KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Duk motsin Muhibba a kan idon Hamida har dai Muhibban ta gaji da mutsu mutsu ta tashi ta bar wurin,murmushi Hamida tayi ta cigaba da cin abincin ta yayin da ake tmbyr ko lfy ta tafi,Ammy ce ta tashi ta bi bayan ta dan duba ko lfy su kuma sauran suka cigaba da cin abincin su except Saheeb da ya bar abincin ya bi Ammy dan duba Muhibba bcoz yana da tafiya yau mai muhimmanci..

Kasa natsuwa fifi tayi sai ta tashi da ƙyar ta bi sa,a hanya suka haɗe sai ya ruƙo ta a jikin sa suna takawa a sannu har suka ƙaraso ciki…
Ganin Ammy a parlor tana ta kiran sunan Muhibba ya saka Saheeb tmbyr me ya faru nan Ammy ke shaida mai wai Muhibban ce ta ce ta tafi bata son ganin ta…

Abin ya ɓatawa Saheeb rai mahaifiyar sa ce matar sa bata son gani,so annoying sai ya ja ƙaramin tsaki,ya ce da Ammyn ta tafi bayan bata haƙurin da yayi,shi da fifi suka shige ɗakin fifin inda ya ɗau bag ɗin sa da ba zata iya ɗaukar mai ba,suka fito da ƙyar ta raka sa ya shiga mota,ya ɗan leƙo da kan sa ya manna mata kiss a goshi a sannan yayi waving nata ya tafi itama tana waving nasa kafin ta koma ciki cikin tafiyar ɗai ɗai tana mai jin kewar sa tun yanzu..

Mamuh37

Rayuwa ta sauya sosai a cikin gidan dan komai na tafiya normal fiye da tunanin mai tunani,rayuwar farin ciki ne kawai ke wakana a cikin gidan..

Soyayya kam tsakanin fifi da Marshall sai abinda yayi gaba,har ga Allah basu taɓa tsammanin shaƙuwar su tayi ƙarfi haka ba da komai ya faru da ɗaya sai ɗaya ya ji alama a jikin sa..
Wasa wasa ƙauna mai ƙarfi ta shige su sosai,duk da fifi ta fi dangana kusancin nasu a matsayin shaƙuwar rabuwa dan ta san days ɗin ta are numbered already..

Yayin da shi Saheeb yanzu yake kuma jin soyayyar ta a ran sa sai dai bai da wani tym na nuna mata ɗumbin soyayyar sa gare ta sakamakon yanayin aikin sa da bai ba shi isasshen lkcn spending tym ɗin sa da ita ba..
Ita kuma gani take kamar rashin amincewa da ita da bai yi bane a zuciyar sa har yanzu ya sa baya wani nuna mata soyayya ƙarara yadda ta daɗe tana dreaming…

A rayuwar Muhibba kuma lamuran ta ta fawwalawa mai duka bcos komai ya tsaya mata cak,bata isa ta bugi ƙirji ta ce zata yi wani abu ba sai Hamida ta ɗora alamar tmby a behaviour ɗin ta..
Sannan Saheeb,ba wani daɗin sa take ji ba dan yadda take stressing nasa in suna tare ko kuma suna waya,abin dai sai a hnkl..

Hamida kuma da Khalid zaman su abij sha’awa dan tun wannan matsalar da suka samu bata kuma yarda wata kafa ta shiga tsakanin su ba,kullum tana kafa kafa da gudun zuciyar sa musamman in mgn ta kama irin ta argument ɗin nan,toh bata wani ja sai ta karɓi laifin dan dai kar su sami saɓani..

Khalid bai da wani complain sosai yanzu a rayuwa dan matar sa na masa duk wasu abin da ya kamata,haka akwai fahimtar juna sosai tsakanin sa da fifi haka nan ma tsakanin matar sa Hamida da ƴar uwar ta fifi..
Duk da tight schedule na Saheeb,hakan bai hana sa yin alherin da ya saba ba ga mabuƙata in buƙatar hakan ta taso ba,kuma yana ƙoƙarin sauke haƙƙoƙin sa as a husband of two wives…

Ammy da Hajja ba abinda ya fi masu wannan daɗi ganin kawunan yaran a haɗe,kuskuren da suka yi a baya ba su fatar kuma tafka wannan kuskuren ever again a rayuwar su,dan duk inda mutum ya kai ga hassadar sa toh in ya ga bond dake tsakanin family members ɗin nan toh dole ya kawar da kan sa dan relationship ne mai ƙarfi..

Cikin fifi na shiga watar haihuwar sa wato wata na tara,Ammy ta fara bata special care kusan yini take yi a sashen fifi,wacce tayi nauyi zama da ƙyar tashi da ƙyar,bata fuskanci matsalolin early pregnancy ba but yanzu da ta shiga last trimester ɗin ta sai ta ga kamar yanzu take fuskantar matsalolin early pregnancy ɗin..
Kama daga ruwan wanka,abinci,kula da ita,komai Ammy ke mata shi bcos Hamida have to take care of her husband as well,in aka bar ta da ɗawainiyar fifi da na mijin ta abin zai mata yawa,dalilin da ya sa Ammy ke kai kawo a sashen fifi kenan,moreover Saheeb is always busy a ƴan kwanakin sai da ƙyar ma take iya ganin sa kuma baya kwana a tare da ita,ko girkin ta ne ko ba nata ba dan Muhibba na fuskantar matsanancin ciwo mai barazanarwa ga rayuwar ta…

Ita dai fifi ta san musabbabin matsalar Muhibba but da yake ba saka kan ta take a lamuran ta ba,sai ta ƙyale ta maida hnkl ta ga nata health ɗin dan tayi alƙawarin kula da babyn ta har ranar da zata haifin babyn kafin ta bar duniya…
Fargaba sosai ke sabunta a zuciyar fifi a duk ranar da ta farka a sabon rana ta tuna kwanakin haihuwar ta matsowa yake which is equivalent to ranakun mutuwar ta dake gab..

Ba kasafai Saheeb ke bibiyar scanning ɗin ta ba wanda hakan ya bata damar ganawa da likitan ta secretly bcos shi Saheeb ya san ya damƙawa Khalid ne kula da lfyr ta wanda daga shi har Khalid ɗin babu wanda ke da masaniya akan likitan da take gani a ɓoy,duk kuwa da Khalid yana iya ƙoƙarin sa na ganin ya bata extra care but bata yarda ko secretly ba tare da sanin Hamida ko mijin ta ta sanar da shi conditions da doctorn nata ya bata ba game da yiwuwar haihuwar ta…

Lyk always yau ma tayi shirin ta cikin maternity gown ɗin ta ta saka ƙaramin hijabi ta tako da ƙyar ta fito zuwa farfajiyar gidan tana duba motar da driver ke jiran ta dan zata tafi ganin likitan ta sbd Saheeb baya nan kuma a nan gidan ta sallame su ne akan wurin Khalid zata tafi dan a mata dubiya ta musamman dan ta ƙi yarda a kawo mata scanning machine ɗin gidan dan in hakan ya faru ta san zai yi wuya ta haɗu da likitan ta da suka haɗu a yawon binciken ta ta waya har dai abin ya kai su ga haɗuwa concurrently…

Motar ta nufa ta shiga tana ajiyar zuciya kamar tayi gudun tsere dan cikin ya mata nauyi ga matsalar cardiac disorder dake damin ta wato health issue ɗin ta..
Jan motar yayi suka fita,sai dai yau bata bari sun fara zuwa wurin Khalid ba ta ce mai ya kai ta ɗaya wurin da yake kai ta in sun baro wurin Khalid..

Juya kan motar yayi suka nufi asibitin likitan ta inda ya duba ta ya kuma bata shawarwari da gargaɗin kar ta rinƙa ɗaga hnkl ta dan the more tana ɗaga hnkl ta the more damuwar ta zai yi muni,haka dai ta karɓi drugs ɗin ta ta koma mota suka tafi asibitin du Khalid inda nan ma ya bata kula ta musamman kafin su dawo gida…


Tunda fifi ta shiga satin haihuwar ta fargabar ta ke gaba gaba,ba laifi tana samin kula daga wurin Hamida da mijin ta Saheeb sai dai kular ragagge ne dan ba wani enough tym gare sa ba,a wannan yanayi ta fi buƙatar sa sai dai ya mata nisa dole ta haƙura wasu lokutan ya rinƙa attending travelling ɗin sa dan suna da muhimmanci duba da matsayin sa…

Suna zaune a parlor suna hira,Hamida,Ammy da fifi wacce jefi jefi take saka masu baki dan bacci baccin dake ɗibar ta..
La’akari da baccin da ta fara yi ne ya sa Ammy yi ma Hamida alama da su ƙyale ta ta huta,daga nan suka fita suka bar mata parlorn inda ta cigaba da baccin nata bisa wani ƙaramin mattress da ta maida sa abin kwanciya in ba ɗakin ta take ba…

Cikin baccin nata ta ji muryar Muhibba na maganganu wanda bata gane ba sai ta daure ta buɗe idanun ta,nan ta ga tana ta kai tana komowa ita ɗaya,waya sagale a kunnen ta tana mgn da alamar damuwa a muryar ta…
Bin ta da kallo fifi tayi kawai ta maida idon ta ta rufe dan in da sabo ta saba da halin i don’t care da Muhibba ke nuna mata ita da unborn baby ɗin ta,duk da tana ganin kamar Muhibban ta san very soon zata mutu ta bar mata mijin nata su cigaba da rayuwar su kamar yadda kullum take nanatawa kan ta…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button