KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS
A nan ɗakin fifi kuwa zafin da take ji bata taɓa jin sa ba tun da ta shigo duniyar nan sbd zafin is irresistible..
Hannun ta ta kai ga side drawer ɗin ta ta laluɓo wayar ta,ga ba haske ga halin da take ciki…
Bata ma san numbern wa ta kira ba ita dai tayi dialing number,wayar na ta ringing sai daga baya aka ɗaga..
Tana jin an ɗaga sai ta fara mgn a wahalce da rashin sabo da yanayin dan har ta fara kuka,tunanin ta mutuwar ce zata yi
“Hamee…ham…Hamee ki zo. Pls ki zo..am gonna die..pls come”ta ƙarasa mgnr tana jan kalmar come ɗin haɗe da tsala wani ihun…
Wayar ta wurgar ta faɗo ƙasa tana ta juye juye tana kuka tana nemar agaji da tallafin mutani…
Kusan 5 minutes bayan ta yi kiran tana durƙushe sai ta ji hayaniya daga haka ta ga an buɗe ƙofar an kunna wuta..
Already ta fara fita hayyacin ta dan haka bata san wa da wa suka shigo ba sai dai ta ji ana kinkimar ta ta mutani biyu a hanzarce…
Muhibba dake sume a ƙasa bakin ƙofar ɗakin fifi Khalid ya kira mai gadin su da ya je ya buɗe mai gate haka ya kai ta motar sa bayan motar su fifi ya tafi wanda Hamida ce ke jan motar dan ba zasu iya jiran driver ya zo ba..
Wsni irin speedy driving Hamida ke yi a kan titin cikin wannan tsakiyar daren tana yi tana kuka tana juyowa tana kallon fifi dake ta juye juye..
Ammy da Hajja dake riƙe da ita kuwa cikin su babu wanda gwiwar sa bai sage da al’amarin ba sai tofa mat addu’a suke ta yi…
Haka Khalid ma yayi ta banka gudu a kan titi yana bayan su Hamida,dai dai inda hanya ta raba nan suka rabu,motar su Hamida yayi dama nasa kuma yayi hagu..
Suka cigaba da gudu har dai motar su Hamida ya iso wani babbar asibiti inda nan Khalid ke aiki wato National hospital dake garin abuja…
Da sauri Hamida ta fito a birkice ta shiga ta kirawo su su zo emergency ne,sannan suka zo da gadon ɗaukar patient aka fito da fifi daga motat aka ɗora saman gadon aka yi wheeling nata zuwa ciki..
Shigar da ita E&O unit aka yi aka dakatar da su Ammy dake yunƙurin shiga ciki…
Card aka buɗe mata sabo fil sannan aka tmby Hamida wasu informations ɗin fifi while ana ciki ana ƙoƙarin stabilizing fifi…
Duk a rikice Hamida take sai kai kawo take ta yi a nan ta nemi da a ara mata waya zata kira mijin ta a nan yake aiki ta faɗa masu sunan sa sannan suka bata waya…
Kiran layin Khalid tayi wanda shima yana can wani asibitin an shigar da Muhibba ɗakin emergency tana numfashi sama sama da ƙyar…
Haɗa sa da likitan da aka kira tayi inda ya mai bayanin komai dangane da fifi sannan suka ajiye wayar…
Duk inda natsuwa take toh ta ƙauracewa wannan ahali a wannan dare..
It’s already 4:50am kusan 5am na asuba but babu wani improvement a condition ɗin fifi abinda ya tsorata su kenan dan sau biyu ana so a mata shirin shiga theater dan ceto rayuwar babyn but ta tmby su har wani lkc bavyn zai rayu suka faɗa mata sannan ta tmby har wani lkc labour ɗin zai kai ta suka faɗa mata sai ta ce toh su bar ta dan tana so ta haihu da kan ta…
Duk yadda suka nuna mata haɗarin hakan sai ta nuna masu ta fi su sani dan ita ke da ciwon a jikin ta kuma ko a yi aiki ko ta haihu da kan ta ta san mutuwa zata yi dan haka ta ce su kirawo mata ƴar uwar ta…
Duk wannan mgnr ya gudana ne bayan ciwon ya ɗan lafa mata but sai basu kira Hamida ba dan suna ganin hnkl ta zai tashi in ta ga condition ɗin ta…
Ai kuwa ciwon na dawo mata ta fara kiran sunan Hamida,sai nanata sunan take yi har dai suka fito suka yi requesting Hamida ta shigo…
Da gudu ta shigo ɗakin ta ƙarasa ta rungume fifi dake kwance akan couch ɗin haihuwa ta fashe da kuka tana faɗin
“Mufida pls fight it…ki yi yaƙi ki tashi kar ki bar mu,..ki tuna fah yanzu Ƙaunarmu ke ƙaruwa,yanzu ne Ƙaunarmu ya kamata ya taimaka mana ya kawo mu kusa da juna ba wai mu rabe ba,Mufida ki tuna fah in baki yi fighting ma rayuwar ki ba this baby will be motherless ya kike so babyn nan ta ji ko ya ji?kina son babyn ya taso ko ta taso cikin rashin mahaifiya ne?ki duba ɗumbin mutanin dake son ki pls Mufida ki tashi kar ki bar mu”!!kuka sosai Hamida ke yi wanda fifi ke taya ta dan ta san ba rai zata yi ba tana ji a jikin ta…
Riƙo hannun Hamida tayi cikim azaban raɗɗin da take ji ta fara mgn
“Ko na mutu Hamee..na baki kyautar abinda zan haifa..ki ɗauka,ki kula da shi..ki kula da shi yadda in ina raye zaki kula da ni…ki bashi duk soyayya da ƙaunar da ba zan ba shi ba…pls promise me…promise me that u will fulfil my request”!!da sauri ta gyaɗa mata kai sai tayi murmushin da yafi kuka ciwo sannan ta ce da Hamida
“Kuma kar ki manta da alƙawarin mu na daddyn mu kin ji?kar ki manta ko bayan na mutu ki tsaya ki cika mana alƙawarin mu ok”?kuka kawai Hamida ta fashe da shi tana daɗa rungume Fifi..
Sai da kukan yayi tsanani sannan aka zo aka fitar da Hamida tana fizgewa tana faɗin a bar ta ta gana da ƴar uwar ta but ina,haka aka fitar da ita tana kuka..
Bayan misalin awa biyu,Khalid ya dawo nan asibitin da fifi take ya sanar da su ya kira Saheeb ya faɗa mai an yi admitting Muhibba a asibiti kuma dama yanzu ya dawo so zai tafi can wurin Muhibba..
Ammy ce tayi saurin tmbyr sa ko ya faɗa mai har fifi sai ya ce a’a sai ta ce mai a bar shi kar a faɗa mai tunda su suna nan zasu iya tsaya ma fifi shi kuma ya tsaya da Muhibba kar su yi son kai…
After lyk 5 hours da zuwan su fifi asibiti an ɗan tsumayi haihuwan but babu wani cigaba sai kawai Khalid yayi signing ya ce su shirya ta a shiga da ita theater a mata aiki kawai dan situation ɗin fifi na deteriorating ga matsalar cardiac disorder ɗin ta ga na babyn dake jikin ta dake shiga distres..
Wata sabuwa ce ta taso dan ana ta ceton ran ta su Ammy na can na kuka a waje da Hajja,ga Khalid dake cikin firgici but haka fifi ta ƙi yarda a shigar da ita ɗakin theater ta ce sai mijin ta ya zo sun gana sannan ta yarda a shigar da ita..
Duk yadda suka yi haka ta ƙi yarda dole aka fara nemar layin Saheeb wanda sai ringing yake ta yi ba a ɗaga ba..
Hankula ne ya kuma tashi dan fifi bata yarda a shigar da ita ba ana ta addu’a a waje ita kuma sai nanata sunan “Gentle” take ta yi wato Saheeb sai daga baya ma ma’aiakatn suka gane waye gentle ɗin nan aka zafafa kiran Saheeb but bai ɗaga ba,ga fifi na jin jiki ga Hamida na kuka a jikin Khalid…
Mamuh
[8/24, 8:12 AM] +234 808 540 5215: 39
On the other side kuma,bayan Khalid ya kira Saheeb ya sanar da shi abinda ake ciki sai ya tura mai adireshin asibitin da take..
Already dama suna gab da landing dama tafiya yayi kusan 6 days ago toh a yau zasu dawo shi ya sa yana dawowa ya nufi asibitin ba tare da ya sauya kayan jikin sa ba…
A lkcn da ya ƙaraso asibitin har Khalid ya tafi,so he appears so shattered kamar marar lfy,haka ya nemi ɗakin da take aka nuna mai sannan ya tafi hnkl tashe..
Yana shiga ya hango ta kwance kamar marar rai,nan hnkl sa ya daɗa tashi ya kasa natsuwa sai da ya ƙarasa gare ta ya durƙusa ƙasa..
Fuskar ta dake lulluɓe kusan duka cikin abin bada numfashi(oxygen)ya kalla ya kawo hannun sa ya fara shafa fuskar nata har ta ɗan motsa ta buɗe idanun nata da ƙyar cikin wahala..
Ganin shine sai ta ƙara buɗe idanun ta da kyau dan ta gan shi shima ya gan ta,hannun ta na rawa ta ɗora saman nasa..
Da sauri ya maida idanun sa kan hannun nata ya kalla sannan ya kalli fuskar ta da ya sauya yayi fari kamar wacce bata da isasshiyar jini a jiki..