NAMIJIN DUNIYA COMPLETE NOVELTHE WORLD MAN COMPLETE NOVEL

THE WORLD MAN (NAMIJIN DUNIYA) COMPLETE NOVEL

Suna shiga suka samu su Hauwah dasu Momynta sun kammala aikin snacks ɗin har sun fara celling ɗinsu da raping sheet turus tayi haɗe da kama haɓa ta ware fararen sexy eyes ɗinta tace”badai har kun gamaba Momy”.
hararta Hauwah tayi tace”da jiranki zamu tsaya yi ne alanƙosa aida mun tsaya jiranki da ƙila sede muji kunya domin ke ɗinnan yadda kike da nawa ina tinanin a gidanki Uncle Zaid zesha fama dake”.
damm ƙirjin Jameelah yabayar sakamakon tinowa datayi yau za’ah kawo lefen Zaid da wata bada itaba har yau be kirata ya sanarmata da yanason ta ba tana cikin wannan tinanin taji muryar Inteesar cikin shagwaɓa tace”Momy kinji Hauwah tana cemun wai alanƙosa”.
murmushi Momy tayi tace”rabu da ita ƴar albarkana itace alanƙosa domin itama yanzunnan fitowarta kenan ta zauna ba abinda takeyi se aikin ci daka ni se Hindatu mukayi aikin komai kuma ma inban dage na fitar da ɗiyata kunya ba wazan fitar rabu da ita”.
gwalo Inteesar tayiwa Hauwah haɗe da cewa”muje Jameelah”.
“toh Aunty”.
nan suka tafi sosai su Momyn Hauwah suka yi mamakin ganin Inteesar da Jameelah amma sesuka make zama suka yi suka tayasu raping ɗin kayan suna gamawa Inteesar tace”Jameelah ki iba ki ɗanɗana”.
“toh Aunty”.
nanta ɗauki komai ɗaya taci itama Inteesar ta ɗauka ta ɗanɗana suka taya Hindu me aiki kai kayan cikin gida bayan sun gama kamar gaske Jameelah tace”Aunty bara naje gida na shirya tunda naga har angama aikinma”.
“toh sis”.
nanta fita sukuma suka nufi ɗakin Hauwah suna shiga suka zauna kan ɗan madaidaicin gadon Hauwah taɓa Inteesar Hauwah tayi tace”wai Besty ya akai naganki da wannan yarinyar ne”.
“wacce yarinya fa”.
“hmm gaskiya Besty rainin hankalinki yawa ne dashi wacce yarinya nike nufi bayan Jameelah naga yarinyar nan ba wadda ta tsana sama dake kika wani jawomana ita ke bakya tinanin ko turota akayi dantaga abinda mukeyi ba”.
“hmm keda Khadijah kuna bani mamaki wallahi na taho zanzo nan gidan yarinya tacemun zata bini so kuke na koreta shi ɗan adam ba’ah masa haka bakasan ranar da zemaka ba shi ɗan adam rana garesa ko biki taɓa karanta littafin marubuciyar nan ba Real eeshow mesuna BAR RAINA ALLURA (Itama ƙarfe ce) labarin ya ƙayatar dani sosai saboda marubuciyar ta nuna duk yadda mutum yakai da ƙinka a rayauwa be isa ya hanaka samun rabonka ba duk ƴinshi dakai ita rayuwa haka take zakaga kaƙi mutum ƙarshe shiɗin dai daka raina gaba shize temakeka gaskiya zan turomiki da littafin ki karanta zaki faɗakantu sosai labarin Sajida duniya ne”.
“eh dai naji amma kinsan wani abu idan kika cigaba da wannan haƙurin naki mutane zasuyita cutarki saboda yarinyar nan da uwarta inda za’ah basu wuƙa ace su kashe wani abu da suka tsana wallahi ke zasu kashe nifa na tsanesu wallahi”.
“dan Allah mubar wannan zancen batashi nike ba tin jiya narasa gane kan Zaid tunda yabar gidanmu na kirashi ya ɗaga ko magana be bari nayi ba yacemun wai aiki yikeyi idan yagama ze kirani shiru-shiru inata jira ya kirani be kirani ba dana daɗa kiranshi be ɗauka ba har zuwa yau idan na kirashi baya ɗauka na biki yadda nikejin zuciyata ba na riga na saba da waya dashi wallahi jiya se wajen huɗu bacci ya ɗaukeni hankalina har yanzu yaƙi kwanciya wallahi”.
dariya Hauwah tayi ta kama baki tace”oh su Besty anyi nisa ba’ah jin kira wannan irin ƙauna haka harda ƙinyin bacci lallai Uncle ɗina ya iya love irin wannan mutuwa haka da kikayi kansa haka sefa kina mishi uzuri tunda kinsansu masu kuɗinnan sunada sabgogi a gabansu bare kuma satin biki yakama dole sekinmasa uzuri romeo”.
“eh najin inban damu da mijin dazan aura ba wa kikeso na damu dashi amma aida baya iya bacci har seya yimun addu’ah na kwanta sannan muke sallama a waya shiyasa jiya nakasa bacci”.
“hhh dole Besty ki kasa bacci tunda yariga yagama shagwaɓaki dole kice kinkasa bacci niko Allah muntuba aini gani nike ba’ah yo mutumin dazan kasa bacci ba dominsa ba gaskiya”.
“hmm haka dai kikace dandai har yau baki haɗu da wanda kike so bane shiyasa wayasanma ke me zaki gwarama ni anga nawa”.
“hhhh”.
nan suka cigaba da hirasu da ƴan tsare-tsaren ansar kaya.

Kwance yake akan tamfatsetsen italian bed ɗinsa idanunsa a lumshe kamar me bacci tsaki yayi haɗe da buɗe sexy eyes ɗinsa yace”anya ko wannan yarinyar ba mayya bace ba kuwa meyasa dana rife ido ba abinda nike gani se ita gaskiya inko ba mayya bace ƙila ta haɗa iri dasu take ƙoƙarin cinyeni koma dai menene Allah yafiki stupid kawai”.
ƙara sakin wani tsakin yayi yaƙara lumshe idanunsa nanma still ba abinda yike gani se ita tsaki yaƙara yi yaji an turo ƙofa anshigo wasu english wears ne jikinta wando da riga wandon iyakarsa guiwarta jeans baƙi se rigar sky blue me ratsin net daka gurin ƙirjin baƙaramin kama jikinta kayan sukayi ba tasha uban kitson atarch har ɗuwawu tana tafiya ko ina na jikinta na motsawa hannunta ɗauke da cup ɗin coffe jikin drawer ta nufa da niyyar aje coffeen dake hannunta caraf idanunta ya sauka kan faffaɗan ƙirjin Abdallah dake cike da gashi irin na jaruman maza masu ji da class se ɗaukar ido gashin keyi shedar yana shan gyara tana ajewa ta juya idanunta ya rife ta kai hannu da niyyar taɓawa taji ya dakamata tsawa haɗe da cewa”ke wacece irin tinkiya ce mara tarbiyya waya baki izinin shigomin part da har kika wuce falo kika shigomin bedroom with out my permission dakin bari wannan ƙazamun hannun naki ya taɓamun jiki da sekin raina kanki domin wallahi da sena nunamiki true colour ɗina “.
sosai yayimata kwarjini lokaci ɗaya ta diririce murya na rawa tace”dama Yah Abdallah coffee na haɗomaka”.
batare daya buɗe sexy eyes ɗinsa ba yace”nacemiki ina buƙata ne da zaki shigowa mutane bedroom bako sallama saboda rashin hankali ko da ke kike bani coffee ɗin ko ancemiki ni inashan coffee ɗin kowanne tom and jerry ne irinki kinfice da tsiyarki kinbani guri ko sena tashi stupid kawai mara aji”.
saurin ɗaukar coffen ta tayi jiki na rawa ta fice tana fita yayi tsaki ya miƙe tare ɗaura towel ya nufi toilet.

4:00pm
Hauwah na shirin shiga gidansu Inteesar wasu haɗaɗun motoci guda huɗu suka yi parking biyu hilux biyu Parado baƙaƙe se ɗaukar ido suke parking suka yi daidai ƙofar gidansu Inteesar wasu haɗaɗun matane dattijai wanda bazasu gaza shekaru 50 ba suka fito daka mota ɗaya su biyu amma inkagansu seka ɗauka ƴan shekaru talatin da biyar ne saboda yadda jikinsu ya nuna kana ganinsu kasan sun jiƙu da naira ɗaya motar kuma wasu matane su huɗu matasa masu jini a jika suka fito masu tsananin kama da Zaid musamman ma ƙaramar cikinsu sauran hilux ɗin biyu kuma shaƙe suke da akwatuna wani daɗine yakama Hauwah ta nufi inda suke cikin girmamawa tace”Ina yininku”.
“lafiya ƙlau badai kishiyar tawa bace daiko data kwacen miji na bace ko” .
cewar ɗaya daga cikin dattijan dariya Hauwah tayi tace”Babah ba ita bace ƴar uwarta ce ita tana can gidan”.
tafaɗa ta me nuni da gidansu sosai taji daɗin jin wannan kalaman daka bakin wannan matar hakan ne yaƙara tabbatarmata da dangin Zaid suna son aminiyartata nan tayimusu jagora zuwa cikin gidan ɗaya daga cikin matasan matannan ce tace”amma dai sister zaki kaimu inda amaryar tamu take ko”.
“insha Allah zankaiku”.
“yauwa Jabeer ku shishigo da kayan “.
“toh ranki shidaɗe”.
cewar Jabeer nan suka shige gidansu Inteesar .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button