KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Wani tausayin ta ne ya kama shi mai tsanani sai ya ɗan kawar da fuskar sa dan zuciyar sa ya karye for the very first tym Saheeb ya tsinci kan sa da zubda hawaye akan rashin ƙwarin gwiwar ciwon matar sa…
Murya a disashe can ciki yana rawa ta fara mgn tana jan numfashi da ƙyar tana ajiyar zuciya..
“Miji na…ka zo ashe…ban san..ban..ban san zaka zo nan kusa ba..na daɗe ina ta jiran ka ina ta ce masu su kira min kai amma…babu wanda ya gwada kiran ka…but a yanzu da na gan ka na ji daɗi”!da ƙyar ta kai ayar zancen sannan ta ja numfashi da ƙarfi kafin daga bisani ta dakata…
Kallon ta yake yi cikin halin tsantsar tausayin ta ya matso kusa da ita suna kallon juna..
Shafa fuskar ta yayi yana manna mata kisses a kumatun ta hawaye na zubo mai ya kasa mgn sai hawaye dake ta fito mai…
Hannu na rawa ta kawo ta shafa fuskar sa tana goge mai hawayen da ke fito mai tana girgiza mai kai alamar ya daina kuka sai dai shima girgiza mata kan yake yi akan ba zai daina kukan ba..
“Miji na ka yi shiru ka saurare ni..tun ɗazu nake jiran ka ka zo,i hv been fighting with this feelings dan ka zo mu gana,ganawa na ƙarshe”!!saurin rufe mata baki yayi da hannun sa yana girgiza mata kai but ta ɗan fizge ta cigaba da mgnr ta..
“Saheeb am dying…i am dying…it is certain..su kan su likitocin sun gani sun faɗa min..but ina ta daurewa dan ka zo in gan ka ganin ƙarshe kafin in mutu…na riga na gama ganin all signs of death Saheeb kuma na san at any moment…zan tafi in bar ka ba dan ina so ba sai dan ya zama dole…Saheeb bana son ka dakatar da ni daga mgnr da zan yi,i know it will hurt u but ka yafe min dan in sami rahamar ubangiji”..
Ɗan numfasa tayi kuma tana jan iska da ƙyar kamar zata tafi sai tayi yunƙuri ta cigaba da mgnr dan nauyin da take ji a ƙirjin ta ya wuce misali..
“Miji na…na zauna da kai sama da shekaru goma,baka taɓa min abinda zan ce ka zalunce ni ba..baka taɓa min abinda bana so ba,ka yi ƙoƙarin ka wurin ganin ka sauke haƙƙin ka a matsayin ka na miji na,and am proud of u for that..komai ka min a rayuwa sai dai ka san me”??ta tmby tana ɗage giran ta biyu sai ya girgiza mata kai yana kuma damƙe hannun ta cikin nasa yana zubda hawaye..
“Nayi blackmailing naka for long,..duk wasu abubuwan da na faɗa maka akan rashin lfy ta were all lies,i was sick but not to that extent,a lkcn da na tafi ganin likita..ya faɗa min cewa uterus ɗi na was weak but ba har haka ba kamar yadda na faɗa maka ba…i did what i did kawai dan in sami attention ɗin ka ne,ni na saka likita ya rubuta min abinda ya rubuta a file ɗi na sannan na ce ya bani file ɗin in kawo maka ka gani…the result was perfect na sami attention ɗin ka sai dai da yake Mufida bata da haƙƙi na..maganin da na rinƙa sha a matsayin antidepressant ashe yana min illa a jiki ban sani ba…ban daina shan maganim ba duk dan in sami attention ɗin ka,miji na…ka yafe min ka gafarta min…na san na ɗau haƙƙin ka kai da Mufida sbd selfishness ɗi na ashe ina nawa ne Allah ya tanadi min nawa hukuncin nayi tunanin hikima ta ta janyo ka gare ni ashe mutuwa ta na janyo,am deeply sorry Saheeb ka yafe min dan in sami Peaceful death,dan am dying very soon…”!!
A halin nan da yake ciki na ganin matar sa zata tafi ta bar sa bai ɗaukaka mgnr nata da ta gama yi ba sai girgiza mata kai yake ta yi yana ce mata a’a ta daina mgnr zata mutu..
Da yake ita ta san abinda take ji sai ta ƙyale sa har ta ɗan kuma gathering wani ƙarfin ta kuma nemar yafiyar sa…
Sai ga Saheeb na sharɓar kuka kamar ƙaramin yaro,daɗa damƙe hannun sa tayi ta ce
“Saheeb ka ce ka yafe min dan kar in mutu da haƙƙin ka a tare da ni,pls”!!yana kuka yana rungume ta daga kwancen da take bakin sa na rawa ya ce
“Muhibba na yafe maki..baki min komai ba,haka Allah ya ƙaddara zaman mu zata kasance,ni baki min komai ba kuma na yafe maki”!!murmushi tayi mai tafe da ciwon rasa rai sai ta ce mai
“Nagode miji na..na ji daɗi da ka yafe min..na san zan mutu a matsayin yardarjiyar mace da mijin ta ya yarda da ita..ka min alfarma ɗaya Saheeb”..da sauri ya ce
“Menene alfarmar da kike nema in maki Muhibba”?ɗan tsagaitawa tayi sannan ta ce
“Ko bayan na mutu ka cigaba da so na kamar yadda kake so na a yayin da nake doron ƙasa ina rayuwa,ka so ni fiye da yadda ka so ni while am still alive..promise to always pray for me yayin da na bar ka bana tare da kai..i know am still being selfish but son da nake maka ya kawo haka..promise me that Ƙaunarmu ba zata yanke ba ko bayan bana raye a duniya”!!yana kuka yana kissing hannayen ta ya ce mata
“Na maki alƙawari Muhibba,zan maki addu’a a ko da yaushe..ko a sallah na ko a bacci na”!!murmushi ta mai ta ce mai..
“Ka nema min yafiyar Mufida..ka ce ta yafe min pls”gyaɗa mata kai yayi sai ta lumshe idanun ta hawaye na zubo mata..
A halin gajiya da yanayin da take ciki ta ruƙo sa gagam jikin ta na rawa ta ce
“Zo kusa da ni ka kwanta while am dying,i want u next to me while i will fade away ka ji”!!ran maza ya motsu Saheeb duk ya rikice ya ruɗe ya rasa abin yi haka ya zo kusa da ita ya kwantar da kan sa a ƙirjin ta tana shafa kan sa yana kuka a zuciyar sa kuma yana jin raɗaɗi yana mata addu’a haka tun Muhibba na da nunfashi a hnkl ya fara tafiya har ya tsaya cak..
Yana jin ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi da furta kalmar “sallalahu alaihi wasallam” alamar a zuciyar ta ta fara shahadar sai ta ƙarasa a bayyane..
Ɗago da kan sa yayi ya dube ta yayi zurum kamar statue sai daga baya ya miƙe tsaye ya shafa fuskar ta sannan ya manna mata last kiss a goshin ta ya fito waje…
Ko da suka ga yanayin sa su likitocin,sun san ta tafi ne sai aka shiga ciki kawai aka fara gyara ta…
Yana manne da jikin bango ya fiddo wayar sa sai ya ga kira ya shigo dama wayar a silent yake..
Khalid ke kiran sai ya ɗaga ya kara a kunne ba tare da ya ce komai ba..
Kusan minti ɗaya wayar na kunnen sa kafin ya sauke ya fito jiki a sanyaye ya shiga motar da ya kawo sa dama driver ne..
Gaya mai inda zai kai sa kawai yayi sai driver ya ja motar suka kama hanya…
Motar nasu na tsayawa ya fito da ɗan sauri cikin hanzari ya ƙarasa ciki yana tafe kamar zai haɗa da gudu….
Cikin sauri ya ƙarasa ciki inda da zuwan sa ya fara hango su Ammy hnkl tashe..
Ƙarasawa gare su yayi ya tmby inda fifi take nan hnkl tashe Ammy ta ce mai tana ciki tana tmbyr sa ya jikin Muhibba sai dai bai iya amsa mata ba ya wuce ciki inda fifi ke kwance ana shirya ta zuwa kayan theater..
Tana ganin sa ta miƙo mai hannun ta da sauri ya ƙarasa gare ta,abin is heart touching dan ba abu mai sauƙi bane a ce mutum ya rasa matar sa ɗaya ba cikin biyu sannan ɗayan da ta rage ma tana ƙoƙarin barin sa ba…
Durƙusawa Saheeb yayi a gaban ta yana kuka kamar dai yadda yayi ɗazu a wurin Muhibba bcos ita kan ta a nan ɗin,kalmar mutuwa take ta nanata mai sai da ya rufe mata baki sannan ta ɗan tsagaita..
Yana kukan ya rinƙa faɗa mata yadda yake son ta yake kuma ƙaunar ta,alfarmar da ya rinƙa nema daga gare ta shine kar ta tafi ta bar shi,in ta tafi ina zai fuskanta ya ji daɗi..
Yana kukan tana kukan suka rungume juna ta rinƙa nanata mai kar ya manta da ita ya saka ta a zuciyar sa duk da ta san irin son da take mai shi baya mata irin sa amma ya mata alfarma ɗaya,ko bayan bata raye,kar ya manta da ita a zuciyar sa da rayuwar sa…