THE WORLD MAN (NAMIJIN DUNIYA) COMPLETE NOVEL

Suna shiga yaji kansa ya daɗa juyewa yanajin wata irin muguwar tsanarta na shigarsa a zuciyarsa yanajin inda za’ah bashi wuƙa a lokacin ace ya kashe maƙiyinsa to ba makawa Inteesar ze kashe dakyar ya yaƙi zuciyarsa ya duƙa yagaida Umminsu Inteesar ba yabo ba fallasa ya gaidata Khadijah tagaidashi a ciki-ciki ya amsa cike da mamakin yadda taji ya amsa gaisuwar Khadijat ta ɗago idanunta ta kalleshi gani tayi yana bin ko ina na ɗakin da kallon ƙasƙanci da zallar tsana gami da kyama sosai abun yashiga bata mamaki tana cikin mamakin abinda idonta ke ganemata taji muryar Umminsu tace”Khadijah kawomasa ruwa”.
cikin yatsuna yace”a’ah nagode Ummih”.
murmushin manya Ummih tayi suka fice suka barsu ragewa gurin yayi daka Inteesar seshi a hankali ta miƙe tana tunkaro inda yike abun mamaki setaga ya miƙe zumbur kamar wanda aka tsireshi da allura ya miƙe yana toshe hanci ya fice waje da sauri dube-dube tashiga yi taga ko ina tsaf yike na ɗakin ba abinda ɗakinsu yike se ƙamshin turare a zuciyarta ta tambayi kanta”to meyasa yake toshe hanci kamar wanda yakejin wari”.
rasa me bata amsa ne yasa wata zuciyar cemata “ƙila ƙamshin turaren ne bemasa ba to amma kuma meyasa yake binmu da irin kallon danaga yana binmu dashi “.
rasa me bata amsa ne yasata saurin bin bayansa.
Ɓangaren Zaid ko yana fita ya saki wata nannauyar ajiyar zuciya lokaci ɗaya yaji wata fresh air na shigarsa ya nufi gurin dasu Abbah ke zaune cikin girmamawa ya duƙa a gaban Abbah yace”Abbah ga wannan a siyawa me jiki magani”.
washe haƙora Abbah yayi irin na zalamammun iyaye masu tsananin son abun duniya yace”toh!toh!! toh!!! angode Malam Zaidu kaidai baka gajiya da abun arziƙi angode Allah ya saka da Alkhairi”.
“Ameen Abbah ni zan wuce sauri nike”.
“toh madallah ka gaida magabatan naka”.
“toh zasuji”.
yaƙarasa faɗa yana duben ta inda zeganta caraf suka haɗa ido da Jameelah dake ɗauke da tray a hannunta cikin karairaya take tafiya harta isa gabansa ta aje tray ɗin dake hannunta haɗe da waro mitsi-mitsin idanunta tace”badai Yayah har zaka tafi ba”.
“eh Sis sauri nikeyi meeting ɗin gaggawa ne ya tasomun”.
“okay to amma dai ko jus ɗin kasha dai”.
“anya Sis sauri nike kibari watarana nasha”.
kukan shagwaɓa Jameelah tashigayi harta buga ƙafa hakan baƙaramun ƙara burge Zaid yayiba yaƙara lula cikin duniyar ƙaunarta yace”sorry Sis bani insha”.
“yauwa Yayana”.
nanta zubamasa yasha baƙaramun ɗaurewa kan kowa na gurin yayi Uwar Gwarama tana haɗa ido da Jameelah ta ɗagamata hannu alamun aikinta na kyau nan yayimusu sallama kota kan Inteesar dayaga tana tahowa bebiba ya fice da sauri saurin bin bayansa tayi amma me tana zuwa yana barin gurin a guje ko kulata beyiba zubewa tayi a gurin tare da fashewa da wani marayan kuka jitayi an dafata tabaya hakan yasata saurin goge hawayenta tayi saurin ɓoye damuwarta tayi ta juya haɗe da cewa”Besty tinanin yadda za’ayi gobe nike narasa meza’ah tarbi ƴan kawo kayannan dashi”.
“shine kuma zaki duƙa kamar wadda wani abun ke damunta kodai ƙafar ce ta motsa muje nagama tsara abubuwan da zamu siyo semuyi snacks da drinks se chickens ina ganin ya isa”.
“eh ya isa ammafa ni a hannuna befi 6k ba ina tinanin har su sai lemo susai chicken ga uwa uba snacks”.
“muje inada kuɗi a account ɗina semuyi amfani dashi”.
“toh ke bakida amfanin da zakiyi dasu da zaki ce ga wasu a gurinki”.
“ai Besty ko inada amfanin da zanyi dashi na fasa meye ranar inada shi ban temakekiba ai abun bemun rana ba haba Besty a tinanina in inada abu tamkar kema kinada shine muje dan Allah musan abunyi”.
“hakane kam Besty nagode Allah ya saka da Alkhairi yabarmu tare”.
harar wasa Hauwah tayimata haɗe da cewa”ameen Bestyna Allah ya shiryeki Bestyna inban miki ba wazan yiwa”.
“Ameen dai Besty”.
nansuka shiga dan tsara abubuwan da zasuyi domin tarbar ƴan kawo kaya.
Zaune suke a gaban Boka sun gama zayyanemasa duk abinda ke faruwa tsakanin Inteesar da Man of the world wata uwar dariya Boka Kutsugu yayi lokaci ɗaya ya haɗe rai tare da cewa”tunkafin kuzo nan nasan da zuwanku wannan yarinyar da kuke gani ba’ah zaune take haka kawai ba domin yarinyar nan da kuke gani ba ƙaramar hatsabibiya bace dole sekinyi da gaske sannan zaki kamota”.
“kinji ko dama na faɗamiki yarinyar nan baƙaramar hatsabibiya bace dama ni ina ganinta nasan ba haka nan take zaune ba “.
“Boka yanzu ayi duk yadda za’ayi a cire yarinyar nan ta fita daka zuciyarsa asamasa soyayyata a zuciyarsa”.
wata uwar dariya Boka kutsugu yaƙara kecewa a karo na biyu yaƙara haɗe rai ya ɗaga hannu sega wani abu ya bayyana duk jini a jikinsa me kama da zuciya yana hurawa ya miƙawa Feenerh irin ɗari-ɗarinnan ta riƙa yi da kyankyami ta ansa a yaƙune wai ita me kyankyami aiko garin yaƙuna abu ta sille tafaɗi batt ba aba ba labarinta dariya Bokan yaƙara yi haɗe da cewa”kinga wannan abar dana baki da kin cinyeta da shikenan kigama da wani Abdallah domin zuciyarsa gabaki ɗaya na ciro na baki kika wulaƙanta”.
dafe ƙirji Feenerh tayi cikin kiɗima tace”kayi haƙuri Boka bansan zuciyarsa bace aida tini na cinyeta dukko da jinin da yike jikinta yanzu ka ƙara bani wata zan cinye yanzu yanzunnan”.
“hhh ai aikin gama yarinya ya gama bakin alƙalami ya bushe sau ɗaya muke bada zuciyar ga mutum saura magani na biyu idan kinsamo aikinki zeyi kyau”.
wani daɗine ya mamaye zuciyar Zuby ganin aminiyarta tayi loosing ɗin Man of the world hankali tashe Feenerh tace”yanzu Boka ba yadda za’ayi abani zuciyar yanzu kenan”.
“babu zancen zuciya yanzu sede kije ki samo hantar ɓauna kuma ki tabbatar da kanki kika soketa ki yanko da ita za’ai mahaɗin maganin”.
a gigice Feenerh tace”hantar ɓauna kuma Boka nashigesu ni Nafi ina zansamu wata hantar ɓauna kuma”.
wani daɗine yaƙara kama Zuby a zuciyarta tanata farinciki a fili ko ta nunawa tayi kamar tana alhinin abinda ke damun Feenerh murya na rawa Feenerh tace”Boka to meze hana nabaka kuɗi a samo hantar ɓaunar ko nawa kake so a shirye nike dana kashe ko nawane matsawar nidai buƙatata zata biya “.
“hhh ke zaki samo da kanki inba haka ba maganin bazeyi aiki ba dole da kanki zaki nemo”.
“toh zan gwada samowa”.
“yauwa ammafa karki kuskure kisa wani ya samomiki akwai matsala gagaruma akan hakan kome yaje ya dawo ki kuka da kanki”.
“bama zansa kowa ya samo ba da kaina zansamo”.
“yadaifimiki idan kin samo kin kawo dashi zan haɗa miki magani “.
“toh”.
nansuka miƙe Feenerh ta aje kuɗin dake hannunta suka fita suka tafi ɗan warewa gefe sukayi da Zuby tace”aiko Ummah dole nakomo gobe ni yabani zuciyar na cinye sede taji a salansa domin idan nasamu shiga gurin Namijin duniya nunawa zanyi bansanta ba wallahi zan koyawa yarinyar nan hankali seta gane shayi ruwa ne ai Ummah naji daɗi da bata ci zuciyar ba wallahi”.
“kibari mukoma gida karta jimu”.
“toh”.
nan suka tsuke bakinsu suka cigaba da tafiya.
Washe gari tunda ta tashi da asuba bata komaba kamar yadda tasa ba kullum ta share gidan tass tayi wanke-wanke tana gamawa ta nufi gidansu Hauwah!!!!!!!
Votes and Comments
Plz share to others
Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.ƴar Mut???? MAN OF THE WORLD
(NAMIJIN DUNIYA)
MALLAKIN
REAL EESHOW
HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…
BOOK 1
PAGES 3️⃣1️⃣➡️3️⃣2️⃣
Tana cikin tafiya taji muryar Jameelah daka bayanta tana cewa"Aunty Inteesar nima zanbiki ayi aikin dani".
juyawa inda take Inteesar tayi zatayi magsna cikin tsiwa taji Khadijah tace”bama gayya a ƙara gaba ke bama kiji kunyar cewa zaki bita ba saboda ke ɓera ce karfa ki manta itace wadda kuka tsana ɗinnan kuka hanata sakat a rayuwa wadda bakwason ganin cigabanta itacefa wannan karuwar da kuke cewa wadda kuke cewa bawani karatu se yawon tazubar duk wannan be isheku ba saboda ke ɓeran masallacci ce ba kunya bare tsoron Allah kika wani yayimo wani tsumma jikinki wai zaki bita to ba inda zakije bama gayya umma tagaida Ashsha ki ƙara gaba hanyar jirgu daban ta mota daban kuma karki ƙara kiran yayata da Aunty kije can ki nemi Aunty a can badai nanba”.
juyawa Jameelah tayi jiki ba kwari saurin kamo hannun ta Inteesar tayi tace”rabu da ita Jameelah kizo muje kekuma banason iskancin banza ko ke tace zatabi da zaki wani sakawa mutane baki taho mutafi bakomai sister”.
“nagode Aunty Intee”.
“bakomai sister”.
“ai gaskiya ce dole infaɗamiki maƙiyinka har abada maƙiyinka ne ko ya zo ya nuna yanasonka ƙarya yike kullum bashi da burin daya wuce yaga bayanka shine saboda ke damo ce sarkin haƙuri mutum yagama takaki yadda ransa yikeso yazo kuma ya shigemiki ki ansheshi lokaci ɗaya ba dolema mutum gobema yaji daɗin hayemiki ba ai yaci ace ki nunamata kurenta koda zaki ansheta”.
wata uwar harara Inteesar ta bankawa Khadijah ta kama hannun Jameelah suka shige gidansu Hauwah suka barta nan tsaye baki buɗe ta wuce cikin gida tanata masifa.