THE WORLD MAN (NAMIJIN DUNIYA) COMPLETE NOVEL

“Ummah gaskiya ni nagaji da wannan ƙailular taki kinsanko irin san da nikewa mejan kunnenan kuwa da kika wani ƙi maida hankali kan zancen”.
“kefa Jameelah daɗina dake rashin haƙuri ki kwantar da hsnkalinki indai ina numfashi baki da wani mijin se mejan kunne domin yau ko gobe zansa Malam yasa Zaidu mejan kunne yazo gaidashi semu samu kafar saka maganin boka Tsula kai waye nafiki son kiyi aure gidan daula kodon inriƙa zuwa inaɗan yago abinkaiwa a bakin salati”.
“yanzu naji duka “.
“kedai abinda nike so dake kiɗanje ki wankemun ɗan wanke-waken can domin yau waccan tsinanniyar yarinyar batayiba ta tafi yawon tazubar ɗinta”.
ƙin tashi tayi dakyar ta tashi tana zumɓure-zumɓuren baki ta fita.
Ɓangaren Namijin duniya ko Doctor na gama gyarawa Inteesar ƙafa cikin yanayin caring Doctor Shahid yace”princess gaskiya kinada dauriya da watace da yanzu tana nan ta cika ɗakinnan da ɓararrako”.
wani sansanyan murmushi Inteesar tayimasa wanda yayi mugun tafiya da zuciyar Doctor Shahid tace”nagode”.
“ba godiya a tsakanin princess kedai kawai ki kula da shan maganinki insha Allahu nanda kwana uku zakiji ƙafar ta saki”.
yaƙarasa zancensa yana sakarmata wani shu’umin murmushi ,murmushin itama ta mayarmasa itama cikin siriyar muryarta dake tafiya da zuciyar ɗa namiji tace”insha Allah zankiyaye”.
wani ƙullutun baƙin cikinsu ne ya tokarewa Namijin duniya maƙogoro ganin yadda Inteesar keyiwa Doctor Shahid murmushi tsaki yayi a karo na uku sakamakon jin Doctor Shahid na niyyar ƙara jan Inteesar da hira murya aɗan daƙile cikin basarwa ya katse Doctor Shahid tare da cewa” Mallam kayi abinda ke gabanka”.
“sorry Sir”.
nan Doctor Shahid ya tsuke bakinsa saboda yana ɗagowa yaga Namijin duniya na jifansa da kallon kashiga taitayinka beƙara cewa da Inteesar komai ba ,ɓangaren Inteesar ko wani ƙullutun baƙin cikinsa taji tashiga itako metayiwa wannan mutumin da bayason yaga wani ya raɓeta bayason yaga wani yana nunamata kulawa tana farinciki tana cikin tinani taji muryarsa a ɗan daƙile yana cewa da Doctor”thanks”.
saurin dawowa tayi daga duniyar tinanin data tafi taji ƙamshinsa a gabda ita waigawa tayi taganshi befi saura taku biyu ya iso inda take ba saurin miƙewa tayi dukda zafin da ƙafarta kemata ta haɗe girar sama data ƙasa dan karya kaimata wargi tashiga aikamasa da harar wutsiyar ido tafara tafiya tana ɗingishi murmushin gefan baki yayi ganin yadda ta wani haɗe rai yabi bayanta yarigata zuwa gurin mota hakan yasashi yana isa ya buɗemata murfin motar har tayi niyyar wucewawarta taga idanun mutanen gurin gabaki ɗaya yadawo kansu hakan gefe guda kuma wata zuciyar tace mata”kishiga har yanzu kina ƙarƙashin ikonsa tunda baku tashi daka gurin aikiba”.
hakan yasata jiki a sanyaye ta shiga ya mayar ya rife ya zaga yashiga mazaunin driver yaja motar suka bar gurin yana fita daka get ɗin gurin ya cilla hancin motarsa titi ya ware a.c ɗin dake motar ya kunna karatun Alqur’ani megirma ƙira’ar Sudais tashiga tashi a cikin motar suratul Muhammad ba tare daya ƙara bi takanta ba yashiga bin ƙira’ar da daddaɗar muryarsa me daɗin sauraro .
Ɓangaren Inteesar ko juyar da kanta tayi tana kallon titi hakan datayine yabashi damar ƙarewa fuskarta kallo ɗan motsawa tayi hakan yasashi saurin ɗauke kansa daga gareta cikin nutsuwa yake tuƙi ganin hankalinsa ya karkata akan tuƙin taga ya nufi hanyar cikin gari da ita saurin kallonsa tayi gani tayi ya wani make kamar besan metake nufiba sosai ranta yakai ƙololuwar ɓaci da abubuwan da yikemata ta aro jarumta cikin tsiwa tace”Malam ajeni anan”.
yi yayi kamar badashi take ba hakan daya yimata baƙaramin ƙara tunzurata yayiba a harzuƙe tace”Malam ka ajeni anan”.
ƙara banza da ita yayi hakan yasa takai hannu cikin ɓacin rai zata murɗa handle ɗin motar kafin taƙarasa taji ƙarar sa lock ɗinsa hakan yasa ta koma ta zauna tare da jingina da jikin kujerar ta lumshe oily eyes ɗinta cikin kwanciyar hankali ya cigaba da tafiyarsa harya isa wani tanƙamemen mall mesuna MAN OF THE WORLD SHOPPING MALL da manyan baƙi ƙarasa shiga gurin yayi tare da yin parking a tanƙamemen parking space ɗin gurin yana daidaita parking ɗinsa yaɗan saci kallonta gani yayi har bacci ya ɗauketa a haka jiyayi wani murmushin dabe shirya yinsa ba ya kuɓucemasa ganin yadda ta duƙunƙune ne yasashi gane a.c tayimata yawa yaɗan ragemata haɗe da kwantar mata da kujerar ya gyaramata kwanciyarta ya buɗe ya fita tare dasa lock ta waje ya nufi cikin gurin bejima da shiga ba yafito bayansa da masu aiki a gurin sanye da riguna da kaya niƙi-niƙi a bayansa danna key ɗin motar yayi har zasu zuba a boot ya dakatar dasu yayimusu nuni da gidan baya cikin girmamawa suka zuba yashiga motar yaja seda sukayi tafiya me nisa rasa hanyar dazebi yakaita gidane yasashi juyawa ya kalli inda take gani yayi ta tashi taɓe baki yayi haɗe da cewa”ina zankaiki”.
ba tare data kalli inda yike ba tace”Suleja amma a titi zan sauka”.
ba tare daya tankamata ba ya juyar da kansa ya cigaba da tuƙinsa cikin kwanciyar hankali yaƙara volume yashiga bin karatun Alqur’ani taɓe baki tayi a zuciyarta tace”ashe su wa’eeh an iya abun mutane”.
jin muryarsa tayi kamar a mafarki yace”keeeh dawa kike”.
se lokacin tagane a fili tayi maganar tsuke bakinta tayi har suka isa bakin titi kamar yadda tace dashi yayi parking gefan titi ba tare daya kalleta ba yasa hannu ya jawo ɗaya daka cikin ledojin da yasa aka saka a baya ya buɗa ya fito da wasu rantsatsun abayas masu ɗaukar hankali ya zaro ɗaya daga ciki ya buɗa ba tare daya kalleta ba yace”daka yau wa’innan kayan zaki riƙa sawa da safarsu da niƙab ɗinsu dan bazan lamunci saka wannan banzan gyalen da kikeyi ba domin Comphany ɗina ba gurin nanaye bane da mutum zaki riƙa saka wa’innan fugaggun gyaluluwan naki masu kama da matacin koko a ciki akwai hijabs kowanne kowanne kaya da kalar niƙab ɗinsa da hijab ɗinsa su zaki riƙa sawa”.
wata dariyar rainin hankali tayimasa tare da taɓe baki ta aro jarumta tace”waikai meyasa kake son takurawa rayuwata ne sekace wani mijina ina ruwanka da kayana kuma da kake cewa gyalena kamar matacin koko meye naka a ciki naga tundaka gidanmu nasawo kayana meyasa su basu yimun maganaba sekai kuma kai bakaga irin shigar da Sakatariyarka take ba se tawa saboda ni kaɗai ka tsana to bazan dena sawa ba banason kayan kakaiwa matarka tasa domin ni a ganina ita zakaiwa wannan kullen baniba”.
taƙarasa zancensa tare da ture rigar daka jikinta cikin isa yace”ke wacece da zanyimiki kyauta ki mayarmu dame kike taƙama baki isa kin karyamun record ba dole ki ansa”.
wani kallon tara saura kwata tayimasa cikin tsiwa tace”mutum ce kamarka kai waye da baza’ah mayarmaka ba masha Allah kaga seka aje record akaina anyi rejecting ɗin kyautarka domin ni wallahu bazan ansa ba ka adana zasu yimaka amfani gun matarka”.
taƙarasa zancen tare da saurin murɗa handle ɗin ƙofar cikin sa’ah tajishi a buɗe tayi saurin fita ganin ya kawo hannunsa da niyyar cafkota tafice cikin sauri dukda tanajin zafin ciwon da ƙafarta ke mata karo na farko a rayuwarshi daya yi murmushi dukda rashin kunyar data tayimasa beja motar ba har seda yaga ta tsallaka titi tahau napep sannan ya tada motarsa yabar gurin a guje.