KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS
Da karayar zuci ya ce mata ta daina kiran mutuwa dan in har ta tafi shima bin ta zai yi..
“Na san ni mai laifi ne a gare ki Khadija amma ki sani tun farkon ganin da na maki..na tsinci kai na da son ki,so mai tsanani da ƙarfi haɗe da shiga zuciya farat ɗaya,ko da na rinƙa ƙyale ki ina barin ki a dai dai lkcn da kike buƙata na kusa da ke..ba yin kai na bane,Muhibba ce ke ciwo mai tsanani ban san ya zan yi,in na bar ta na dawo gare ki zata ga na so kai na da yawa tunda ke tawa ce ƴar uwa ta ce,wannan dalili ya sa nake ta kasancewa kusa da ita but duk da haka,hakan bai sa na bata rayuwa ba dan ina ji ina gani ta tafi ta bar ni,ta bar mu mu duka,ta bar mana duniyar,a yanzu da na san halin da kike ciki khadijah..bana so in rasa wata matar kuma..bana so in rasa ki..pls don’t do this to me..i will never forgive myself in na zuba ido na kalle ki kika bar duniyar nan khadijah..ki taimake ni ki yi fighting wannan battle ɗin ba dan ni ba ba dan kowa ba sai dan babyn mu da Ƙaunarmu..ki dawo gare ni kar ki rabu da ni,i love u so very much my wife”!!ya ida yana kuka…
Itama kukan take yi sai aka zo aka fara tapping nasa akan ya fita dan har Hamida ta kuma dawowa tana kuka tana son ta shiga ciki amma aka hana ta..
Da ƙyar aka ɓamɓare hannun Saheeb daga na fifi suna kallon juna aka yi wheeling nata zuwa theater room inda suna shiga aka rufe ƙofa take wuta ya kawo mai kala..
Hankula duk a tashe,Hamida ta manne a jikin Hajja tana kuka kamar me,Khalid dake ta namijin ƙoƙari ma a yanzu ya kasa dan abin ya girmi tunanin sa dole ya zauna wuri ɗaya…
Ammy na ta addu’a a zuciyar ta da fatar Allah ya sa a yi aikin lfy,yayin da ta kalle Saheeb ta tmby sa ya jikin Muhibba..
Nan ya faɗa masu cewar ta bar su,salati Ammy ta fara yi Hajja ma haka,tashin hnkl da ba a saka masa rana…
Ana fama da ciwo ga karaya,sabon kuka ne ya kaure a asibitin shi kam daurewa yayi ta yi idanun sa duk sun yi ja jazir..
2 hours later
Wutar ɗakin theater ya mutu sai hnkl su ya koma ga ɗakin suka yi zurum zurum suna jiran jin sakamako..
Fargaba da zullumi duk ya addabi zukatan su musamman Hamida da ta matso gab da ƙofar ɗakin..
Bayan lyk 5 minutes Dr ya fito hannun sa riƙe da baby duk ya jigata,yana fitowa ya dubi fuskar su su duka,tausayin su ne ya kama sa ya rasa ta ina zai fara gaya masu sakamakon da suke jira,haka ya daure yayi na maza ya miƙo babyn yana faɗin..
“It’s a boy”!!daga haka yayi shiru,Hamida ce ta karɓi babyn hannun ta na rawa sannan ta maida idanun ta ga Dr inda ya share zufan fuskar sa ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya sannan cikin tsoron ganin reaction ɗin su ya ce
“Am sorry”!!bai ƙara furta wata kalmar ba Hamida ta fara ganin duhu ko kafin a yi wani yunƙuri har ta fara tanga tanga zata faɗi..
Ammy dake kusa da ita ne ta riƙo ta wacce gwiwar ta ya gama sanyi,ta fashe da kuka tana salati..
Saheeb couldn’t say or do anything but zamewa ƙasa da ya yi ya haɗe kai da hannayen sa biyu..
Khalid kuwa shi ya karɓi babyn dan tuni Hamida ta sume,already Hajja ta tsinke da lamarin a zuci take nata kukan but tana salati a hnkl a bayyane..
Mamuh40
“She is in temporal comma,zata ɗau lkc kafin ta farfaɗo gabaɗaya so sai kun yi haƙuri da yanayin da ta shiga da kuma halin da zata cigaba da kasancewa a ciki for a while”!!..
Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar Ammy da Hajja har ma da Khalid dake riƙe da baby a hannun sa..
Shi kuwa gogan da tun ɗazu yake durƙushe bai ɗago ba bare ya ce ƙala yana dai sauraron yadda su Ammy da sauran ke hamdala amma bai iya ɗagowa ba har sai da ya ɗau lkc sannan ya miƙe tsaye ya taka a hnkl har inda likitan ke tsaye ya tsaya a gaban sa ƙeƙam a gaban likitan yayi folding hannayen sa a ƙirjin sa sannan ya ce da likitan
“Sake maimaita abinda ka ce”shi kuwa likita tunanin sa overwhelming sakamakon nasa ya saka Saheeb har yake son maimaicin amsar da ya faɗa mai..
Gyara position yayi ya maimaita ma Saheeb sakamakon surgery ɗin,kamar ƙiftawar ido Saheeb ya shaƙo sa ya haɗa sa da bango yana shaƙe masa wuya.
A tsorace Khalid ya hau kiran sa yayi da Hajja ke mai faɗar wani irin rashin hnkl ne wannan.
Bai saurari kowa ba dan zuciya ta ɗibe sa sai gurnani yake ta yi yana kuma matse likitan,a taƙaice dai da ƙyar aka ƙwaci likitan yana ta faman tari..
Rai ɓace Saheeb ya hau shi da faɗa yana ta yi kamar ce mai aka yi fifin ma ta rasu..
“Wani irin daƙiƙi ne kai?how om earth zaka zo ma mutani da irin wannan banzar mgn as ur surgery outcome?haka kai aka koya maka ana conveying saƙo!?ko naku da dokoki ne da sigar conveying ma mutum ko patients relatives saƙon outcome ne?ta yaya zaka zo ka ba mu wannan incomplete answer ba tare da ka ƙarasa ba?dubi nan ka gani,that is her blood sister her twin sister,kana gani ai bayan ia gama faɗin banzan sakamakon ka ta sume,what if akwai mai hawan jini ko cardiac disorder kuma ya ji wannan shirmen naka ya yanke jiki ya faɗi ya mutu fah?kana fah ganin halin da muke ciki na nemar sanin mafitar wannan aikin but shi ne ka zo kana bamu irin wannan shashashar amsar”??..
Ammy ce ta tsawatar mai dan yadda yayi ta yi kamar shine mahaifin likitan ma abin was awkward..
Da ƙyar Saheeb ya daina aika ma likitan mugayen kallon da yayi ta aika mai da shi sannan ya ingiza sa ya shige cikin ɗakin da ba a gama gyara fifi ba..
Idanun sa a kan ta yana ta ƙure ta da kallo,daga inda ake gyare ta ne aka hango sa sai ya ɗaga hannu alamar su tsaya ba sai sun zo ba zai tafi..
Kusan 10 minutes yana tsaye yana kallon ta daga bisani ya bar wurin ya fito waje inda ya tarar har Hamida ta farka tana ta kuka tana kallon babyn..
Glancing fuskar babyn yayi ya sallame su akan zai je a kai Muhibba gida dan a mata wanka a kai ta gidan ta na gaskiya..
It’s so touching dan haka Khalid ya bi shi suka bar asibitin dan sosai Saheeb ke buƙatar comfort amma baya cikin hayyacin sa..
Fitar su da mintuna aka turo fifi kan wheel zuwa ɗakin hutu inda aka ba su Ammy damar ganawa da ita a ɗan taƙaitacciyar lkc dan tana tsaka mai wuya ne presently yaƙi take yi da ran ta..
Da shigar su ɗakin Hamida ta zo ta zauna kusa da ita ta hau yi mata mgn tana kuka tana kallon babyn dake ta mutsu mutsu da baki,inda kusan a kashi ɗari toh kaso arba’in kawai ya kwaso na kamannin mahaifiyar sa duk kaso sittin ɗin mahaifin sa ne..
Haka Ammy da Hajja suka yi ta rarrashin ta suna bata mgn,daga bisani da kukan nata yayi tsanani ma karɓan babyn Hajja tayi ta ja gefe ta zauna tana rarrashin ɗan dan ya fara kukan yunwa…
An kai Muhibba gida an sanar da rasuwar ta,toh dama ba wasu ƴan uwa a kusa gare ta ba dole sai a washegari ko da zasu zo dan haka suka ce a mata sutura kawai a kai ta..
Haka aka mata wanka aka mata sallah aka suturta ta aka kai ta final destination ɗin ta..
Sai da Saheeb ya ƙulle kan sa a ɗakin Muhibba yayi ta kuka tuƙuru yana yi yana mata addu’ar rahamar ubangiji..
Sai misalin ƙarfe shida na yamma ya bar gidan ya nufi asibiti dan ganin halin da fifi ke ciki..
Dama su Ammy sun dawo gida dan karɓar gaisuwa tunda fifi na ɗaki ne na musamman ba a so a dame ta sosai sai Hamida ta tsaya tare da ita while Ammy da Hajja suka dawo gidan da babyn dan a mai wanka…
Ranar dai an ga samu an ga rashi,a wurin Saheeb da a ce babyn mace ce toh da tabbas sunan marigayiya zai maida mata wato Muhibba..