KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Duk yadda dadin kalaman suka karbu suka kuma sanyaya zuciyar ta suka ratsa ta hakan bai sauya mata jin komai ba dan kuwa babu sunan ta a jiki sunan yar uwan ta mufida ne Kenan sakonnin na mufida ne saidai bata ga sunan wanda ya aiko ba
Jiki a sanyaye ta mika mata batare da ta nuna yanayin data tsinci kanta na kishi da jin haushi akan fuskan ta ba.
Nan fifi ta amshe sakon tana kan tambayarta nawaye?wani shiru ne kawai ya ratsa wajen har fifin ta kammala karantawa dakanta ta dago idanuwan ta da zimman yin nazarin wanda zai iya aiko mata kyautar
charaf sai idanun ta suka sauka akan wani abu,shima a killace yake shikadai ana shi gidan a gurguje fifi ta dauko shi ta budeShi
Wani abun wuyar danyen dutsen safaya(saphiere)ne kalar sa ya shiga ja sosai yana faman sheki kamar asalin duwatsun diamond
Design din bana engine ko bugun kamfani ba bane asalin hannun kwarancewa ne ya tsara zaman zanen aka dedeta siffar duwatsun ta inda zaiyi matukar kyau wanda ko kallo daya bazai ishesa ba
Wannnan shine abun wuyar data gani a wani jaridar london times tace tana matukar sha’awar sa kuma tasan wa dady kawai ta nuna sukayi hirar kenan shi ya mata wannan sakon?tunda in ba shi ba babu wanda ta taba gaya ma wannan zancen
Daga yanayin yadda yay tsaye yana kokrin saka fuskn tausayi ta fahimci cewa tabbas shi din ne da wani irin gudu ta taho ta fada jikin sa ta saki wani irin kukan murna da tsananin kaunar sa
Tace. “Dukkan wayannan nawa ne? Nagode dady na Suna tayi dai hamida batace musu uffan ba
Wani shiru tayi agefe tana kallon su cikin tuno da Allah me kyautar kunci,..
Agaban ta mahaifin su ya tallafo fuskn fifin yana gaya mata maganganu masu dadin ji,yana me tabbatr mata cewa zai iya sallame dukan arzikin sa da komi nashi a duniya domin jin dadin ta da samun kwanciyar hankalin ta,kayan data sa ajikin ta kalar ja ne dan haka ta warware abun wuyar kamar zata kwama sai ta kuma ta fasa ta dawo tana kallon yar uwanta hamida dake kwakwulo murmushi da kyar
Da faffadan nurmushi fifi ta karaso wajen ta tana me damka mata abun wuyar tace hamida sakamin”ba musu hamida ta karbe,fifi tana ta surutun ta cikin bata labarin abunda ya wakana alokacin da sukayi hirar da daddy.
“Wani irin kishi da damuwa shi yake cin zuciar hamida amma ahakan ta daure ta shiga dannewa da tattausan lafazi tana amsata cikin sautin murmushin ta me fallasa tsananin kuna da ciwo
Warware abun wuyar tayi ta zago da shi a wuyar fifi tana malkaya mata last hook din abun wuyar,yadda ya xauna a wuyar fifin yay matukar kyau ya dada sawa takeji har can cikin ranta dama ace itace ta mallake sa..
Dauke kai tayi cikin sauke maganganun zuci a cikin dukkan tarin kyautattukan nan yanzu babu nata ko daya aciki?
Ta gama fahimtar cewa Bawai ana mata hakan dan ba’a son ta bane mancewa da ita akeyi agabanin farincikin yar uwan ta
Yaya zataji aranta me takeji duk babu wanda ya taba yin la’akari da hakan.
Zama sukayi dukan su suna cin abinci suna hirar ban kwana still wani shiru hamida tayi tana tura abincin bakin ta kadan kadan sakamakon rashin dadin sa datakeji abakin ta
Bayan sun gama sun fito zasu wuce nan ma su dr fatima yonas da yayan ta duka biyun suka tada nasu wasar inda gaba daya suka fi bada muhimmanci da kulawar su akan mufida,har hawaye sukayi ma juna alkwarin zasu na kirar ta sunyi shi yafi abun a kirga
10am na safiya suka isa aiport babban jirgin zirga zirga na kasan shiya kawo su nigeria aqashe garin ranan asabar karfe 2 na rana..
Kusan dukkan mutanen familyn sune suka zo tarban su,yayar baban su ammy khalid harma da kakar su hajja…
To Hamidar ce ta soma isowa garesu domin ta bar mufida acan baya tana famar tattara nata kayan.
Kallo daya ta musu ta gane su inda ta taho,nan suka tarbe ta da murna da fara’a ayayin da dukkan hankalin ta ita kuma ya koma kan kyakyawar hadadden namijin dake tare da su wanda take kyaun tsammanin cewa shine KHALID MAKARFI wato yaron ammy na biyu
zuciyarta ne ya shiga tsananin bugu ayayin da suka kalle juna suna masu sakar ma juna murmushi me sanyi
Su ammy da hajja kuwa sai tambayar ina fifi take?da alaman ita kawai suka fi so su gani so tsaban nuna zakuwar su da rawan jikin su ko hamidar ma bata iya samun damar nitsuwa ta amsa su dakyau ba
Haka kawai hamida taji khalid ya mugun dauke mata hankalin ta domin kuwa babu marabar sa da irin namijin data ke muradi a zuciar ta wanda takejin duk duniya da shi kawai zata ita rayuwar ta
Daga yanayin yadda suke satar kallon juna hajja tayi murmushi sbd Shi khalid dama yafi yayansa SAHEEB MAKARFI sakewa dason mu’amala da mutane Kuma gidan kaf yafisu rashin qyamar mutane yafisu fara’a da tausayi Dan komai na uwarsa ammy ya dauko
Sama sama suka gaisa da shi sai ya dan kawo Hannun sa zai karbe Troleyn hannun ta yana mikowa kamar daga sama yaji an wani tunkude sa a mugun razane ya dago kansa ya juyo inda yayi gamo da wata kyakyawar surar data dauke mai numfashi atake ta kuma tafiyar da shi sumewar tsaye yayi yana me tsura mata brown eyes dinsa cikin yanayin da ba sai ka tambaya ba
Hakika yasan yau yaci karo da muradin zuciyar sa
Mamuh_KNM_
PLEASE SUBSCRIBE
5
Idanun sa kyar a kan wannan kyakyawar surar da ya zamo mai abu mafi haske tun tashin sa daga safe zuwa wannan lokaci..
Fifi kuwa Hankalin ta ba a kan sa yake ba sai kan yar’uwar ta mafi soyuwa a gare ta wacce ita kuma hamida gaba daya nata hankalin a kan na Khalid yake sakamakon taimakon da ya kawo mata wanda ita a zuciyar ta ji tayi kamar shima ya fahimci wani sirrin dake zuciyar ta ne da bai jima da darsuwa ba..
Da fara’ar ta cikin maido hankalin ta ga Hamida ta shiga daga mata hannu tana mata nuni alamar ta zo ta taimaka mata trolley din ta ya budu har kayan ta suna shiri zubewa ga kuma sauran tarkacen ta da take kan kwasowa daga jirgin..
Khalid dake daf da rike trolley din Hamida a hannun sa idanun sa gaba daya yakoma wannan kyakyawar surar rasa abin cewa yayi,yana iya fadawa zuciyar sa cewa tunda yake tunda yake mu’ammala da yan mata masu ji da kyawun fuska da kyawun dirir halitta bai taba dirar da idanun sa kan mace mai irin wannan surar ba,ba wai hasken ta ne ya rude sa ba a’a,tsantsar kyawun ta ne ya ja hankalin sa a haduwar idanun su na farko..
Hamida dake tsaye tana kallon ikon Allah ganin ita ce aka zo taimakawa da daukarwa kayan ta amma kuma an tsaya ana karema yar’uwar ta Mufida kallo,kallon da ko makaho ne ya san ba kallon da kowa kewa kowa bane,cikin wannan kallon akwai abubuwan fassarawa da dama sai dai in mutum bai da lura da la’akari akan abubuwa..
Ganin Hamida tayi tsaye ta kasa responding mata kuma har yanzu babu wanda yayi la’akari da zuwan ta sakamakon shigowar baya da ta yi kuma ba wani magana tayi ba bare muryar ta ya ankarar da su cewa ta iso,shi kadai Khalid din ya san da zuwan ta acikin su sai hamida dake tsaye..
Maida dubar ta tayi ga Khalid din dan ganin wa ta buge a rashin sani nan take idanun ta ya sauka a kan kamanni jini da suke danyi da daddyn su..
Wani irin kallon karshe ta mai a kyau,idanun ta ko kiftawa basu yi ba ta ware su kyar a kan kyakyawar fuskar sa mai cike da abin kallo dan kuwa wannan kallo nasa da tayi babu abin da ya fado mata fiye da mijin dake cikin mafarkin ta..