KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

KAUNARMU COMPLETE HAUSA NOVELS

jin kalmar mutuwar da ta kira sai da Ammy ta ji bugun zuciyar ta ya dadu dan sam bata son jin wannan kalmar bare har ya kasance ya alakantu ne da fifi…

Dada rungume ta tayi tana danne hawayen dake kokarin fin karfin ta ya fito murya na rawa ta ce.
  “A’a Mufida ta kidena cewa hakan ba zaki mutu ba har sai kin ga yayan ki,sai kin more su mu ma mun gan su,tare zaki rayu da yayan ki har girman su,da yardar mai rahama yayan ki ba zasu yi maraicin rashin uwa ba kamar yadda ke kika taso cikin ta ba Allah ya jikan mahaifiyar ki”..

Hajja da ta rigada ta ta fara hawaye tun bayan jin kalmar mutuwar da fifi tayi sai ta kasa hakura ta yi magana..

Tace”A’a Mufida ba yanzu zaki mutu ba kuma bana son kara jin kalmar nan ta fito daga bakin ki”..

Kallon ta fifi tayi ta kuma kallon Ammy da yanzu ta raba jiki da ita,ta kuma juyawa ta kalli Khalid da shima ya dan shiga wani yanayi sai ta basar da zancen duk da ta san ita din ba mai tsawon rai bane rayuwar ta mai iya datsewa ne any moment kuma ita so take ta saka murmushi a fuskokin kowa kafin ta rabu da su ba wai ta rinka saka su a damuwa ba,abaxata ta hau yin dariya tana fadin
  “Ammy,Hajja, Khalid kun bani dariya,ashe haka kuke?wasa fah kawai nake maku dama gwada ku na yi dan in ga yawan son da kuke min kuma na gani,ta gwalo ido cikin wasa”sai dai Hajja ban gane miki bafa,fada min gaskiya hala dama kin matsu ne in tafi in baki wuri dan ki kwace min saurayi”?
da sigar tsokana tayi maganar..inda Duk ta saka su dariya ba kadan ba

duk da akwai kalmar rabuwar nan dai a wannan zancen nata but ta saka su nishadi..

Ganin duk sun sake ran su ya sa itama ta taya su dariyar har dai suka zazzauna aka hau serving nasu abinci..

Sosai fifi ta ci abincin dan ba zata iya tuno rabon ta da cin abincin gargajiya irin ta kasar ta Nigeria ba sai yanzu kuma da yake abincin da cikakkiyar soyayya aka bata shi sai ta ji kawai kaunar family din nata na kara ninkuwa a zuciyar ta fiye da da kafin ta san su in person..

Da suka gama cin abincin ne Khalid ya mata tayin fita zaga gari kafin dare,ai kuwa bata ja da tayin sa ba dan ita kan ta ta fi son haka,ko ba komai ta san zata fara ajiye tarihi da memories masu wuyar mantawa musanman tare da dan uwan ta kuma wani bangare na rayuwar ta wanda bata san ya zata fassara sa ba..

Da kazar kazar din ta ta tashi daga kan dardumar tana mai yi ma Ammy da Hajja godiyar saka ta jin ita din wata ce a gare su hade da yi masu sallamar sai sun dawo..

Sosai Hajja ta rinka gargadin Khalid akan kar ya kuskura yayi tukin ganganci da zai jijjiga jikin Mufida,shi dariya ma Hajjan ta bashi ganin yadda duk hankalin ta ya bi ya tashi akan kar a taba lafiyar takwarar ta,ita fifi in ta nata ne bata ki a yi ta rough driving din ba dan ta fi son hakan sbd ya fi dadi da saka annashuwa a gare ta a kuma zuciyar ta…

Juyawar su kenan da nufin fita Hamida ta bayyana a gaban su tana saukowa daga sama..

Tun daga kan babbar dardumar idanun ta ya nuna mata har an yi family lunch an gama kuma cikin nishadi aka yi sa dan ga yadda abinci ya barbarzu alamar mutani daban daban ke ba mutum daya abincin..

Babu inda hankalin ta ya kai sai ga fifi,wani abu ne ya taso ya tsaya mata a kirjin ta rasa abin yi tayi…

Idanun ta ne ya dawo kan yar uwar ta da mutumin da ta jima da mai masauki a zuciyar ta,bayan an gama cin lunch ba tare da ita ba yanzu kuma fita za’a yi ba tare da an damu da nemar ta ba…?

Idanun fifi ne ya sauka kan Hamida da ta tsaya cak a fourth to the last step ta kasa karasowa tsabar daurewar kan da ta tsinci kan ta a ciki…

“Hamee tun dazu nake ta nemar ki sai da fa Khalid ya zo ya nuna min dakin ki muka zo tare,kinyi bacci ne? munyi ta yin sallama baki amsa mu ba hope you are ok dan yanzu fita zamu yi ni da Khalid ya ce zai kai ni in zaga gari kafin dare,na san ba zaki taho ba ko na ce ki inaso dan haka mu sai mun dawo,go ahead am sure you will love the lunch da Ammy ta hada mana….na gargajiya ne mai dadi,just enjoy har mu dawo ok sis”!

karasa maganar tayi tana mai dan buga kafadar ta alamar comforting din ta take son yi cikin nuna tsananin damuwarta akan ta..
Hamida kuwa batace uffan ba

Bayan haka fifi ta juya ta fita Khalid na bin ta a baya suna magana kasa kasa suna dariya wanda ya kuma kunna wutar kiyayyar fifin a zuciyar Hamida…

Su Ammy dake daga cikin parlor din ne ta tsaya kare ma kallo,cikin kitsa maganganu ganin wai duk wannan abin da ya faru babu wanda ya lura da ita kuma ba a aika a kirawo ta ba haka suka ci abincin su cikin farinciki,ita kadai ce ake wa wariyar launin fata dan bata cancanci kaunar kowa daga cikin family members din nata ba,wannan bakin ciki da me yayi kama…?

Fasa saukowar tayi kawai ta koma dakin ta duk da haka bata sami natsuwar zuci ba sai kai kawo take ta yi a karshe zuciyar ta ya saka mata ta tafi dakin fifi dan ganin ko nan ma an nuna bambancin kamar ko da yaushe..

Fitowa tayi ta nufi hanyar babbar balcony din dake upstairs da nufin tambayar ma’aikatan gidan dakin fifi..

Tana tafe ta ga gilmawar wata sai tayi saurin kiran ta ta tambaye ta dakin Mufida ai kuwa ta kai ta har dakin inda da shigar ta ta ga abin da ya girgiza mata zuciya da ruhin ta dan in akwai aljannar duniya toh dakin fifi ya dace da wannan sunan…

Komai yayi ne kusan dukan abunda take muradi su aka zuba a dakin fifi abin nan ya sake tayar mata da hankali..

Danne damuwar ta tayi ta fita a dakin ta koma nata dakin,bata jin marmarin dandanar abincin gidan ma dan haka cookies din ta da ta zo da shi a jaka ta fiddo ta hau ci tana jin ciwo a zuciyar ta..

A haka tun tana dannewa kar tayi kukar bambancin da ake nuna mata har ta bar hawayen suka zubo,shaidan kam sai dada tunzira zuciyar ta yake yi ta rinka saƙe saƙe kala kala akan yar uwar nata daga baya ta dauko laptop din ta dan rage zugin da zuciyar ta ke mata dab wayar ta kam bai da amfanin komai dan in dai wai dan a kira ta ne dan jin ya take bayan ta bar kasar germany toh tasan yaudarar kan ta zata yi dan ba kiran nata za a yi ba

Ita kanta ta san izuwa yanzu favourite din kowa da kowa ta amsa kira ya fi sau a kirga daga saukar su hala har yanzu da suka fita da mutumin da take jin shi a zuciyar ta ma hakan ne…

Tunowa da yanayin farincikin da suka fita ciki dazu ya sa ta ji kamar ta masu mummunar addu’a amma haka ta daure ta maida idanun ta ga kallon da ba wani gane shi take yi ba dan hankalin nata ba a kan kallon yake ba…

MamuhMamuhgee

zafafa biyar na kudine ka nemi wannan numbern ka biya kudinka ko katinka

07067124863
09032345899

7

fitar su agidan Khalid yafara tukinsa a hankali gudun kar ma wani ya gani aje a fadawa hajja,yana hawa kan titi ya kalli fifi ya ce da ita ta gyara zamanki da kyau yan mata zamu fara tukin mu ko?.. Murmushi suka maida ma juna

Ita a dadin ta dan dama hakan ta fi so,tun daga haka sai ya kara speed din motar yana tukin juye juye in yayi sai ya kalle ta ya ce speed din yayi sai ta girgiza kai suna dariya ahaka sai ya kara gudun,a haka a haka ya rinka kara speed har ya kure zuwa last speeding point din inda fifi sai ihun murna da dadi take ta yi dan tunowa takeyi da last drive din su a germany tare da kawayen ta.

Wurare da dama ya kai ta ya kuma bata dukkan lokacin sa cikin sukuni,bai yi rushing din ta ba komai a natse ya bar ta tayi,tun daga gidajen ganin kayan al’ajabi da aka bar su su bude a wannan lokacin dan har wuraren shakatawa sai da Khalid ya kai fifi kuma bai gajiya duk wani tambayar da zata mai akan abin da ta gani haka zai bata cikakkiyar amsa mai gamsarwa…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Leave a Reply

Back to top button