KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

  Gani take kamar duk sakamakon damuwar da ta ɗorawa kan ta akan raahin haihuwar ne,ta kasa gane illar maganin da take sha ne ke haifar mata da ciwon cikin sai ta rinƙa ƙara yawan maganin madaɗin biyu a rana sai ta maida shi huɗu a rana ta sha biyu safe biyu yamma..

  Saheeb kuwa ya kasa samin natsuwar sa dan in ciwon cikin ya motsa mata sai ta yi kamar zata tafi tayi ta juyi haka zai ta kula da ita..

A lkcn da ya nemi Khalid a abin sai Khalid ya mai nuni da su tafi asibiti a duba mata mahaifar nata ƙememe Muhibba ta ƙi yarda dan ta san blackmailing Saheeb da tayi kuma take kanyi in ta tafi asibiti za a iya sanin gaskiya ita kuma batajin zata iya karawa da Mufida..

  Haka nan Saheeb ya bar ta dan ta ce ita gynaecologist ɗin ta zata tafi ta gani in ta shirya..
  Sosai take cikin matsala amma ta ƙi zuwa asibitin ga ciwon na daɗa gaba amma taurin zuciya irin na Muhibba bai bar ta ta tafi ganin likita ba ta yi ta managing kan ta..

Wani rana haka da dare misalin ƙarfe tara bayan Saheeb da Muhibba sun sami sa’insa da junan su sai ya fitar mata a ɗakin ya koma nasa baidai sami kwanciyar hnkl ba sai ya fita ya bar sashen ma gabaɗaya ya nufi sashen su Ammy..

  Ko da ya shiga duk sun kwanta sai ya nufi ɗakin fifi dan dama niyar sa washegari ya zo duba ta but yadda Muhibba ta ɗaga mai hnkl haka ya sa baya jin ya cigaba da zama a sashen dole ya zo ya ga fifi duk kuwa da ya san yaata laifi but he want to impress her today ta hanyar nuna mata sincere apology ɗin sa…

  Da fari da ya shiga ɗakin sai ya ga duhu ya mamaye ɗakin so yayi switching wutar ɗakin,ga mamakin sa sai ya hango ta jingine da gadon ta ta haɗe kai da gwiwar ta,hasken da ya mamaye ɗakin ne ya saka ta ɗago kan ta..
  Tana ganin sa sai ta zuba mai ido kamar bata taɓa ganin sa ba sai yau,shi kuma ya ƙarasa shigowa ciki a sannu,idanun ta na kan sa haka shima nasa idanun na kan ta..
  Da ya ƙarasa shigowa ya zo dab da ita sai ya zauna kusa da ita,sunkuyar da kan ta ƙasa tati ta mai shiru,bai san ta ina zai fara ba amma yana so yau ya kasance tare da ita ya faranta mata ya saka ta jin daɗi kamar yadda ya dace..

  Hannun sa ya saka ya riƙo nata,bata ce mai komai ba tana bin sa da kallo har ya kwantar da ita tana kallon sa ya dawo ta dama ya kwanta haɗe jawo marufin gadon ya lulluɓe su..
  Mamakin sa sosai ne ya kama ta ganin yadda yake mata abu kamar kurma,jan ta zuwa jikin sa da yayi ne ya saka ta lumshe ido dan dole ta kasa buɗewa..
  Kunnuwar ta ne suka jiyo mata sautin muryar sa yana bata haƙuri kamar kullum,ran ta a ɓace ta fara jan jikin ta amma ya matse ta dan ya fi ta ƙarfi ta ko ina..

  “Ki kula kar ki bige min baby”.dakatawa tayi daga fizge fizgen da take yi ta natsu tana numfarfashi kamar tayi gudun tsere..

  Hannun sa ya kai kan cikin ta da ya fara girma sosai,zagayawa ya shiga yi da hannun nasa bisa cikin ta ba tare da ya ce komai ba..
  Da ya gama yayi ƙasa da kan sa ya sumbaci cikin nata sannan yayo sama ya rungume ta tsam a jikin sa,ƙala bata ce mai ba sai da suka share wasu lokuta a haka sannan fifi ta fara yunƙurin raba jikin ta da nasa amma ta ji ya kuma riƙo ta ƙam..
  Bata ankara ba ta ji ya fara janta a sannu ba da zafi zafi..
Tun bata biye masa har ta sauko ta biye mai abu kamar wasa sai ga fifi manne da Saheeb ana zuba love abin gwanin burgewa..

A nan ɗakin nata ya kwana bayan ya gama cika mata brain da alƙawarurrukan daga yanzu bai kuma yin nesa da ita ya mata alƙawarin tare zasu raini unborn baby ɗin su..

Tare suka yi wanka da asuba suka yi sallah tare suka kuma komawa baccin safe again bayan yayi showering nata da salon soyayyar sa mai ɗauke hnklin ɗiya mace…


  A sashen Muhibba kuma tun safe da ta farka ta duba bata gan sa ba ta shirya hnkl tashe ta fito,kamar ta fara tsayawa a sashen Hamida sai kuma ta fasa ta wuce zuwa sashen su Ammy..
  Babu wani walwala sosai a tattare da ita so bata wani jima ba tare da su ta tmby ƴar aikin gidan ko Saheeb ya shigo amma ta ce mata bata sani ba.
  Hnkl ta na bata Saheeb na nan tare da fifi kamar ta je kamar kar ta je sai ta miƙe ta haura saman gabab ta na ɗan faɗi..

Bata san me zata gani ba in ta shiga ɗakin fifi but bata dai son ta ga abinda ran ta ke raya mata..

Da isar ta ɗakin ta ɗora hannu a handle ɗin ta murɗa ta tura a hnkl ta sa kai..

Wani faɗuwar gaba ne ya riske ta ba dan komai ba sai ganin Saheeb da tayi tare da fifi kwance cikin tsantsar jin daɗij yanayin su..

Juyawa tayi idanun ta rufe da kishin mijin ta da ɓacin rai ta bar sashen tana ta nanata dama yana son yarinyar nan amma kullum baya admitting ya saka ta ta rinƙa jin kamar daga ita sai ita a rayuwar sa dama ƙarya yake mata..

Bata tsaya ko ina ba sai a sashen Hamida da yanzu ta dawo daga rakiyar mijin ta zai tafi aiki..

Sallama tayi a bakin ƙofar parlorn,bata jira an bata izini ba ta saka kai ta shiga,daidai Hamida zata zauna kenan ta ga Muhibba kuma da ganin ta ka ga wacce ke cikin tashin hnkl..

Bata ba Hamida damar yin mgn ba ko uffan bata ce ba Muhibba ta riga ta da baki cikin fushi da ɗan zafin rai..

“Ke Hamida tare da ke muke komai Amma ashe wannan ƴar yarinyar mai ƙoƙarin amsa sunan matar Saheeb na can na kalaikaye min miji ni ina nan ina tinƙahon miji nawa ne ni kaɗai nagama da shi?,for goodness sake is that girl so dump and foolish just look at me na yi kama da wacce zan haɗa miji na da wannan ƴar yarinyar”?

Hamida na shiru tana jin zafin kalaman Muhibba ga ƴar uwar ta..

“Kina ji na kuwa Hamida?ki bani mafita ta yaya zan ɓullowa wannam yarinyar na ƙi jinin in gan ta kusa da miji na”!

Dakatar da ita Hamida tayi ta hanyar ce mata
“Me ya sa”?rai ɓace ta bata amsa da

“Because he is mine and all mine alone”!

Murmushi Hamida tayi ta koma ta zauna tayi crossing ƙafar ta ɗaya kan ɗaya tana karkaɗawa tana duban Muhibba dake tsaye tana bin Hamida da kallon mamaki..
“Meye haka ina nemar mafita ta yadda zamu kawar da lbrn wannan yarinyar a rayuwar miji na ke kuma kin zauna kamar ba kya ji na”!da ɗan ɗagon murya Hamida ta ce

“And why should i help you Muhibba?for crying out loud ke baki da brain ɗin tunanin kan ki ne sai na baki mafita?waini nace miki tsanarta nayi ne uhm?shawara fa nabaki..go ahead and use ur head mana..kema ki samowa kan ki mafita as far as am concern ke ɗin ai babba ce kin girme mu so use ur big head and find a proper solution for ur self

“Arazane Muhibba ta bi Hamida da kallon mamaki..

Karkaɗa ƙafa ta cigaba da yi tana duban Muhibba sai kawai Muhibba ta mata wani tsawa itama ta miƙe tsaye ta mayar mata da martanin tsawar nata.

“ai ban yi ƙarya ba ki je ki samowa kan ki mafita na gaji da duk wannan abin am out…kiyi waje

ɗora hannu a ƙwanƙwaso Muhibba tayi tana kallon Hamida da tsantsar mamakin ta..

Kalamai marasa daɗi ne ya fara fitowa daga bakin Muhibba zuwa ga Hamida,itama Hamida cikin rashin haƙuri ta hau maida mata martani har da gori da tunatar da ita ita ta kasa bada farinciki a rayuwar mijin nata sai hassada dan ta ga nata twin sister ɗin ta bashi farinciki..

A sannu duk suka gama tonewa kan su asirin shirin su da suka yi ta yi a ɓoye ba tare d wani ya sani ba gori akan gori,faɗa sosai suka yi mai muni,tas suka tonawa kan su asiri kamar ba a taɓa zaman mutunci ba..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button