KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS
Daɗin daɗawa ma ga fifi ta dawo part ɗin dan ta ji hayaniyar mai aikin su Ammy na tmbyr ta ko ta tsaya ta taya ta girki amma ta ce a’a ta tafi kenan shi Saheeb ɗin ne ya ce mata ta dawo dan ya rinƙa ganin ta da kyau yana nuna mata so da kulawar sa ita kuma ko oho..
Har dare tana part ɗin ta bata fito ba haka Mufida bata haura ta duba ko lafiya bata gan ta ba toh dama babu ruwan ta da Muhibban,mijin ta ne a gaban ta kuma duk inda yayi nan itama zata yi bata jin tana da lkcn wata Muhibba bare ta sakawa ran ta damuwar ta,ta san days ɗin ta are numbered dan sarai doctor ɗin ta ya faɗa mata komai game da rayuwar ta da na babyn ta sai dai bata sanar da Saheeb ba dan bai san tana da wani doctorn ba all he knows shine Khalid ke kula da ita bayan hakan bai san komai ba…
Kusan kimanin sati biyu kenan rabon Khalid da Hamida sai dai ya zo ya gaida mahaifiyar sa da kakar sa,in yayan sa na kusa su gaisa in baya nan yayi tafiyar sa.
Duk wannan mu’amalar nasu da Saheeb ko da wasa bai bayyanawa ɗan uwan nasa abinda ya jiyo Hamida da Muhibba suka aikata ba haka bai sanar da mahaifiyar sa ba bare kakar sa Hajja..
Hakama Hamida na nan na ta targeting nasa in ya zo amma bata taɓa sanin lkcn da yake zuwa har ya tafi sai dai ta ji an ce ai Khalid ya zo har ya wuce..
Kwanar kuka take yi a ranar da ta ji hakan sai dai bata san wa zata tunkara da damuwar ta ba ƴar uwar ta da ta ha’inta zata tunkara ko wa,bata sani ba amma matuƙa abin na damin ta a ran ta…
Wata ran tana kan share hawayen ta bayan 111 missed calls da ta bar wa Khalid sai ta tashi wuf kamar an tsungule ta ta yafa ƙaramin mayafin ta ta nufi sashen Mufida dan ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba fifi na zuwar mata hira sai dai bata taɓa faɗa mata abinda ke damin ta ba hasalima in ta zauna sai ita ta tashi ta ce bata jin daɗi zata kwanta,tmbyr inda Khalid yake kuwa fifi ta mata shi sau nawa amma amsarta shine ya tafi aiki so daga haka fifi zata ja bakin ta tayi shiru..
Haka ko da Saheeb da Ammy suka so sanin me ya sa ya tafi aikin ba tare da matar sa ba sai ya nuna masu so yake y barta da fifi tunda sun fara shiri yanzu,so kowa ya yarda da dalilin sa ban da Muhibba da ta san kwanan zancen..
Waya take yi da daddyn su tana ta murmushi sai ta an turo mata ƙofa dan haka ta kai duban ta ga ƙofar sai ta ga Hamida duk hnkl tashe idanun ta cike taf da hawaye ta ƙarasa shigowa bedroom ɗin Mufidar abinda bata taɓa yi ba kenan tunda aka masu aure sai yau..
“Daddy i will call u back ina zuwa”fifi ta faɗa tana kashe wayar haɗe da dubar ƴar uwar nata..
Hnkl tashe ta tashi ta ƙarasa gare ta tana tmbyr ta lfy,kuka ne ya ci ƙarfin Hamida sai kawai ta ɓalle da kukan sosai,hnkl fifi ya tashi sosai sai ta riƙo ta suka zauna a gadon ta saka hannun ta cikin nata tana tmbyr ta me ya same ta..
Da kunya ciki a zuciyar ta ta zayyanewa Mufida dalilin tafiyar Khalid sakamakon abinda ya jiyo,da mamaki fifi ta tmby ta me ya jiyo nan matsanancin kunyar fifi ya mamaye Hamida amma haka ta daure din dai ta fayyace mata komai daga fari har ƙarshe…
Wani mamaki ne ya kama xuciyar Mufida sai da ta ɗau lkc tana ƙaryata kunnuwar ta amma Hamida tayi ta nanata mata ai hakan ne ita dai ta yi kuskure babba Mufida ta dube ta da idon rahama ta yafe mata ba zata ƙara ba…
Kallon ta kawai fifi tayi ta yi ta rasa me zata ce,ƙirjin ta ne ya mata wani irin nauyi sai tayi shiru har Hamida ta gama surutan ta tana kuka…
Rungumo ta fifi tayi tana fidda hawaye daga idanun ta tana jin zafi a ƙirjin ta sai dai ta kasa furta komai har sai bayan wasu lokuta sannan ta rarrashi Hamidan a nitse.
“Is ok Hamee na maki alƙawarin zan taimaka maki mijin ki ya dawo maki InshaAllah!
a firgice Hamida ta ɗago tana kallon fifi da mamaki
murmushin da ya fi kuka ciwo fifi ta mata tana gyaɗa mata kai ta kuma rungume ta batace komai ba..
Ba ƙaramin guilty conscious ne ya addabi Hamida ba tunanin ta in ta gama faɗawa fifi gaskiyar ƙulalliyar da suka mata from a-z fifin zata bada negative reaction sai ta ga akasin hakan..
A nan part ɗin fifi Hamida ta yini dan tayi yadda zata yi ta sa Hamidan ta sake jikin ta kafin daga bisani ta raka ta har sashen ta suka yi sai da safe ta dawo part ɗin ta…
Kuka ne mai ƙarfi ya kama Mufida tana yi tana danne ƙirjin ta dan nauyin da ya mata ba kaɗan bane,tana ta son ta karyta zancen cewa Hamida ce ta aikata mata hakan sai dai ya faru ko saura a gyara gaba..
Ciwon ta ne ya so tashi cikin dare dan Saheeb baya nan ya ɗan je wani tafiya haka tana jin nauyin faɗawa Ammy wannan abin so ta barwa kan ta,in da wanda zata faɗawa bai wuce saheeb ba toh baya nan dole ta jira har ya dawo sannan dan kar ta ɗaga mai hnkl,kuma daga baya tayi tunanin kawai ta fasa faɗa mai ɗin ita tayi yadda zata yi dan Khalid ya dawo ga matar sa…
Washegari fifi da kan ta ta kira Khalid bata bari ya riga ta da baki ba ta nemi alfarmar da take nema daga gare sa sai ya rasa abin faɗi kawai ya ce mata ya ji zai dawo nan da kwanaki uku,gudun kar ta takura mai da yawa sai ta mai godiya kawai suka yi sallama ta fita dan zuwa ta ma Hamida albishir..
Mamuh36
Kamar yadda Khalid ya faɗa haka ya cika,danna daidai 3rd day ɗin da suka yi waya da Mufida ya dawo gidan..
Ranar Hamida sai da tayi kukan murna ta rasa me zata mai dan ya ji daɗi sai dai bai bi ta kan ta ba ya bar ta kamar bai yi kewar ta ba..
Kasa aiwatar da komai Hamida tayi har dai ta kira Mufida a waya wacce daidai lkcn kuma tana waya da mijin ta,ganin kiran ƴar uwar ta ya sa ta katse nasa kiran ta ɗau na Hamida..
Da shesheƙa Hamida ta fara mata bayanin ƙyaliyar da Khalid ke mata,haƙuri kawai fifi ta iya bata ta ce ta ɗan bar sa zuwa washegari hala ya sauko..
A haka dai Khalid da Hamida suka kwana a part ɗin su,shi ya kwana a ɗakin sa ita kuma ta kwana a ɗakin ta abinda basu taɓa yi ba tun auren su..
Ita dai bata yi baccin kirki ba dan kewar mijin nata ne kawai ke mamayar ta but bata da yadda zata yi haka nan ta kwana cikin kewar sa idanun ta buɗe duk sun kumburo…
Da safe misalin ƙarfe shida ta farka ta haɗa ma Khalid breakfast duk da ciwon da kan ta ke yi haka ta daure ta girka mai wani da zai tafi da shi office ta je tayi wanka ta dawo ta shirya cikin shigar atamfa ja mai ratsin fari fari ya mata kyau ta ɗan yi makeup kaɗan tayi ɗaurin ta ta fito ta zauna a dinning table ɗin tana jiran sa…
Fitowar sa kenan cikin shigar tafiyar aiki yana gyara necktie ɗin sa sai ya hango ta kan ta haɗe da table ta tallafe kan da hannayen ta biyu tana bacci..
Wani tausayin ta ne ya ratsa sa sai ya ƙaraso gare ta,a hnkl ya saka hannun sa yana shafa bayan ta but kamar yana petting nata ne..
Cikin baccin ta ta ji abinda yake mata sai ta ɗan ɗago da baccu bacci a idon ta,ganin sa sai ta wartsake gabaɗaya ta tashi..
Saurin maida ta yayi ta zauna shima ya jawo kujerar kusa da ita ya zauna suna fuskantar juna,for a while bai ce komai ba sai daga bisani ya fara mgn..
“Na san na maki hukunci mai tsauri ta hanyar ƙaurace maki but ki sani,hakan ba yana nufin ban yi kewar ki bane ko ban damu da rashin ki a kusa da ni bane,i did what i did to wake u up from ur challenged future,ba zaki cigaba da rayuwa a duniyar nan da ƙiyayyar ƴar uwar ki ba,but am happy ganin abubuwa sun daidaita a tsakanin ku kuma kuna getting along da juna,i pray that it will continue all through”!!gyaɗa mai kai tayi da sauri tana jin sanyi a ran ta..