan har bacci ya ɗauke ta mai tsanani,Hajja dake bakin ƙofar ta tana ta jiyo shesheƙar ta haka tana sauraron maganganun ta ta turo ƙofar ta shigo a hnkl ta isa inda fifi ke kwance a kaikaice.
Kallon tausayi ta ma fifi sannan ta matso dab da ita ta mata addu’a ta gyara mata kwamciyar a hnkl gudun kar ta tashe ta daga baccin kar ciwon kai ya dame ta…
A ɓangaren Hamida abubuwa babu sauƙi dan ranar a wani yanayi ta yini har mijin ta ya dawo ya same ta a haka nan ya tmby ta damuwar ta but ta kasa ce mai komai sai langaɓeai da take ta yi a jiki,duk ta yi sanyi hnkl ta baya jikin ta halin da ƴar uwar ta ke ciki ba ƙaramin takurawa zuciyar ta yake ba..
Haka dai Khalid yayi ta fama da matar nasa hatta da abinci sai da ya karɓo masu a cikin gida dan kasa aiwatar da komai tayi,kkrin da tayi na girka abincin sai da ya ƙone ƙaurin sa ya cike gidan kaf da rana shi ya sa da yamma ya shiga wurin su Ammy ya karɓo dinner…
kamar ƙiftawar ido cikin Fifi ya kai wata shida gab da na bakwai,babu abinda ya sauya a zamantakewar ta da mijin ta Saheeb,alƙawarurruka kam ta sha ta har ta gaji har ma ta daina yarda da shi da kalaman sa dan faɗa yake yi baya cikawa..
Sashen Muhibba kuma rashin lfy sai daɗa gaba yake yi ciwon ciki matsananci kullum cikin ta take na yau na ɗare na jiya,sannan depressant da ta karɓa tana sha bata daina sha ba..