NAMIJIN DUNIYA COMPLETE NOVELTHE WORLD MAN COMPLETE NOVEL

THE WORLD MAN (NAMIJIN DUNIYA) COMPLETE NOVEL

8:30pm
Tsaye yake a ƙofar gidansu yanata dialing number ta amma amsar ɗaya switch off sosai hankalinsa yayi mugun tashi ɗaga kannan da zeyi yaga Hauwah ta fito daka gidansu tunkaro inda yike tsaye sosai yaji wani irin sanyi ya ziyarci zuciyarsa bakinta ɗauke da sallama taƙarasa murmushin daya ƙara masa kyau yayimata cikin girmamawa Hauwah tace”Uncle Zaid anyini lafiya”.
“inafa lafiya banji zuciyata ba ina zakijini naga ta lafiya”.
sosai Hauwah daɗin kalamansa akan ƙawarta nanta labartamasa duk abinda yafaru a iya yadda tasani sosai hankalinsa ya tashi sosai takejin daɗin yadda yake caring ɗin ƙawarta tace “Uncle ka kwantar da hankalinka bara inshiga insanar musu seka shiga ka ga jikinta”.
“aiko da kin temakeni domin bakiji yadda hankalina yayi mugun tashiba dukda kin faɗamun amma hankalina yaƙi kwanciya in naganta hankalina yafi kwanciya”.
“tom bara naje”.
nanta shiga .

A tsakar gida tasamu Abbah da Uwar Gwarama zaune Abbah yana cin tuwo Uwar Gwarama tana ƙuƙula magungunan mata da take siyarwa abinka dame sana’ah goma maganin me gasa ƙarasawa tayi inda suke cikin girmamawa tace”Abbah sannunku da hutawa”.
“yauwa Hauwah ya mutanen gidan naku”.
“lafiya ƙlau Abbah dama Zaid ne yazo zamuje gidansu shine nike faɗamasa Inteesar ɗin batada lafiya ……”.
bata ƙarasa abinda take son cewa ba cikin zalama Abbah ya tari numfashinta da cewa “meyasa to baki ce yashigo ciki yagaida itaba aida kince ya shigo aishima yanzu yazama ɗan gida ko Tsahare”.
tsilum Uwar gwarama tace”aiko dai Malam”.
jin abinda Uwar Gwarama tace sosai yabawa Hauwah mamaki tace”ai Abbah nacemasa bara inyimasa iso yashigo”.
“toh! toh!! toh!!! kin kyauta ki sanar dasu suɗan gyatta seki shigo dashi”.
“toh”.
nanta nufi ɗakinsu Inteesar zaune tasamesu Khadijat na karantawa Inteesar wani littafin Real eeshow mesuna ZANJIRATA sosai suke jin daɗin littafin domin yana kaimusu Umman su kuma tana kan sallaya tana lazumi hararsu Hauwah tayi tace”yanzu nan saboda rashin mutunci shine kuka cigaba da karantawa koku kirani inason jin yadda zata kaya tsakanin Amatujjabar da Yayah Mahmud saboda dramar su nakaimun “.
“ya haƙuri Aunty Hauwah zan karantamiki kema seda nace tabari kizo taƙi kinsan Aunty da gauƙa yanzu ma kuma muka fara”.
“toh ƴar ƙanwata takaina “.
taƙarasa zamcenta ta nufar gurin Ummah duƙawa tayi ta sanar da ita zuwan Zaid sannan tasa suka ɗan kintsa dukda ɗakinsu fes-fes yike basu da lalaci nanta fita tashigo dashi.

Uwar Gwarama na ganin fitar Hauwah ta kalli Abbah daketa sukurkuta lomar tuwo yana santi tace”Malam bara inɗanje inɗan kunna turaren wuta sirikinmu bayazo yanaɗan jin bashi -bashi ba kadai sanni da iya karramar baƙo bare kuma babban sirikinmu”.
“aiko dai da kin kyauta”.
wani shu’umin murmushi tayi ta wuce ɗakinta tana shiga ta iske Jameelah tana waya da saurayinta cikin azama tace”ke banza kina nan kina shashsnci Allah yakawo mana dama Zaidu yanzu ze shigo ya duba waccan tsinau ɗin ki tashi ki ɗebo rushi kizuba magain nan”.
tsalle Jamilah ta buga tare da miƙewa cikin jin daɗi tace”I love you Mamah na maganin kukana”.
ta fice cikin sauri murmushi Uwar Gwarama tayi ta tafi ta ɗakko maganin da boka yabata ta fito waje a tsakar gida suka haɗu da Jameelah ta ebo wuta a marfin langa nanta jiki na rawa ansa Uwar Gwarama tayi tana murmushi tace”yimaza kije kiɗan kintsa jikinki karya ganki kamar wata ƴar jaka”.
“toh”.
nanta wuce ita kuma ta buɗe maganin ta zuba .

Zaid na shigowa ƙamshin turarennan ya bugu hancinsa lokaci ɗaya yaji kansa yashiga saramasa dakyar yake iya ɗaga ƙafa yake tafiya har suka isa!!!!!!!!

Votes and Comments
Plz share to others

_*Daga Alƙalamun ???? *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)

MALLAKIN
REAL EESHOW

HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…

BOOK 1

PAGES 2️⃣9️⃣➡️3️⃣0️⃣

      Inda Abbah ke zaune yaƙarasa tare da zama kan sallayar da aka shimfiɗamasa ya zauna cikin girmamawa yace"Abbah ina yini".

“lafiya ƙlau ya wajen iyayen naka”.
“lafiya ƙlau Abbah suncema suna gaisheku”.
“masha Allah Hauwah yimasa jagora zuwa gurin mejikin”.
“toh Abbah”.
taƙarasa faɗa tana kallon Zaid da bashi da niyyar miƙewa ɓangaren Zaid ko ji yayi duk bayako son ganinta daurewa yayi ya miƙe da nufin bin bayasan sukaji muryar Uwar Gwarama dake fitowa daka ɗaki cikin shiga ta alfarma jiki na rawa Zaid yayi saurin duƙawa yace”Ummah ina yini”.
ganin yadda jikinsa yaketa faman tsuma baƙaramun daɗi taji ba a zuciyarta tace”kai gaskiya Boka Tsula aikinka na kyau jibi yadda jikin wannan shu’umin yaron daya wulaƙantani yaketa faman karkarwa kamar mazari kaɗanma kagani ɗan shegiya zaka kwashi kashinka a hannu domin seka gane shayi ruwa ne seka zama tamkar raƙumi da akala domin Jameelah se yanda tayi dakai badai kai ƙaramin tsageraba hadda wani cewa dani ni Inteesar nike itakuma har wani gwalli takeyi wai ita zatayi aure gidan jindaɗi maga yadda za’ayi ayi auren matsawar ina numfashi bazan taɓa barin ɗiyar Aminah taji daɗin duniya ba kamar yadda na hanasu jin daɗin gidannan haka bazan taɓa barinku kuji daɗin gidan mijiba sede ku ƙare a bauta matsawar ina numfashi “.
katsemata zancen zucin da takeyi Zaid yayi murya na rawa yakuma cewa”Ummah ina yini”.
wani gauron numfashi ta sauke haɗe da dawowa daga duniyar tinanin data lula tace”lafiya ƙlau yaron kirki ya wajen magabatan naka”.
baki har ɓari yikeyi yace”lafiya ƙlau Ummah sunama gaisheku”,.
a wani yatsune Uwar Gwarama tace”muna amsawa ɗiyar kirki ƴan makaranta kifito ga yayanku yazo ku gaisa ko duk hadda ce har yanzu kiriƙa barin kwakwalwarki ta huta dan Allah darenma ace mutum baze hutaba sekace al’huda-al’huda aikya fito ku gaisa inyaso seki koma kicigaba da karatun”.
Jameelah dake ɗaki tana chart ɗinta da saurayinta ce tayi gyaran murya alamun bata kai ayaba ta cigaba da danna wayarta bayan 5mins cikin fi’ili tayi kabbara sannan ta miƙe taƙara feshe ko ina na jikinta da turare sannan ta gyara zaman hijab ɗinta tashiga tafiya cikin yanayin ɗaukat hankali.

Ganin yadda jikin Zaid keta faman ɓari baƙaramun mamaki hakan yaba Hauwah ganin yadda bakinsa har rawa yike gurin gaida Uwar Gwarama tinani tashiga yi a zuciyarta tashiga tinanin ita a iya saninta Zaid baya shiri da Uwar Gwarama to kuma meyasa taga jikinsa har ɓari yikeyi kanta rasa wanda zebaa amsa ne yasata tsuke bakinta tana mamakin iyayi irin na Uwar Gwaramaa zuciyarta tace”hmmm iska na wahal dame kayam kara ko a ina Jameelah ta taɓa shiga class oho Allah dai yasa ba wata kitumurmurar suka haɗa ba”.
tana cikin wannan zancen zucin taji ƙamshin turaren Jameelah ya bigi hancinta saurin ɗagowa tayi caraf sukayi ido huɗu da Jameelah daketa faman zuba ƙamshi tasha kwalliya kamar wadda zata gasar kyau baƙaramun ɗaurewa kanta yaƙara yiba da mamakin abinda take gani ganin abun take kamar almara wata uwar harara Jameelah ta bankamata suna haɗa ido da Zaid tasakarmasa da wani narkakken murmushi wanda yasashi suman wucin gadi lokaci ɗaya yaji wani mugun sonta na fisgarsa jiyike duk duniya bashida wani abu da yikeso kamarta martanin murmushin data yimasa ya mayarmata wani sanyine ya ratsa zuciyarta inda takejin wata muguwar ƙaunarshi na ƙara ninkuwa a cikin zuciyarta jitake kamar taje ta rungumesa haka takeji .

Uwar Gwarama ce ta kalli Zaid cikin iyayi tace”kaganta nan Zaidu kullum aikin kenan daka hadda se zuwa makaranta koda yike tafi masu rataya jaka kullum kamar wanzamai aje can aje nan duk wani lungu na garinnan inkabi seka gansu kamar wa’inda akaimusu hakika da kare shiyasa ƙilama shiyasa aka rasa mashinshini”.
murmushi Zaid yayi yace”masha Allah sister yanzu izunki nawa”.
farr Jameelah tayi da mitsi-mitsin idanunta da suka ƙara narkar da Zaid cikin ƙaunarta zatayi magana kenan caraf Uwar Gwarama tace”hmm ai dake tayi sauka Hafizah ce bakaga yadda ƴan unguwa suke zuwa ɗaukar karatu gurinta ba”.
“wow masha Allah ashe ƙanwar tawa Malama ce kenan a daɗa bada himma watarana zakiga amfanin abun “.
“insha Allah Yayah”.
Hauwah dake gefensu dakyar ta tare dariyar data kusa kuɓucemata tace”muje Uncle Zaid kaga me jikin”.
taƙarasa maganarta tana niyyar yin dariya sauke numfashi Zaid yayi danshi har yama manta da abinda ya kawosa lokaci ɗaya yaji wani irin abu yazo ya tsayamasa a zuciyarsa jiyike kamar ya zura da gudu saboda yadda kansa ke mugun saramasa dakyar ya yaƙi zuciyarsa gurin cewa”ok muje”.
nan tayi gaba yabi bayanta ɓangaren Hauwah ko baƙaramun mamakin su Uwar Gwarama take ba tana wannan tinanin har suka isa ɗakinsu Inteesar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button