KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS
Hawayen dake tseren zubo mata ne suka sauko sai ta share da yatsar hannun ta tana kallon sa..
Murmushi ya mata sannan ya nemi da ta mai alƙawarin ba zata kuma ƙulla wata alaƙa da Muhibba ba..
Alƙawarin ta mai tana tabbatar mai da cewar in har ya ga tana kusantar hakan toh ya jawo hnkln ta but bata fatar kusantar hakan kuma..
Daɗi ya ji da ya iya tsawatarwa matar nasa ta dawo kan hanya,maida duban sa yayi ga abincin ya umarce ta da tayi serving nasa..
Da sauri tayi hakan,fried chips ne da scrambled egg sai quacker oath da ta haɗa masu..
Ya ji daɗin breakfast ɗin dan haka ya cinye duka yana santi haɗe da yabawa hannun nata da ya girka abincin,daɗi sosai Hamida ta ji har ta rasa ina zata saka kan ta…
Tare suka fito bayan yayi feeding nata itama ta ƙoshi sai ta ɗauko mai food flask ɗin sa na abincin da ta mai..
Nan ma wani yabon ta sha shine ta rako sa har mota,suka yi warmly goodbye sannan ya tafi ita kuma ta nufi sashen fifi…
Da sallamar ta a baki ta shiga parlorn sai tayi tozali da Muhibba dake fitowa daga kitchen cikin sauri cikin shigar blazers da wando ta ɗora wani summer cardigan,kan nan babu mayafi sai wani turban,handbag ne a hannun ta da car key,ƙafar ta ya sha heels ne baƙaƙe..
Kallon wofi Hamida ta mata itama ta maida mata da matarni har da ɗorawa da
“Ina cikin hanzari ne amma ki bari in dawo zan yi fixing naki inda kika dace”!!ta faɗa tana tafiya..
Cikin sauri Hamida ta maida mata amsar da ya saka ta juyawa dan kallon Hamidar da kyau but sai ta ga har ta wuce ta..
Abinda ta ce mata kuwa ba wani abu mai tsayi bane sama da
“Kullum cikin hanzari kike shi ya sa kika kasa ba mijin ki farinciki har ya samo wacce ke bashi,that’s why u always behind,hanzari!!!hanzari!!hanzari,too bad”..
Ba ƙaramin ƙonawa Muhibba rai waɗannan kalaman Hamida suka yi ba sai dai bata ce komai ba illa ƙwafa da ta yi ta juya ta fice…
Kai tsaye Hamida ta shige bedroom ɗin fifi sai ta gan ta zaune da towel babu kaya a jikin ta tana ta positioning wayar ta kamar dai video call zata yi..
Murmushi tayi ta ƙaraso ciki,sai a sannan fifi ta gan ta sai ta kife wayar a kan gadon ta fara yunƙurin tashi dan tarbo Hamida but Hamida ta hana ta ta hanyar ƙarasowa ɗakin da sauri tana riƙo hannun ta game da furta..
“Don’t take d trouble sweet”faɗaɗa murmushi fifi tayi sai ta zauna suna fuskantar juna..
Gaisawa suka yi irin ta ƴan uwa a nan Hamida ke shaida mata yadda suka yi da Khalid sai fifi tayi murmushi kawai tana sha’awar rayuwar su dan suna burge ta,kullum suna tare da juna unlike ita da suke raba mijin sannan bai cika zama ba,a ƙalla cikin sati biyu yayi tafiya ya kai uku,bai da wani lkcn isasshe da yake spending ɗin sa da ita..
Hirar su suka yi har Hamida ta taya fifi gyare gyaren inda bata gyara ba kafin ta koma apartment ɗin ta tayi girki mai ƙara lfy a jiki da kyaun kallo ta cika sa cikin food warmer tayi blending fruits ta tace ya zamo kamar fruit juice sannan ta haɗa su a wani basket ta dawo sashen fifi da su…
Abin ya ma fifi daɗi dan dama ƙiwar girkin take yi dan a ƴan kwanakin nan aiki na mata wuyar yi kuma ta ƙi yarda Ammy ta turo mata ɗaya daga cikin ma’aikatan ta haka ta ƙi yarda a rinƙa kawo mata abinci daga sashen…
Har dare suna nan tare suna ta hirar su,wanda cikin hirar ne Hamida ta kawo wata shawara da tayi tasiri a zuciyar fifi har tayi tunanin ɗabbaƙa shawarar immediately sai dai ta bari har mijin ta ya dawo sannan ayi mai yiwuwa..
Shawarar akan daddyn su ne da rayuwar zaman kaɗaicin da yake yi na rashin mace,sun gama tsara komai yadda zai kasance,lkc kawai suke jira su fara aiwatar da plan ɗin nasu…
Wayar Hamida ne yayi ƙara kamar ba zata ɗaga ba sai ta ɗaga ta kai idanun ta kan wayar..
Sunan dake haskowa ne a screen ɗin wayar ya saka ta buɗe baƙi cikin mamaki tayi saurin ɗaga wayar tana faɗin
“Am on my way luv ina wurin Mufida ne”!!tana gama faɗin hakan fifi ta saka mata dariya ganin duk ta ruɗe..
Bata bi ta kan ta ba ta tashi abin ta tana mata sai da safe,sauri sauri ta dawo apartment ɗin ta inda ta gan sa yana cire necktie ɗin sa a gajiye..
Saurin ƙarasowa gare sa tayi tana bashi haƙuri haɗe da taimaka mai ya cire necktie ɗin ta kwashe duk kayan da ya cire da hannun ta ɗaya,ɗayan kuma tayi wrapping round his waist tana mai yi mai sannu.
A haka suka ƙarasa sama inda bedroom ɗin su yake ta taya sa yayi wanka itama ya saka ta yi na dole,tare suka ƙarasa wankan bayan an gama romancing kamar ba za a bari ba sannan suka fito…
Abinci ma yanzu tare suka ci suna feeding junan su da love and care,a wurin kwanciya kuwa,yau sai da Hamida ta tabbatar mijin nata yayi kewar ta itama haka,dan basu wani runtsa da wuri ba sai cikin dare sannan baccin ya ɗauke su…
Yadda Allah ya so haka yake kasancewa,yau da gobe sai mai duka,a kwana a tashi ga mai tsawon rai cikin Mufida ya shiga wata takwas cif cif sakamakon scanning ɗin da tayi na ƙarshe ya tabbatar da hakan…
A lot has happened kamar yadda Hamida ta tsayawa Muhibba a ido kamar matsala ta ƙi yarda a cigaba da cutar da ƴar uwar ta,dan har threatening Muhibba Hamida tayi akan in ta ja abin da nisa toh kaf zata zayyanewa Marshall gaskiyar zance dan Khalid bai faɗawa kowa abinda ya ji suna discussing akai ba ranar…
Sosai tsoron Hamida ya ɗarsu a zuciyar Muhibba dan ta san da zarar bakin ta ya buɗe shikenan maybe ta rasa Saheeb ɗin na har abada kenan because in har yayi realizing cewa she has been blackmailing him for long toh ba ƙaramin zafi zai ɗauka da ita ba sai dai ta kasance cikin matsalar ita ɗaya
Sannan a fanni ɗaya tana fama da health condition ɗin ta,dan duk da tayi stopping maganin da take sha completely,babu abinda ya sauya game da lfyr ta,yanzu tana normal anjima zata rikiɗe kamar ba zata yi rai ba…
In ta zauna takan ji mamakin yadda ita Muhibba Hamida ke wa gashin ƙuma da mummuƙe,tana ganin Hamida is too small for her to handle amma ashe mightiness da Hamida ke da shi ya sha gaban tunanin ta…
Dai dai da pretence ɗaya in Muhibba tayi Hamida na wurin toh sai ta razana ta da kalamai masu tsoratarwa dan Hamida gani take yadda fifi ta dawo mata da annashuwar ta rayuwar ta wic is her husband,toh duk wani abinda zata mata a yanzu bai biya fifin ba shi ya sa take dagewa da strength ɗin ra take sokawa Muhibba mgn cikin mgn dan ba zata yarda ƴar uwar ta ta cigaba da fuskantar cin zarafin kishiya ba alhalin ta san komai na kishiyar…
Ga Muhibba kuwa babbar regret ɗin ta a rayuwa shine yarda da tayi da Hamida har Hamida ta san sirrin ta yanzu gashi tana mata barazana,abin kan dame ta ba kaɗan ba…
Thursday morning
Duk suna zaune ana breakfast a part ɗin su Ammy as family,kowa cin abincin sa yake yi ba tare da ya tanka ba,sai da aka yi nisa sai Muhibba ta fara jin wani iri a jikin ta,sincerely tana jin pains kamar kullum but fear ɗin ta shine kar ta buɗe baki ta furta Hamida ta taso ta gaba akan she is lying,dan yau ɗin girkin fifi ne wacce ita duk wannan bidirin da ke faruwa tsakanin Hamida da Muhibba bata da masaniya all she is after shine rainon cikin ta da lfyr jikin ta kafin ranar haihuwar ta dan ta sani,Dr ya sanar da ita bai ɓoye mata ba akan zai yi wuya ta rayu in har tayi experiencing labour pains,but ya bata option akan ana iya yi mata surgery a ciro babyn in kamar saura satittuka kafin EDD ɗin ta but sai ta ƙi yarda ta ce tana so ta ji zafin da mahaifiyar ta ta ji a yayin da ta haife ta kafin ta bar duniya,sbd believe ɗin ta shine duk mace da bata san zafin haihuwa ba toh ba zata mutunta kyauta da baiwar da Allah ya mata ba na bata kyautar haihuwar,so she choose to undergo the labour pains…