KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS
Turo ƙofar parlorn aka yi da ƙarfi alamar duk wanda ya turo ƙofar ya ji every single part of their conversation,a tsorace Hamida ta juyo hakama Muhibba duban su suka kai ga wanda ya shigo dan ganin sa..
Zazzaro ido Hamida tayi sakamakon ganin wanda ya shigo ta juya ta kalli Muhibba da itama ita take kallo lokaci guda suka juya kallon ƙofar..
Mamuh35
Ƙarasa shigowa yayi take Hamida ta shiga taitayin ta ta ɗan koma da baya yayin da Muhibba ta ƙare masa kallo ta juya ta kalli Hamida ta ɗan ja ƙaramin tsaki ta sa kai ta fice ta bar sashen..
Gaban ta ya zo ya tsaya cak yana ƙare mata kallo daga sama har ƙasa,irin wannan disgusting looks da yake mata na ruɗa ta..
Da ƙarfi ya riƙo kafaɗar ta cikin tsantsar ɓacin rai da tir da halin matar nasa ya fara mgna cikin bacin rai, cikin ɗagon murya da hargowa..
“Ki Tabbatar min da gaskiyan wannan hirar naku da na gama ji yanzu da bakin ki”!!
a tsorace Hamida ta dundunce cikin tsoro da fargabar me zai biyo baya ta hau in’ina tana ƙoƙarin fizgewa khalid ya kuma matso ta dab da shi..
“Khalid you are hurting me let go off me”!.kamar zatayi kuka ta furta hakan
daka mata tsawa yayi yana ce mata
“Yes i wanna hurt u so that u will feel d pain u hv been making ur own blood twin sister experiencing,hamida ba zan ga laifin ki ba dan dama wanda bai so ka ba tun asali ba zai taɓa son ka ba har abada ko ya zo ya ce yana son ka toh da manufa ne,now i get it,you are a selfish person,kin cika son kan ki da yawa,just imagine,Hamida haka kike ashe?ki haɗa kai da wata wai Muhibba da duk kusancin ku bai kai girman kusancin ki da ƴar uwar ki ta jini ba,hnkl kwance ki yarda tana cin ma burin ta akan ƴar uwar ki and d most provoking part of all shine da sanayyar ki hakan ke ta faruwa”..?
Zafafan Hawayen sa daya ke dannewa su suka kwace mishi suna gangarowa a hankali muryn sa yayi wani irin sanyi yace
“Hamida Me ya sa kika canza halayyar ki kika zamo kamar wata muguwa marar imani?huh?sbd Allah Hamida duk waɗannan munanan abubuwan da kan ki da hannun ki kika yi su?in fact ke ce mai coming up da idea ɗin?.ƴar uwar ki ta jini kika haɗawa waɗannan abubuwan?common Hamida u weren’t lyk dis. meye ne ya sauya ki kika zamo haka?duk ƙoƙarin da nayi ta maki ashe abinda kika saka kanki a kai kenan?
Kuka ta fashe dashi batace dashi uffan ba
shiru yayi yana watsa mata kallon banza ita kuwa banda kukan babu abinda take yi..
Haɗa ta da wall ɗin parlorn yayi yana kallon ƙwayar idanun ta,tas tana hango tsantsar ɓacin ran da yake ciki..
“So u two have been blackmailing my brother huh?kai Hamida how many evil hv u done?ashe tuntuni kun daɗe da sanin juna ma sanin da yayi zurfi har ke kina iya bada shawarar ga abinda ya dace a yi?kun saka shi zama cikin zargin kan sa akan laifin da bai sani ba ku kuna nan kuna arranging plans ɗin ku shi yana can yana kwantar mata da hnkl yana nesanta kan sa da ƴar uwar ki matar sa kuma kina ankare?ke ce a gaba mai jagorantar komai ma”!!
A raunne ta dago Zatayi magana yace baison ji
Sosai Hamida ke kuka tana nadamar wannan rana da ya zo mata a haka
kwata kwata ba haka ta shirya faruwar Abun ba so tayi daga wannan argument ɗin da suka samu tsakanin ta da Muhibba shikenan ta fitar da ita a rayuwar ta ta koma ga ƴar uwar ta but unfortunately Khalid ya gama jin komai bata da yadda zata kare kan ta komai ya ƙwace mata…
Sakin ta Khalid yayi ya juya baya yana furzar da iskar takaico da ɓacin rai,yana mamakin yadda zuciyar Hamida ya ƙeƙashe ya bushe haka har akan kishin ƴar uwar ta take iya haɗa kai da Muhibba su cuci ƴar uwar nata…
Nade hannayen sa yayi a ƙirji ya juyo ya dube ta da kyau sannan ya ce mata cikin murya mai firgitarwa da tsoratarwa.
“Tun yaushe kika fara zaluntar Mufidan?saurin duban sa tayi gaban ta na faɗi cikin kuka sai ta girgiza mai kai tana faɗin
“Wlhy ban taɓa shirya zaluntar ta ba ruɗin zuciya ne ya shiga tsakani na da Mufida amma Ƙaunarmu na nan a zuciya ta”!!shutting nata yayi ta hanyar ce mata
“Ƙarya kike yi karki ce min akwai ƙauna a tsakanin ki da Mufida after all these conversation da na ji da kunne na,har kin ba Muhibba shawarar karɓar wannan maganin da take sha,well for ur information maganin nan na nan na haddasa mata illa,illah mai tsanani,ɓoye ɓoyen ku wata rana zai ƙare but kin san me?
“am leaving,am leaving u na har abada.. coz ba zan iya cigaba da zama da mace irin ki ba, duka soyayyar da na nuna maki,da irin zaryar kai komon da Mufida ta rinƙa yi maki duk dan ki yafe mata ku shirya amma tun asali da yake ba son ta kike ba sai kika rufe idanun ki kika rinƙa bin abinda zuciyar ki ke raya maki yake bijiro maki,so am getting out of ur life hamida ki je Muhibba ta zame maki abinda ni da ƴar uwar ki muka kasa zame maki”!!yana kaiwa nan ya ingiza ta ya wuce ya shiga tattara kayan sa..
Faɗi ƙasa tayi tana kuka mai haɗe da shesheƙa tana maganganu ita kaɗai tana nemar yafiyar Khalid bai kulata ba har ya gama yaja jakar sa ya fita..
Bata kuma tsorata ba sai da ta ga da gaske tafiyar zai yi dan ya fito da akwatin san rai ɓace ya xubasu s booth ya rufe..
Tana kuka ta taso ta zo zata riƙe shi,wani tsawar da ya mata sai da ta ja da baya jikin ta na ɓari tana kuka mai tsanani tana nemar yafiyar sa haka ya ya shige ya ja motr sa ya fita a gidan..
Kamar zata haukace haka ta rinƙa yi ita kaɗai tana aibata ranar da tunanin haɗa kai da Muhibba ya bijiro mata,tunda take a rayuwar ta bata taɓa ganin Khalid yayi fushi mai tsanani irin wannan ba sai yau,kenan ya tafi ya bar ta kenan?hukuncin da ya zaɓi yi mata kenan?..
Surutai dai babu wanda Hamida bata yi ba tun tana ganin abin kamar hasashe har dai ya tabbat Khalid ya tafi ya bar ta shikenan ita bata da wani gata,garin nemar gira ta rasa ido,ita ina zata kalla ta ji daɗi a ran ta…
Haka ta yini tun safen nan har dare bata sami kan ta ba abin kamar wacce ta rasa hankalin ta haka tayi ta yi,kiran tayi har ta gode
Allah bai ɗaga ba daga bisani ma kashe wayar yayi gabaɗaya,text msgs kuwa sun fi a ƙirga da ta aika mai da shi but babu reply,kwanar kuka da nadama tayi tana da ta sanin rayuwar ta…
A fannin Muhibba da ta bar sashen Hamida bayan kallon banzan da ta ma Khalid,sashen ta ta nufa ta shige ɗakin ta ta saka mai lock..
She is weak already bata da wata dabara da ta rage mata tunda dai har Khalid yaji abin da ya faru tsakanin ta da Hamida toh ta san Saheeb ya gama jin komai…
Kai kawo ta shiga yi a ɗakin tana saƙa da warwara,rikicewa ƙwaƙwalwar ta yayi ta kasa lissafin komai dan dama in dai irin wannan ne toh Hamida ce mai bata mafita toh yanzu sun ɓaci babu jituwa a tsakanin su..
Furzar da iska tayi tana cigaba da kai kawo at same tym da take takura brain ɗin ta ya bata mafita a same time ciwon cikin ta na addabar ta dama daurewa tayi ta tsaya ta yi wannan faɗar da Hamida amma tana jin ciwon sosai…
Zama tayi a kan sofa ɗin ɗakin nata tana ta nemawa kan ta mafita but sam bata samo komai ba haka ta ɗau wayar ta ta rinƙa kokarin kiran Saheeb sai tayi dialing sai ta kashe dan bata san me zata ce mai ba in ya ɗaga kiran.
Gabaɗaya Muhibba ta rasa natsuwar ta da tunanij ta a ranar ga Saheeb ɗin bai ko waiwayo ta ba bare ya san halin da take ciki