THE WORLD MAN (NAMIJIN DUNIYA) COMPLETE NOVEL

AFTER ONE DAY
Sanye Abbah yike da Uniform ɗin masu shara sega wani me irin kayansa gaisawa sukayi yace”a’ah Ahmadu se yanzu kazo”.
“a’ah na daɗe da zuwa ina bayane yanzu gashi inji Oga tin ɗazu yabayar yace abaka inkazo”.
ansa Abbah yayi yana dubawa yaga takardar sallamace daga aikice sosai hankalinshi ya tashi yana ƙoƙarin tafiya office ɗin Ahmad Malam Ahmadu ya dakatar dashi tare da cewa”yace kar abarka ka shiga gurinsa”.
sosai hankalin Abbah yaƙara tashi a wannan ranar duk yadda yaso dayaga Ahmad abu ya faskara dole haka ya tafi gida.
Jiki ba kwari haka Abbah yashiga gida tare da zama kusa da Uwar Gwarama jiki a sanyaye kallonshi Uwar Gwarama tayi tare da cewa”lafiya kashigo hannu na dukan cinya Malam”.
“Ladidi an koreni a aiki”.
Khadijat dake zagayowa dake zagayowa daka backyard ɗin gidan ce wani farinciki duk ya lulluɓeta da murnarta ta shiga ɗakinsu tana ƴan waƙe-waƙenta ɗago kai Inteesar tayi daga karatun Alqur’anin da takeyi tare da cewa”meyafaru naga kina murna”.
“Abbah aka kora a gurin aikinsu”.
“shine kuma kike murna”.
“eyi ai gwarama da aka koresa daga aikin koba komai a dena banbantamu da ƴaƴan so shima yaji yadda mukeji a zuciyarmu na abinda yikemana kamar ba ƴaƴansa ba duk ya tsanemu ni wani lokacin har tinani nike anyako Abbah ne babanmu”.
“Khadija meyasa kike irin wannan ne koba komai ai mahaifinmune kidena irin wannan inkuma ba hakaba zamu ɓata”.
“yi haƙuri Aunty”.!!!!!!
Votes and Comments
Plz share fisabilillah
Dan Allah a tayani share
Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.
???? THE WORLD MAN
(NAMIJIN DUNIYA)
MALLAKIN
REAL EESHOW
HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…
BOOK 1
PAGES 0️⃣3️⃣➡️0️⃣4️⃣
Jiki ba kwari Abbah yamiƙe yaɗauki buta ya zagaya be wani jimaba segashi yafito yaƙara zama kusa da Uwar Gwarama baki buɗe Uwar Gwarama ke kallon Abbah sannan tace"amma dai gaskiya Malam se yanzu na yarda da zancen Uwani na cewa zuciyarka a mace take murus yo inbanda haka meyasa bazaka nace gurin wannan yaro arziƙinba kaji ba'asin abinda yasa ya korekaba se kawai ka yayo jiki ka tawo gida to wlh Malam ahir ɗinka dan tashi zakayi ka koma bazan riƙa ci dakai da wata ƙatuwa da ƴaƴanta ba akan wanne dalilin kamar kai nikeyiwa neman imma zaka tashi kaje kaji meke faruwa kaje danni bama zan iya cida me ƙashin tsiyaba wallahi wani yahana uwarsu yin sana'ah tace se ƴaƴanta sunyi karatun boko yanzu aisaci boko a wuta aikaga ko maga abinda bokon nasu ze tsinanamasu dukda bamma yadda bokon akeyiba ba babban bokoba wanda harka mutu baza'ah dena yimaka gori ba danni bame ɓatani ƴaƴana basu jawomun abun kunyaba na wata su jawomun haka kurum a'ah ba dani za'ayi wannan sa lallen kazarba atoh".
har Uwar Gwarama ta gama zazzage Abbah becemata ƙalaba yashafa sumar kansa tare da cewa”to a temakeni da abinci konaji sanyi a zuciyata”.
wani banzan kallo da Uwar Gwarama ta makawa Abbah da sauri ya miƙe tare da washe baki yace”ya haƙuri bara inje ɗin”.
“yadaifimaka “.
nan Abbah yafara tafiya daidai nan Wata matashiyar mata tayi sallama wadda bazata wuce shekaru42 ba jin Uwar Gwarama bata ansamata ba haka Abbah shima ta nufi ɗakinta.
Tana shiga Khadijana yiwa Inteesar kitso ta saki da sauri ta rungumeta tare da cewa”sannu da dawowa Ummah”.
murmushi Umma tayi itama Inteesar ta rungumeta rungumesu tayi gabaki ɗayansu sannan tace”ko ni Aishatu zaku karyani ku sakeni inzauna”.
murmushi sukayi gabaki ɗayansu suka zauna cikin farinciki Inteesar tace”ya aka baro su Halima”.
“suna gaidaku”.
cikin zumuɗi Khadija tace”Ummah kinsan wani abun farin ciki ko daya samemu kuwa”.
cikin farim ciki Ummah tace”Auta meya samemu haka naga kina farin ciki haka”.
kallonta Inteesar take da mamaki dan ita batasan meya samesu na farinciki da Khadija keta farin ciki hakaba tana wannan tinanin ta tsinkayi muryar Khadija na cewa”Ummah anfa kori Abbah daka gurin aikinsa kinji daɗin danaji kuwa “.
haɗe rai Ummah tayi tare da cewa”Khadija meke damunki ne haka da har kike farinciki dan an kori mahaifinki daga aiki ashe duk huɗubar danakemuku ke bata shiga kunnenki Khadija mahaifinku nefa kome yike yimana bekamata kiyi farin cikiba Khadija “.
“ai Ummah……”.
saurin katseta Ummah tayi ta hanyar cewa”ya isheki haka a rayuwa duk wanda bashi da haƙuri baze kai labari ba kuma komai na duniya ɗan haƙurine watarana se labari komai kaga yasamu bawa da sanin Allah kuma komai muƙaddarine daga Allah ba’ah taɓa dawwama a abu ɗaya shiyasa kullum bani da abinda zancemuku sede kuyi haƙuri kunji shi haƙuri riba garesa”.
Ummah na cikin yimusu magana Uwar Gwarama ta buɗe ƙofa cikin masifa tace”ga kayana can kije ki wanken”.
ta wuce fuu Ummah takalli Inteesar tare da cewa”tashi kije kiyimata”.
“toh”.
zumɓurar baki Khadija tayi tare da cewa”saboda Allah Ummah duk gasu Bilki da Ruƙayya bazasuyiba se Aunty saboda itace karkatacciyar kukar gidannan me daɗin hawa haba”.
“au bakiji nasihar dana gama yumuku ba kenan ko saboda kinada kunnen ƙashi ko”.
Inteesar ta fita tsakar gida Khadija ma tabita tashiga tayata cikin kayan harda nasu Bilki da Ruƙayya hattana pant ɗinsu da suka gama period seda suka haɗa nan Inteesar tashiga wankemusu.
Kwance yike akan sofa ya lumshe idanunsa kamar me bacci a hankali ya buɗe idanunsa da suka yimasa nauyi yayi kana ganin fuskarsa zaka gane yanada damuwa tashi yayi ya nufi tanƙamemeb wardrobe ɗinsa ya buɗe ya zari wasu haɗaɗɗun ƴan kanti yasaka ya feshe jikinsa da turarukansa masu daɗi kanshi sannan ya ɗauki phones ɗinsa ya fita.
A hankali yike sakkowa daga stairs yana ɗaura gucci watch a hannunsa tunda ta ɗaura idanunta akansa ko ƙiftawa batayi harya ƙarasa sakkowa cikin takunsa kamar yana tausayin ƙasa yaƙarasa sauka ya nufi falon Haneefa ce zaune ita kaɗai cikin wasu english wears riga da wando rigar kusan rabin ƙirjinta a waje fuska tasha heavy make-up kamar ga atarch yare-yare da murmushi tace”morning sweetheart”.
Abdallah(Namijin duniya) kallo ɗaya yayimata ya ɗauke kansa gefe yaƙara haɗe rai kamar wanda aka aikomasa da mutuwa yace”lfy what of you”.
“lafiya ƙlau”.
ya miƙe ya nufi ƙofa ɓangaren granny ɗinsa ya nufa yana shiga ya tadda Abbih ɗinsa da Mummy zaune ƙarasawa yayi bakinsa ɗauke da sallama ƙasa-ƙasa taɓe baki Innah tayi tare da cewa”yaudai ban dafa abincina dakaiba dunkum dangin tsaka atoh inma zakaci abinci da Mamanka tayi kaci dan bazan bakaba”.
dariya Mummy tayi tare da cewa”rabu da ita Son ai se inbaka nawa”.
murmushin gefan baki yayi ya zauna tare da cewa”ina kwananku “.
“lafiya ƙlau Son yaka tashi”.
“lafiya ƙlau Abbih”.
“masha Allah”.
miƙewa Abbih yayi tare da cewa”Ammi ni zan wuce inada wani meeting”.
“to Allah ya tsare”.
“Ameen ya Allah Son seka fito”.
“toh Abbih”.
nanya fita Mummy ta miƙe tace”Ammi se anjima Son seka dawo “.
“toh”
yafaɗa a daƙile Mummy washe baki Ammi tayi tare da cewa”toh Fatimah Allah yayimiki albarka”.
“Ameen”.
nanta tafi murmushi Abdallah yayi ganin Ammi ta kauda kanta gefe yaƙarasa gurinta tare da cewa”Ammi an tashi lafiya”.
“da ban kwanaba ka ganni zaune kamar duniya ne”.
murmushi yayi yace”Ammi tuba nike ayi haƙuri”.
“aini tunda kaƙi jin maganata nabarka da halinka ace yaro kamar wanda akayiwa mugun abu bakason yin aure anjuma nan zan shirya inje gidan aminiyata inma wani abun akayimaka naji dan bazan bari a cuci jikana kwalli ɗaya ba a duniya atoh bara in zubomaka abinci inshirya ku ajeni gidan Ta Annabi ina dalili ina ɗan mafari a sabautamun jikana ga abokinka har zeyi aure nanda sati biyu amma kai shiru akeji “.
bece komaiba a ta wuce a zuciyarsa yace”hmm Ammi bazaki gane abinda ke damuna ba a duniya ba macen da zata yarda ta aureni matsawar tasan meke damuna”.
yana wannan zancen Ammi ta fito ta ajemasa plate ɗin irish kaɗan yaci ya miƙe tare da kallon agogon hannunsa yace”Ammi sena dawo bara se su Muhd su kaiki ni kuma na wuce inada meeting”.
“toh seka dawo”.
nanya fice ta taɓe baki tare da cewa”imma wanine yasamun hannu agun jikana zanji koma meye”.
nanta tafi ɗaki ta shirya ta fita suka tafi.
Yana fita ya shiga mota suka fara tafiya har sun ɗauki hanyar gurin aikinsu ba tare daya buɗe idoba yace”Hospital zamu”.
“toh Oga”.
nan suka canza akalar motar suka nufi wani katafaren asibiti suna isa ya zagaya ya buɗemasa nanya fita cikin takunsa na isa harya isa ciki ya nufi office ɗin doctor Muhseen murya can ƙasa yayi sallama ya shiga murmushi ɗauke a fuskar doctor Muhseen yace”sannu da shigowa”.
“yauwa”.
Namijin duniya yafaɗa tare da zama kan kujerar dake kusa table ɗin Muhseen ya miƙamasa hannu suka gaisa bayan sun gaisa Doctor Muhseen ya ɗakko wata farar leda tare da miƙawa Namijin duniya ya ansa cikeda kulawa Doctor Muhseen yace”bara inɗakko maka water seka sha”.
“ohk”.
nanya ɗakko mishi ya buɗe drugs ya buɗe bottle yasha sannan ya miƙe yace”se anjuma”.
nan ya fita be jira amsar doctor Muhseen ba wani irin tausayin Namijin duniya ne yakama doctor Muhseen a hankali ya furta “Allah na sane dakai Abdallah insha Allahu Allah ze baka lafiya kamar ko wanne mutum”.
nanya nutsatsa yana tinanin Allah yabawa Namijin duniya komai amma Allah ya rageshi da wata babbar ƙaddara megirma yace”insha Allahu Abdallah zaka cinye wannan jarabawar”.
jiki a sanyaye ya cigaba da cike files ɗin dake gabansa.