THE WORLD MAN (NAMIJIN DUNIYA) COMPLETE NOVEL

Sosai ran Namijin duniya yakai ƙololuwar ɓaci lokaci ɗaya idanunsa suka sauya kala yayinda jijiyoyin kansa suka tashi ruɗu-ruɗu saboda yasan halin abokan nasa indai sukaga yarinya ko ɗiyar uban waye sesunsa anɗakkomasu ita ɗago jajayen idanunsa yayi ya zubawa aminan nasa cikin takaici yace”ya isheku haka banason irin wannan zancen banzan naku kuma wallahi duk wanda kukasa ya ɗakkota sede uwarsa ta haifi wani domin indai ina numfashi bazan taɓa bari wani ya ɓatamata rayuwa ba”.
mamakin yadda ya haƙiƙance yanata zazzaga musu masifa ne yakama su Ahmad domin tunda suke a rayuwarsu basu taɓa ganin Namijin duniya a cikin irin wannan halinba dafashi Adam yayi yace”anya ko abokina baka kamuba kuwa a tinanina inkaji wannan shawarar tamu murna zakayi amma se mukaga akasin haka saboda irin abinda yarinyar nan takemaka yayi yawa dukfa abinda kaga munayi saboda farin cikinka mukeyi badon wani ba”.
A matuƙar fusace yace”Wannan ba mafita bace face shawarar banza data wofi wadda zata kaini ta baroni wannan shine abu mafi muni da ƙazanta wanda zaku aikata acikin rayuwarku domin narantse da wanda raina ke hannunsa idan ɗaya daga cikinku yayi kuskuren taɓa koda tafin hannunta ne sena salwantar da rayuwarsa dan bazan nuna nasankuba wlh sena nunamuku true colour ɗina dan zanbaku mamaki a duk biye-biyen matanku bantaɓa sakamuku bakiba dan haka salin alin idanunku subar kan wannan yarinyar inba hakaba zakusan wanene Abdallah”.
Da mugun mamaki suke Kallonsa jin furucinsa kasa furta komai sukayi se kallon dake nuni da tsantsar al’ajabi da suke binsa dashi baka jin ƙaran komai face saukar numfashinsa da yike fitarwa kamar wani mayunwacin zaki ganin irin kallon da suke binsa dashine yasa a zuciyarsa yace”ni Abdallah meke damuna ne mena faɗamusu naga suna bina da kallon mamaki na rasa meke damuna kan wannan kucakar yarinyar ne”.
dake miskilin ƙarshene bazaka lura da yanayin da yike cikiba sema wani ƙara shan kunu daya ƙara ajiyar zuciya Ahmad ya sauƙe kana yakafe sa da idanu na wasu mintuna ahankali ya furta “kadde kafara sonta my man”.
Wani banzan kallo ya watsa masa cikin haɗa girar sama data ƙasa yace”Banason maganan banza Meyakawo maganar so aciki wannan zancen kuma”.
Adam da mamaki ya gama cikasa ne yace”Daga cikin kalamanka za’ah fahimci akwai kishin yarinyar me ƙarfi a tare dakai domin badan soyayyaba babu abinda zesa kafaɗa mana magana irin wannan wadda tun tasowarmu baka taɓa faɗamana ba “.
ajiyar zuciya ya sauƙe se yanzu ya tuna irin abinda yayiwa aminan nasa dafe kai yayi tare da cewa “Babu ɗigon soyayyarta acikin zuciyata hasalima tsanarta nakeji me tsanani ko wa’inda suka fita ajima ban kulasuba ma bare wata ita kona rasa matar aure bazan taɓa auren wannan kwailar yarinyar ba wadda ko ƙirjin kirki bata dashi wa’inda suka fita komaima basa gabana bare wata bera irinta anma ku tuna lefin data aikata be kai in ɗauki irin wannan hukuncin akantaba baya ga haka bazanso ace anyiwa ƴata ƙanwata ko matata irin wannan ba shin Mezesa Ni na ruguzawa wata rayuwarta duk abinda nayi nayisa ne domin tana ƙarƙashina banaso ta ɓatamun suna a idon duniya “.
Kai suka jinjina cike da gamsuwa da kalamansa Murmushi Ahmad yayi yace”Wallahi har nayi zaton ka faɗa tarkon ƙaunarta “.
Taɓe baki Namijin duniya yayi tare da shafa lallausar suman kansa data sha gyara yace”Allah ya kyauta wa’inda suka fita komaima basu isheni kallo ba bare ita banason haka mubar wannan zancen”.
“sorry my man kawo kunnenka kaji wata hanya mafi sauƙi data kamata muyi maganinta cikin sauƙi ba tare da tashin hankali ba”.
“ok”.
nanya matsa Ahmad ya raɗamasa magana a kunne wadda nikaina real eeshow banji me yike cemasa ba se gani nayi Namijin duniya ya saki wani killer smile wanda shikaɗai yasan ma’anarsa bayan wani lokaci suka miƙe suka nufi gida zuciyar kowannensu cike da farin cikin samun mafita akan Inteesar.
Ɓangaren Inteesar ko tunda ta dawo gida take kuka hankalin Khadijat yayi mugun tashi ganin yadda ƴar uwarta keta kuka taƙi magana murya a raunane Khadijat tace”Auntyna wai yaushene zaki dena zubar da tsadaddun hawayenki akan abubuwan da basu taka kara sun karya bane sanadin kukannan naki yasa ƙannenki a gida sun rainaki a wajema kina niyyar kijawa kanki wani rainin ganin kinamasa kuka shiyasa yike ƙara rainaki dan Allah abinda nike so dake ko yayimiki abu dukmun ɓatamiki ran daya yi karki ƙara nunamasa ko a fuska kinji haushi idan yaga yana yimiki abu bakya damuwa haushi zekoma yanaji ki share hawayenki kinji Auntyna maganin kukana idan kina kuka ni kuma waye ze sharen nawa kukan inaso kiyimun wani alƙawari Aunty”.
sosai kalaman Khadijah sukayi tasiri a zuciyar Inteesar ta share hawayenta tace”inajinki Khady”.
“Aunty kiyimun alƙawarin duk inda kike zaki zama me ƙarfin zuciya bakomai zaki riƙa yiwa kuka ba koda ko ya cancanci hakan karkiyi agaban maƙiyinki”.
wani murmushi ne ya suɓucewa Inteesar wanda har seda beauty point ɗinta suka bayyana tace”nayimiki my small sis insha Allah “.
“yauwa gwara da kika faɗamata Khady nima tintini nike bata wannan shawarar taƙiji”.
nan sukaita hirarsu cike da nishaɗin bayan wani lokaci suka raka Hauwah har gida sannan suka dawo cikin farinciki suka nufi ɗakin Ummahnsu.
AFTER ONE WEEK
Abubuwa da yawa sun faru cikiko har da soyayya me ƙarfi dake gudana a tsakanin Zaid da Inteesar wanda a yanzu basa iya cikakken 1hr ɗaya beji ɗaya ba ɓangaren Namijin duniya ko duk abinda yasan zeyi yaɓatawa Inteesar rai shiyikeyi dan yaga fishinta bata taɓa nunamasa taji haushi koda abu yaɓatamata rai sede ta nemi wani gurin inda tasan bame ganinta tasha kukanta domin ko bata tagaleshi ba shi seya tagaleta abu kaɗan zatayi yashiga lallatsemata ƙirji yace shine purnishment ɗinta ko kuma yashiga kissing ɗinta da sunan hukunci ɓangarenta da Zaid ko shirye-shiryen biki Umminsa keyi ka’in da na’in domin Abbanshi yace bayason a wuce satinnan ba’ayi bikinba saboda yadda Zaid yabasu labarin yadda sukayi da Uwar Gwarama da alƙawarin da yayi na bayason bikin ya wuce sati ɗaya.
Zaune take a offuce ɗin Namijin duniya waya manne a kunnenta se zabga murmushi take tace”meyasa kake amsa na Hauwah ni nawa kace bakaso”.
daga ɗaya ɓangaren Zaid yace”haba My 100% sure ɗina nina iya sakamiki suna se nine zakiji kunyar samamun suna ni meyasa banji kunyar canzamiki sunanba to nidai ki zaɓamun “.
yaƙarasa zancensa cike da shagwaɓa kamar wani ƙaramin yaro dariya tayi sosai sannan tace”to ɗan Ummih aikai namiji ne”.
“au My 100% sure kina nufin mu maza bamu da kunya kenan”.
zare sexy eyes ɗinta tayi kamar yana kallonta tace”nina isa faɗawa My Husband to be ɗina bashi da kunya”.
cikin jindaɗin sunan data kirashi dashi yace”wow ɗan ƙara faɗa inji amma sunan yamun daɗi sosai”.
cikin shagwaɓar data riga ta zamemata jiki tace”bazan faɗaba nidai ba ruwana”.
“hmm to naji da wanne sunan kika saka a number ta nima zan faɗamiki sunan dana saka akan number ki”.
cikin shagwaɓaɓɓiyar murya ta maƙe kafaɗa kamar wata ƙaramar yarinya tace”naƙi wayon baseka faɗamun kowa ya riƙe nasa “.
dariya Zaid yayi tare da cewa”to ai shikenan tunda bazaki faɗaba ammm dama Ummih tace infaɗamiki ki sanar dasu Ummah gobe za’ah kawo lefe”.
“tom zan sanar dasu insha Allah”.
“yauwa anjuma zan shigo da yamma zankaiki ki gaida Ammi”.
“toh Allah yakawoka”.
“Ameen ya Allah I love you my 100% sure”.
“love you more My husband to be”.
cikin shauƙin juna sukayi sallama tana kashewa cikin zumuɗi tayi dialing no Hauwah tana ɗagawa tace”Hauwah yace gobe zasu kawo lefe”.
cikin murna tace”masha Allah ,Allah yakaimu amma gaskiya basu kyauta manaba memakon yafaɗamana tun wuri musan snack ɗin da zamuyi amma se yanzu”.
“wlh kuwa sannan kuma wai zezo anjuma muje mugaida Ammin su”.
“toh Allah yakaimu”.
“ameen ya Allah”.
tana kashewa juyawar nan da zatayi sukayi ido huɗu da Namijin duniya ya zubamata narkakkun sexy eyes ɗinsa da alama ya daɗe tsaye kanta batama san yana na kallonta ba .