THE WORLD MAN (NAMIJIN DUNIYA) COMPLETE NOVEL

Washe gari tin bakwai su Inteesar sukaje Comphany ɗin Namijin duniya amma har yamma ba’ah yimusuba sedaka baya sannan aka yiwa Hauwa’uh Inteesar na shiga suka miƙe Adam ya kalleta tare da cewa”Madam muntashi sede gobe ki dawo da wuri”.
ko kallonshi Inteesar batayiba cikin ɓacin rai tace”Hauwa’uh mutafi”.
“toh mungode ranka shidaɗe”.
Hauwa’uh batayi aune ba se ganin Inteesar tayi fuuu tayi waje kamar zata tashi sama kallon-kallon suka shigayi Ahmad yace”saura step two da alama wannan ya amsu”.
“amma Ahmad baka ganin a zuciya irin ta wannan yarinyar zata iya ƙin zuwa gobe”.
“hmm bazataƙi zuwaba saboda ninacemaka wannan Adam saboda da wannan aikin zasu dogara kagako dolenta tazo”.
“hakane amma wannan mugune yasan kan tsiyar “.
namijin duniya dai becemusu komaiba nan suka tafi.
A bakin titi Hauwa’uh tasamu Inteesar tsaye murmushi Hauwa’uh tayi ganin Inteesar ta haɗe girar sama data ƙasa dafata tayi kaɓar da hannun Hauwa’uh Inteesar tayi tare da cewa”bazan ƙara zuwa ba Allah haka kurum inzo inda za’ah yita wulaƙantani Allah be wulaƙantaniba se wani banza can wanda tarbiyyama cikakka bashi da ita”.
“haba Inteesar kinsan dai dole kije inbaso kike Abbah yayimiki wani abunba kowa da kika gani yanada zuwa a irin wannan abun se kanayi kana kai zuciya nesa sannan zaka samu abinda kake nema meya tsakanin yauda gobe goben muzo indai baso kike kijama Ummah abun tsiyaba”.
“toh zanyi tinani akai danni bazan juri wulaƙanci wannan mara tarbiyyarba”.
suna cikin hirarsu suka samu adaidaita suka hau suka nufi sileja.
Suna sauka sukaima juna sallama Inteesar nashiga soronsu taci karo da Bilki tana zance tazo daidai wucesu tasaki tsaki tare da hararta tace”haka za’ah ƙare kullum cikin yawon bariki ba’ah can ba’ah nan anrasa mashunshini dole a riƙayimana ƴan gicce-gicce to ahir ɗinki Bashir yafi ƙarfinki”.
murmushi kawai Inteesar tayi tare da yɗauke kanta tayi kamar bada ita takeba ta wuce abinta koda tashiga ɗakinsu ta labartawa Ummansu komai ta nunamata tayi haƙuri taje goben da sukacemata bata wani jima da zamaba tashiga aikin gida ba ita ta gama ba se tara na dare taje tayi wanka sannan Uwar Gwarama taɗan zubomusu abinci kaɗan kamar yadda takeyi suka ansa sukaɗan lasa suka kwanta.
Washe garima da wuri suka nufi Comphany ɗin Namijin duniya shiga sukayi nan suka nufi hall ɗin da ake interview suna zuwa saka tadda bakowa sun juya kenan sukaga Sakatariya tana kallonsu a yatsine kamar wadda taga kashi tace”a cikinku wacece Inteesar”.
“gani”.
kallon tara saura kwata tayiwa Inteesar a zuciyarta tace”kome wannan ɗiyar talakawan zatayi a office ɗin Oga oho”.
a fili kuma tace”kizo muje office ɗin Oga”.
damm gaban Inteesar yabada lokaci ɗaya gumi yafara ketomata dakyar ta saita nutsuwarta tace”muje”.
nan sakatariya tayi gaba tabarsu nan kallonta Hauwa’uh tayi tare da cewa”muje naga kin tsaya”.
cikin dauriya ta aro jarumta dankarta lura tace”tom”.
nansuka bi bayan sakatariya har suka isa bakin katafaren office ɗinsa kallonta Feenah tayi cikin yatsuna tace”kishiga”.
“toh muje Hauwa’uh”.
“a’ah Inteesar kawai yace ke kijirata anan ita tashiga”.
lokaci ɗaya gaban Inteesar ya yanke tafaɗi komai nata seda ya tsaya cak saboda tinanin haɗuwarta da Namijin duniya jitayi kamar ta kwasa da gudu a zuciyarta tace”nashiga uku Allah yasa ba wani abun ya shiryamun ba saboda me za’ah ce ni kaɗai inshiga office ɗinsa anya bada wani abun a ƙasaba kuwa ni Inteesar”.
wata zuciyar ce tace”kiyi addu’ah insha Allahu ba wani abunda ze faru se alkhairi kumama aiga Hauwa taga shigar office ɗin nasa ko wani abunne ya faru zata bada sheda”.
cikin ƙarfin hali tace”sena fito Hauwa’uh”.
“tom Allah yabada sa’ah “.
“Ameen”.
nanta danna wani switch ƙofa ta wangale cikin sauri zuciyarta tashiga bugawa da ƙarfi gefe guda kuma tsoronsa ya dirarmata kanta a ƙasa tashiga tafiya!!!!!!!
Yanzu naji duka naga ruwan comments naji daɗi nagode Allah uabarmu tare much love.
Votes and comments
Plz share to others fisabilillah
Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo._r Mutanen Gwarzo.*
???? *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)
MALLAKIN
REAL EESHOW
HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…
BOOK 1
PAGES 0️⃣7️⃣➡️0️⃣8️⃣
Dukda kanta na ƙasa hakan be hana ƙamshin daddaɗan turarensa ya bugi hancinta ba lokaci ɗaya ta lumshe luli eyes ɗinta ta buɗesu akan tanƙamemen office ɗin Namijin duniya daya gaji da haɗuwa da abubuwan more rayuwa juyawar nan da zatayi tayi ido huɗu da wani tanƙamemen photon Namijin duniya yasha black suit a zaune ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sumar nan kamar kullum a kwance tayi luff da ita lokaci ɗaya taji wata mummunar faɗuwar gaba wadda bata taɓa jintaba a hankali tashiga bin ko ina na office ɗin da kallo juyawar nan da zatayi taci karo da Namijin duniya harɗe kan kujerar office tana juyashi karaf idanunsu yafaɗa na juna da sauri Inteesar tayi ƙasa da kanta ƙirjinta na dukan tara-tara a haka harta isa gaban Namijin duniya da yike ƴan rubuce-rubucensa bazato taji yace"saboda tsabar rashin tarbiyya sallamarma baki iyaba".
dukda tasan bata da gaskiya amma hakan besata ta nunamasa ba sema ƙara haɗe rai datayi a ciki-ciki tace”Salamu Alaikum”.
ba tare daya ɗago ba kamar ammasa dole yace”wa’alaki salam”.
“ina yini”.
wani banzan kallo me cike da tsana yake cifanta dashi ganin haka yasa Inteesar ta ƙara shan kunu ta tsuke ɗan pinky lips ɗinta niyyar zama takeyi akan ɗaya daka cikin kujerun dake gaban table ɗinsa ba zato taji ya bugamata tsawa cikin gadara da nuna isa yace”karki haumin kujera da wannan ƙazamin jikin naki da ba lallaima kina wankaba mara tsarki chairs ɗina na zaman masu tsarkine bana zaman faƙirai irinki ba”.
tsam Inteesar ta matsa tare da makamasa wata banzar harara cikin ɓacin rai tace”banzo nan gurin danka wulaƙani ba dan haka Malam dakata ka iya bakinka danni ba sakarkarun matannan bace wadda abin duniya ze rifemusu ido ayita yimusu wulaƙanci sunaji suna gani saboda abun duniya me kake dashi me gareka kaifa mutum ne kamar kowa balle intsaya kayita rainamun hankali inaji ina gani”.
cikin muryarsa me nuni daya kai ƙololuwar ɓacin rai yace”kinsan ko dawa kike magana kuwa”.
Kallonsa Inteesar tayi daga sama har ƙasa tace”eyi nasan da wanda nike magana man mara sanin darajar ɗan adam wanda baida tarbiyya ko kaɗan a gari nike magana man”.
cikin zafin nama yana huci kamar wani mayunwacin zaki yayi kanta lokaci ɗaya ganin yadda yanayinsa ya canza yasa wani masifaffen tsoronsa ya dirarwa Inteesae tashiga yin baya yana binta harta ƙure da bango ya ɗaga hannu da niyyar yarfamata saboda firgici hakan yasata rife oily eyes ɗinta lokaci ɗaya eye lashes ɗinta suka sauka bazar tsintar kansa yayi da ƙin marinta sema kallonta daya shigayi jin bataji saukar mari ba ne yasa Inteesar buɗe kyawawan eye balls ɗinta ta saukesu akan Namijin duniya bazato taji hannunsa a saman waist ɗinta ya matseta da jikinsa cikin ɗaga murya yace”cikin ni dake yau za’ah ga me tarbiyya dan yau sena nunamiki bani da tarbiyya badai ni kike kira mara tarbiyya ba zan gwadamiki rashin tarbiyya”.
ta buɗe baki da niyyar yimasa magana kenan bazato taji bakinsa cikin nata dukda irin tutturesa da take hakan besa ya kyaleta ba seda ya tsutsi bakinta kamar ba gobe jin alamu za’ah shigone yasashi saurin sakin Inteesar daketa hawaye yakoma ya zauna sosai take kuka harda shashsheƙa zatayi magana kenan Sakatariya Feenah tashigo suna haɗa ido da Inteesar Feenah ta makamata wata uwar harara cikin takun ƴan bariki da ko ina na jikinta yana motsi tana niyyar ƙarasawa inda namijin duniya ke zaune bazato taji muryarshi cikin ɓacin rai yace”waya kirawoki da kawai zaki faɗowa mutane Office ba knocking”.
batare data nuna taji haushi ba sema zaman rigar jikinta data shiga gyarawa tayi dan silifas ɗin ƙirjinta yaƙara fitowa tace”sorry sir dama nashigone dan intambayeka ko kana buƙatar wani abunne”.
“dama in inada buƙatar wani abun ba danna switch nike ba”.
“sorry sir”.
tafaɗa cikin girmamawa ta juya ta ƙara bankawa Inteesar harara a zuciyarta tace”me wannan ƙazamar yarinyar takeyi takeyi a office ɗin Oga da har yike dakamun tsawa”.
wata zuciyarce tabata amsa da” sede in temakonta zeyi amma dai bade ya kula wannan ƙazamar yarinyar da soyayyaba”.
tafita cikin sauri ta fita ganin yanda Namijin duniya yawani haɗe rai.