KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS


5 months later

Abubuwa da dama sun wanzu cikin waɗannan watannin kama daga haɗa daddyn su Fifi da Dr Fatima Yonas da su fifin suka yi dan su zama ma’aurata wanda dama dreams ɗin fifi kenan har ta bar wasiyar in ta mutu toh Hamida ta taimaka mata ta cika mata wannan buri nata,as she is still alive,sai ita da Hamida suka ɗaukaka mgnr har dai su Ammy suka ga dacewar hakan su ma..

Abu dai kamar wasa mutuntakar dake tsakanin daddyn su fifi da Dr Fatima ya ɗaukaka ya dawo babba,dan presently batun bikin su ake yi wanda ya rage nan da sati kaɗan..

A can fannin Dr Fatima kuwa da ƴaƴan ta biyu,bata da matsala ko damuwa da auren dan sun bata support ɗin su 100% as daddyn su fifi is a nice man Throughout his stay a ƙasar tare da su…

Maheer ya fara wayo kuma yanzu ne Allah ya azurta Hamida da Khalid da ƙaruwa dan she is 4 months pregnant,lbrn da ya ma kaf ahalin daɗi,dan sun fara yawa kamar yadda suke buri..

Saheeb dai dama jira yake komai yayi settling na bikin uncle ɗin nasa sai ya ɗau matar sa su koma South Africa tare in ya so sai su rinƙa zuwa visit ko vacation a nan Nigeria tunda a can yake aiki..

Bayan komai ya kammalu suka shirya dan tafiya,sosai fifi da Hamida suka yi kuka kamar sun rabu kenan na har abada,dan kuwa irin shaƙuwa da kusancin da suke yi a yanzu,ko zaman su na da da suka yi suna ƴan mata,basu taɓa yin sa ba,lokuta da dama ba Saheeb ba har Khalid yakan ji mamakin irin ƙarfin kusancin su sai dai in ya tuna ƙarfin jini ya fi gaban wasa sai ya share..

A haka rayuwa ta basu second chance suka fuskanci juna tsakanin su da kuma tsakanin su da iyayen su,a yanzu ne suke zaman so da ƙauna da fahimtar juna fiye da da da aka sami tangarɗa as result of ignorance da negligence ɗin su wanda basu fatar ko a wani gidan ne haka ya faru dan babbar illah ce su sun gani da idanun su..

After alk d luv and care da suka rinƙa nunawa Mufida har ya ma Hamida illah a zuciya ta so kauce hanya a ƙarshe Allah bai dubi halin da suka jefa Hamidar a ciki ba ya saka ƙaunar Mufida a zuciyar ta bayan so many attempt to get rid of Mufida..

Wannan shine clear definition na ƙauna da ake kiran sa da jini,dan ƙauna a jini yake ba kamar so ba da a baki ake faɗan sa ba wataran yana iya gushewa..


Bayan wasu shekaru kamar biyar a rayuwar su fifi,Allah ya azurta Hamida da ƴaƴa biyu na farkon itace mai sunan fifi na biyun kuma mai sunan daddyn su Khalid marigayi,while fifi kuma tun bayan Abdulrahman bata kuma haihuwa ba sai bayan shekaru uku inda ta haihu still through surgery kafin ma ranar haihuwar dan lfyr ta da na babyn,a wannan karon sai Allah ya bata ƴan biyu mata ɗaya ta ci sunan Ammy suna kiran ta da mami,ɗayar kuma sunan Hamida suna kiran ta Rayhan…

Tsakanin fifi da Nigeria shine ziyara dan tun bayan bikin dadyn su da Dr Fatima da ta zo,bata kuma zuwa ta jima ba sai dai ta zo ta ɗan yi kwanaki ita da Saheeb su koma..
Akwai shaƙuwa a tsakanin ƴaƴan su wanda hakan ya masu daɗi dan basu so rashin ƙaunar da ta so ta samo asali a nasu rayuwar ta faru a tsakanin ƴaƴan su…

Fifi kam bata da abin cewa sai godiya ga Allah swt da ya mallaka miji irin nata mijin wanda da ta so butulcewa Allah da zaɓin da ya mata but da yake matar wani bata auren mijin wata shi ɗin ne dai nata ƙaddarar sai Allah ya jefa mata so da ƙaunar sa a zuciyar ta tun bata sauraron zuciyar ta har ta natsu ta zauna da shi gashi a yau Allah ya albarkaci rayuwar auren su da abu mafi tsada da ko kuɗi bai isa ya siya maka shi ba,wato ƴaƴa..

Hamida ma na cikin gode ma Allah da ya bata nata zaɓin mijin ya kuma saka ƙaunar junan su cikin zukatan su,rayuwa mai daɗi da tsafta suke yi,kula da juna kuwa ba a mgn dan kullum cikin yin sa suke,ƴaƴa ko aikin Khalid ko nata ita kan ta aikin baya hana ta ba mijin ta kula yadda ya kamata,kamar yadda a kullum Saheeb baya gajiya da gwada ma Khadijatul Mufidah salon son da yake mata,toh haka Khalid baya gajiyawa gurin ganin ya kuma dasa ƙaunar sa a zuciyar matar sa Ayshatul Hamida…

Duka duka a nan na kawo ƙarshen wannan lbr nawa mai suna Ƙaunarmu,inda nayi kuskure rabbi ya gafarta min inda nayi daidai Allah ya bani ladar sa,ubangiji Allah ya bar ƙauna da zumunci,taku ce
#Mamuhgee

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70

Leave a Reply

Back to top button