KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

Haka nan tun ranar da Muhibba ta rasu fifi kuma ta shige comma,rayuwa ta sauya ma ahalin,wata walwala dai babu ita duk ta kau..

Rayuwar su ta sauya sosai dan daga ranar zuwa yanzu kusan sati biyu kenan fifi bata wani yi ƙwaƙwarar motsi ba sai dai in aka zo yi mata allura ta ɗan juya,da zarar an cire kuma zata cigaba da baccin wahalar da take ta yi…

Likitocin sun sanar da family ɗin fifi cewa wannan miracle ne mace mai cardiac disorder tun a yarintar ta kuma ma da shi aka haife ta ita kuma ta haihu ba tare da ta rasa ran ta ba,toh ba ƙaramin miracle bane…

Asibiti ya zama wurin zaman Saheeb har ranar da aka sallame su suka dawo gida ana bata kula ta musamman,bayan doctor dake zuwa yana duba ta,akwai wasu domiciliary nurses dake kula da ita a gida.

Duk wannan kular bai ma Hamida ba sai da ta ɗora da nata kular,bayan kula da babyn da take yi da har an raɗa mai suna while fifi is in comma..

Babu shagali da aka yi ko ɗaya duk da an yi ɗokin haihuwar amma yadda haihuwar ta zo,sai kowa yayi sanyi aka bari in har Allah ya tashi kafaɗun fifi sai ta zaɓi yadda take so a yi celebrating naming ceremony ɗin…

Babyn madara yake sha tunda ya zo duniya dan babu wani abu mafi sauƙi da zai fi zama a cikin babyn ba tare da ya mai illah ba sama da madarar..

Sunan babyn shine Abdulrahman but aka masa inkiya da Maheer duk da shi Saheeb ya ce in fifi ta farfaɗo kuma sunan bai mata ba toh dole za a sauya sunan..

Ba ƙaramin kula Maheer ke samu daga wurin aunty ɗin nasa ba wato Hamida,ita ke mai wanka ta saka mai kaya ta bashi abinci,tana yi tana kuka,tun mitsitsin babyn nan bai fahimtar Hamida har ya fara dan in yana hannun ta wani lafewa yake yi yayi ta sucking yatsar sa,alamar madarar bata isar sa..

A duk lkcn da yayi hakan toh fah Hamida kuka take yi ta daɗa rungume sa a jikin ta tana addu’ar samin lfy ga ƴar uwar ta..

Shi dama Saheeb ya tare a ɗakin da fifi take take samin kula,duk yadda Ammy ke kula da ita in har ta ga shigowar Saheeb haka zata haƙura ta bashi wuri dan sai yayi ta kushe kular da take ma fifi,daga ya ce nan bai yi ba sai ya ce can bai gogu ba,duk kamar zautacce haka ya dawo gwanin tausayi…

Mgn kuwa ba iyaka,in fara zuba mgn shi kaɗai dan fifin dai ba jin sa take ba,abin sai ya ba mutum tausayi,dan har barin sumar fuska da na kai yayi babu gyara,duk ya sauya dan yanzu be asalin ƙaunar matar sa ke shigar sa,a yanzu da yake ganin kamar rasa ta zai yi dan kullum in ya zo toh burin sa bai wuce a ce ta farka ba amma haka zai yi zaman sa har ya tashi,ko motsu fifi ba zata yi ba…

Kalaman soyayya ya faɗe su wanda da fifi na hayyacin ta toh da zata ce maybe wani Saheeb ɗin ne ba wanda ta sani a matsayin mijin ta mai kawar da kai ba..
Kalaman ƙauna da so kala kala ko da yaushe sai ya faɗawa fifi su,duk ya zauce,ƙaunar ta mai zafi ke shigar sa..

Hamida kan yi kuka im ta gan sa a wannan yanayi,tausayin sa kan kama ta sai dai a halin yanzu,kula da babyn fifi da yi ma fifin addu’a shine abu mafi kusanci da fifin ke buƙata…

Kamar kullum yau ma yana zaune rungume da Maheer a jikin sa yaron na bacci shi kuma yana riƙe da hannun fifi yana mata kalaman soyayya da gwada mata irin ƙaunar ta da yake yi,har da alƙawarin sa na in ta farfaɗo bai kuma matsawa ko da nan da can ne sai ta yarda ta bashi izini…

Idanun sa sun rikiɗe sun yi ja dama su Hajja da Ammy basu jima da barin ɗakin ba,a kullum sai sun sanar da daddyn su fifin halin da ake ciki dan hnkln sa ya kwanta,duk da shima shirin dawowa gida nan Nigeria yake yi dan ya kasance da family ɗin sa gabaɗaya..

Dai dai yana mata surutan nasa kenan hannun ta riƙe cikin nasa sai ya ga kamar hannun na motsi,ɗan tsayawa yayi sannan ya kuma kallon hannun sai ya ga da gaske moving hannun ke yi daga haka ta fara motsawa tana nishi da ƙyar..

A 360 Saheeb ya tashi rungume da ɗan sa ya matso kusa da ita yana ta dariya mai ɗauke da kuka..
Sunan ta ya shiga kira hawaye na zubo mai kamar ba namiji ba namijin ma soldier mai matsayi kamar sa…

Da ƙarfi ya fara kiran sunan nata at same tym yana kiran sunan Ammy akan ta zo da sauri..
Ammy da zata wuce ɗakin dan duba lfyr Hajja dake fama da ciwon kai sai ta ji ana kiran ta da murya mai nuna zumuɗi..

Da sauri ta ƙarasa ta shiga ɗakin,dai dai fifi na tari mai ƙarfi kenan,da ganin haka sai Ammy tayi ƙasa tayi sujjada tana ma Allah godiya sannan ta taso a hnkl ta ƙaraso ga fifi ta riƙo hannun ta cikin nata tana kallon ta..

Rasa abin faɗi Ammy tayi sai murmushi shi kuma already ya fito daga ɗakin ya sauko yana ta faɗin ai Khadija ta farka his wife is awake,she is back to life again…

Kafin a sani tuni gidan ya hargitse da hayani ana ta murnar farkawar fifi,bayan kimanin wasu awowi aka ɗan sarara a ɗakin dan kula da ita da Hamida ke son yi kamar wanka da gyaran jikin ta…

Bata sami damar tmbyr abinda ta haifa ba,tunda dai ta gana da ƴar uwar ta sai ta ji duniyar ta mata daɗi not as she expected kamar da irin mutuwa zata yi ba zata kuma ganin su ba…

Ranar Hamida ce ta kula da ita ta bata abinci sannan ta je ta karɓo Maheer daga hannun Saheeb ta kawo ma fifi,sai daga baya su Ammy suka shigo ɗakin tare da Saheeb dake ta kallon ta kamar zai haɗiye ta tsabar kewar ta da ƙaunar sa da suka kasa barin zuciyar sa yayi saƙat…

Kallon babyn tayi ta yi tana mamakin wai ita ta haife sa kuma take riƙe da shi as his mother,me kuma zata nema a wurim ubangijin ta sama da gode mai da wannan baiwa da ya mata,dan baiwa ce,a lkcn da bata yi tunani ba bata yi tsammani ba sai gashi ta kasance tare da ahalin ta da ɗan da ta haifa da kan ta…

Har dare Hamida bata bar ƴar uwar ta ba sai da Khalid ya ja ra’ayin ta akan ta ɗan bar Saheeb ya gana da matar sa shima tunda tun bayan farkawar ta bai wani sami sararin zama tare da ita ba sakamakon cika da aka yi a ɗakin..

A lkcn itama tayi zurfin tunani sai ta ce ma fifi ta kawo babyn su tafi sai ta ce mata za a maido mata da babyn so take ta kuma kallon babyn kuma..

Da fara’a shimfiɗe saman fuskar Hamida ta fita ta bar ɗakin while fifi ta ƙurawa babyn ido tana ta kallon sa tana admiring babyn…

Tana haka sai Saheeb ya shigo bakin sa ɗauke da sallama sai ta amsa tana kallon sa..
Ƙarasowa yayi ya zauna kusa da ita suka ƙurawa babyn ido sai suka yi murmushi a lkcn ɗaya,ce mata yayi
“Welcome back mon amour”!kallon sa tayi tana mai gyaɗa mai kai kawai..

Daga haka suka cigaba da kallon ɗan har dai bacci ya fara ɗaukar ta tana rungume da Maheer,dabara Saheeb yayi ya gyara mata kwanciya bayan ya ɗauke babyn daga jikin ta..

Shima kwanciyar yayi kusa da ita sai ɗan space da ya bayar kaɗan inda ya shimfiɗe babyn a tsakiyar su ya ƙura mai ido yana ta kallon sa har shima baccin ya ɗauke sa..

Sai a washegari fifi ke sanin rasuwar Muhibba ai kuwa ta mata addu’a sosai da fatar samin rahamar ubangiji a nan kuma aka sanar da ita sunan ɗan ta sai ta ce sunan ya mata daɗi kuma bata buƙatar sauyawa babyn suna daga wanda mahaifin sa ya saka masa..

A cikin kwanakin aka rinƙa taimaka mata tana doguwar tafiya har jikin ta ya warware gabaɗaya ta fara shayar da ɗan ta da kan ta in ta gama ta aika ma Hamida da babyn..
A haka rayuwar gidan ya cigaba da tafiya cikin fahimta da kula da sanin ya kamata..
Ba a cire rai ba,itama Hamida ana mata addu’ar samin nata ƴaƴan in da rai da rabo..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button