KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS
Ba taba ganin khalid tayi ba sai yanzu amma da ganin haduwar sa ta ji wani bakon abu ya ziyarci zuciyar ta wanda bata san menene shi ba amma ta san akwai wani abu da yake rubutacce da zai faru a tsakanin su nan kusa ko anjima..
Magana ne ya fito masa ba tare da ya san ya fito ba hakan ya faru ne sakamakon wani abu da ya rinƙa tsikarar sa wanda bai san menene ba..
“Mu…fffida”!?ya kira sunan da sigar tambaya dan ya tabbatar ko ita din ce sai tayi mamakin yadda ya san sunan ta dan ita ba sanin sa tayi ba sai dai kiran sunan nata da yayi ya nuna mata ya san ta din ne..
Tun kafin ta amsa mai Ammy ta juyo gabadaya tana mai son tabbatarwa kan ta da gaske mai sunan da aka kira din ce ba gizo kunnuwar ta ke mata ba,a yayin da ta juyo din a wannan lokacin Hajja ta juyo itama..
Fuskantar juna da suka yi ne ya tabbatar mata da wadannan sune mutanin da take hira da su a waya kuma take kirgawa a matsayin nata na jinin ta,tana iya cewa bayan soyayyar mahaifin ta da na yar’uwar ta da take da shi a zuciyar ta,toh tabbas soyayyar wadannan mutanin ne ya biyo baya dan bata taso da sanin su ba amma muryoyin su ya saka mata kaunar su a zuciyar ta..
Wani irin runguma Ammy ta ma Mufida wacce ke tsaye tana kallon yar uwar ta dake ganin wani sabuwar shafi da babin tsaka mai wuya dake shirin tunkarar ta a nan Nigeria din..
Hajja ce ta matso kusa da su Ammy cikin farinciki da nuna tsantsar jin dadin ganin jikar ta mafi kusanci da zuciyar ta kuma takwarar ta wacce tausayin ta ne ya rikide ya dawo so da kauna a zuciyar ta..
“Mufida tah matso in gan ki in rike ki in rungume ki ko zan sami natsuwar zuciya,tun safe nake zullumin zuwar ku hankali na bai kwanta ba sai da na ji jirgin ku ya iso a yanzu kuma nake kara samin sukuni da na gan ki da idanuwa na,ban yi tsammani ba amma Allah ya ara min tsawon rai rabo na da ke tun kina jinjirar ki sai yanzu”..
Ihu zata fasa ko barin wurin zata yi ta koma cikin jirgin ya maida ta germany,rasa abin yi tayi,yanzu har a nan din ma babu wanda zai nuna ya san da ita bare ya nuna mata damuwar sa a kan ta bare a kai ga ana ririta ta ana tambayar ta nata lafiyar da rayuwar,a yanzu din ma still fifi ce ba ita ba?..
Take wani irin mugun tsana da kiyayya ya taso mata wanda a kan yar uwar ta duk wadannan abubuwan suka ta’allaka,ita shikenan haka tata rayuwar zata cigaba da tafiya..
Bata ida tunanin zucin ba ta ji su suna fadin Mufida zo mu tafi mun san kin kwaso gajiya ga yunwa…
Tun da Hamida take bata taba sanin tana da wani mummunar fanni a zuciyar ta mai karfi da yake kamar ya rinjayi daya kyakyawar fannin zuciyar ta ba sai yanzu dan kasa rike hawayen ta tayi sai da suka fito kuma ta kasa goge su sai juyawa da tayi ta basu baya tana mai warware nadin mayafin da tayi a kan ta dan ya taimaka wurin boye halin da ta shiga…
Yanzu Tsakani da Allah duk cikin su babu wanda zai tuna da wata wai Hamida? duk hankalin su na a kan Mufida kamar ita kadai ce mutum daya cikin zuri’ar su…
Kasa natsuwa Khalid yayi dan ba karamin dauke mai hankali fifi tayi ba musamman ganin irin shigar ta da yadda ta rinka exchanging tambayoyin da ake mata hakan ya bashi tabbacin ita din kamar shi ne
wato mace ce mai son rayuwa da faram faram bata da dagon kai da daukaka kan ta fiye da wasu halittun…
Tun a nan airport din Khalid ya sallamarwa kan sa ya sami abokiyar tafiya dan da alama ba iya son life kadai take da shi ba wanda shima yake da shi ba,hatta wasu dabi’un ta yana ganin zai zo iri daya da nasa dan haka ya dada saukar da kan sa fiye da yadda ya saba yi a cikin family din su…
Baki daya sun juya da zumar shigewa mota dan su kai gida fifi ta huta,shaf sun manta da Hamida har aka gama kwashe kayan fifi aka saka cikin booth itama zata shige ciki amma ganin kamar babu mutum daya cikin su sai ta tsaya ta hau dube dube
A nan cikin motar kuwa Ammy ce ke kiran sunan fifi akan ta shigo su tafi amma hankalin ta na ga yar uwar ta da ta hango ta chan tsaye..
Karasawa tayi gare ta ta dafo kafadar ta cikin farin ciki game da yi mata magana cikin yanayin jin dadin da take ciki..
“Hamee kin ga yadda su Ammy da Hajja ke murnar ganin mu kuwa,zo mu tafi gida dan duk mu suke jira “murmushin yake Hamida tayi sakamakon gama sauraron zantukar yar uwantan na wai su Ammy da Hajja na murnar ganin su
bayan baro baro ita kadai suka nuna a matsayin nasu yayin da ita aka ware ta kamar ba tare suka zo duniyar da ita mafi soyuwar nasu ba…
Kamar ba zata juyo ba sai daga baya ta juyo da murmushin da ya fi kuka ciwo zuciyar ta kuwa shake yake da kiyayyar yar uwar nata da take ma kallon katanga ce ma farincikin ta dan bayan ta karbe zuciyar daddyn su da na Ammy da Hajja har wanda take ganin Allah ya kawo mata shi shima fifi ta dauko hanyar kwace mata shi
Shin wai ita laifin me tayi ne da babu masu son ta da damuwa da ita ne?
menene aibun ta da bata samin kulawar kowa sai yar uwar ta kadai ke samu,shin ita a haka zata yi ta rayuwa komai nata fifi na samin sa ba tare da ta nema ba?..
Hankalin ta kamar baya jikin ta haka ta rinka bin bayan fifi har suka zo wurin motar wanda sai a sannan Ammy ta tuno da Hamidar amadadin ta ji wani iri ko damuwa batayi ba sai ta ce..
“Wai dama Hamida baki shigo cikin motar bane kika tsaya a waje kamar ba jinin ki kika hadu da su ba?..wannan tambayar ta Ammy ta kara tabbatarwa Hamida shikenan wani bakin cikin zata kuma fadawa ciki bayan wanda ta baro a germany…
Gyada kai kawai Hamida ta iya yi ta shige cikin motar ta zauna a kujerar baya yayin da fifi ta shiga na gaba,da so samu ne daga Ammy har Hajja so suka yi fifi ce a nan inda Hamida take amma ganin kamar ita ce ke muradin zama nan kusa Khalid sai suka bar ta dan kar su saka ta yawar magana…
Wani abin bakin cikin da ya sa Hamida jin zaman motar ya gundire ta taji ta matsu su zo gidan ta kebe ko zata sami sanyin zuciya shine,ita ce a tare da su a bayan seat din motar amma kaf hankalin su na a kan fifin ne
kowa sai son nuna mata so da kauna yake yi ta hanyar tambayar ta akan karatun ta,akan raywarta akan lpyarta a nan kusa da fifi kuma Khalid ne yake ta sakar mata murmushi yana nuna mata kulawar sa shima ta hanyar tambayar ta “if she will be comfortable da zaman nigeria din…
A haka har suka iso babbar gidan dake dauke da different parts ginin duplex mai ban sha’awa saboda tsarin da aka yi ma gidan kadai abin a zo a gani ne,wannan gini ya sa fifi kasa boye kyawun da gidan ya mata ta fitar da shi ta hanyar furta
“Wow,nice house”nan take kuma aka maida hankali hade da ba maganar nata muhimmanci..
Sai nan nan ake ta yi da ita har suka shiga daga cikin gidan inda nan ma wata duniyar ce abin kallo,mai aiki aka kirawo akan ta zo ta kwaso kayan fifi dake booth dan a kai mata wata killatacciyar dakin da aka gyare sa musamman saboda ita nan kusa da na Ammy da site din hajja..
Ana shigo da kayan ne Hamida dake tsaya a matsayin batacciya tayi ta kallon su har suka gama shigewa da kayayyakin fifi ciki
Khalid ne ya fito dan gyara parking din motar sa sai a sannan ya ankara da Hamida…
Yace.”Ohh no”da dan sauri ya karaso gare ta yana furta
“Hamida ki yafe ni ban nuna maki hanya zuwa ciki ba ko?kiyi hakr yar uwar kin nan is so attractive,waidama dagaske ku yan biyu ne?dana ganta hankali na duk ya koma gare ta shi yasa na manta in nuna maki hanyar shiga cikin gida im deeply sorry”..