NAMIJIN DUNIYA COMPLETE NOVELTHE WORLD MAN COMPLETE NOVEL

THE WORLD MAN (NAMIJIN DUNIYA) COMPLETE NOVEL

Takurewa Inteesar tayi ajikin kujeran jikinta yashiga rawa saman goshinta da hancinta yafara fitar da zufa tamkar babu a.c a office ɗin kanta ta fara juyawa tana shura ƙafarta cikin tsananin azaban ciwon da cikinta ke mata a take idanunta suka shiga tsiyayar da hawaye ga jikinta dake karkarwa tamkar mazari cikin yanayin ficewar hayyaci ta janye hijabin dake jikinta tare da tasani ba ta dafe ƙasan maranta tana kuka.

Da sauri ya rintse idanunsa sakamakon ganin yanda saman breast ɗin ta suka bayyana ta saman doguwar rigar jikinta da sauri yaja baya tare da rintse sexy eyes ɗinsa dukda bawani abu dayaji a jikinsa kome ya tuna kuma yayi saurin buɗe wa yana kallon yanda hawaye ke ambaliya a idanunta kamar wani famfo dakyar ya saita kansa jiyayi a zuciyarta tabashi tausayi amma dake ya iya wanke allonsa bazaka ganeba saboda ƙara shan kunu daya ƙarayi cikin muryar zaratan maza yace”keeeeh”.
tsabar firgita tafara ja baya yana binta har suka isa inda ta fara mofewa luuuu ta tafi zata faɗi hakan yasa cikin zafin nama yasa hannu ya jawota bazato ta faɗo jikinsa hakan yabawa ɗankwalinta damar saɓulewa ƙasa yalwataccen gashinta ya sauka a gadon bayanta bazato sukaji tsawa ƙara shigewa tayi jikinsa ta inda ƙirjinsu ya haɗe dana juna gam .

Ɓangaren Namijin duniya ko ba’ah cewa komai saboda ya shagala da kallon zara-zaran eye lashes ɗinta da suka kwanta sukayi luf dasu yanayin iskar da akeyine yasa yalwataccen gashinta kaɗawa ya rifemata fuska bazato taji lallausan hannunsa a fuskarta yana gyaramata dogon gashin sun daɗe suna kallon juna eyes to eyes saurin dawowa yayi daga dogon tinanin daya shiga bazato taji ya hankaɗeta ya saki wata uwar tsuka kallon farar suit ɗinsa yayi meze gani suma sun ɓaci da jini sosai cikin ƙololuwar ɓacin rai ya buɗe baki zeyi magana kenan yaji muryar Abbih ɗinsa na cewa”Son buɗe nine”.
damm ƙirjinsa yabayar sakamakon ganin Inteesar dashi duk sun ɓaci da jini murya kamar ammasa dole yace”toh Abbih ganinan zuwa”.
wani ƙasƙantaccen kallo ya watsawa Inteesar tare da yin tsuka bazato taji lallausan hannunsa a nata ya nufi toilet ɗinsa da ita!!!!!

Kuyi manage da wannan saboda kwana biyunnan da banyin typing yasa na sangarce nasan insha Allahu nanda gobe zan dawo normal saboda akwai labari a bakina sosai

Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo._ar Mutanen Gwarzo.*???? *MAN OF THE WORLD*
(NAMIJIN DUNIYA)

MALLAKIN
REAL EESHOW

HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCI…

BOOK 1

PAGES 1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣

   Ba  abinda take se aikin rawar jiki domin wani sabon tsoronsa ne ya dirarmata dan gani take wata muguntar ya shiryamata domin tasan baze taɓa barinta ba tunda ta ɓatamasa guri ɓangaren Namijin duniya ko yana shiga da Inteesar toilet ya cire ƴar saman suit ɗinsa ya fita.

Dukda tana cikin firgicin abinda ya fitar dashi amma hakan be hanata bin ko ina na toilet ɗin da kallo ba a zuciyarta tace”amma gaskiya ankashe kuɗi a banɗakinnan kamar baza’ah mutu ba ace duk toilet aka tsaya ƙawatawa haka kamar mutum ya zuba abinci yaci dan kyau”.
tana cikin wannan zancen zucin taji buɗe ƙofar Namijin duniya ƙara raɓewa tayi ɗan nesa dashi kamar wata munafuka ƙarasa shiga yayi ya zauna kan kujerar wanka yashiga tinanin irin rashin mutuncin da zewa Inteesar a zuciyarsa yace”haka kurum Ahmad kasa nabi shawararka kan wannan ƙasƙantacciyar yarinyar aiko dole kazo asan mafita dan seta gane kurenta bazan taɓa bari abinda takemun ya tafi a banza ba wallahi jibi yadda tasa na tsaida mahaifina a waje duk saboda iskancinta dole na gyaramata zama “.
yana cikin wannan maganar suka haɗa ido da Inteesar daketa faman zare ido kamar wadda tayiwa sarki ƙarya wani kallon tsana da ƙasƙanci da nunamata zaki gane shayi ruwane yike binta dashi tare da yin tsaki yace”kin dena kallona da wannan idanun naki kamar na mayu ko senazo nan na tattakaki mara mutunci kawai “.
yaƙarasa zancensa tare da sakin wani uban tsaki yana yamutsa fuska sakamakon zuciyarsa dake tashi saurin duƙar da kanta ƙasa tayi jiki a sanyaye zuciyarta na bugawa da sauri-sauri ga wata tsananin faɗuwar gaba dake damunta.

A zuciyarta tace”nashiga ukuna Allah kaɗai yasan irin muzantani da wannan mara tarbiyyar mutumin zeyi haka nanma ya lafiyar kura bare antaɓota na ɓatamasa kujera yanzufa wannan mara sanin darajar ɗan adam ɗin duk wani fishinsa kaina zeriƙa hucesa”.
duk wannan zancen zucin da Inteesar take batasan a fili takeyinsa ba kaf Namijin duniya yajita bazato taji ya bugamata tsawa yace”keeeh dawa kike”.
saurin dawowa tayi daga zancen zucin da takeyi batasan lokacin data ce”ba magana nayiba”.
hakan yayi daidai da buga ƙofar toilet ɗin kwafa yayi tare da tashi cikin tafiyarnan tasa ta isa ya nufi ƙofa rakashi tayi da uwar harara tare da yin tsaki tace”abanza man kare ko ƙarya nayimaka kanada tarbiyyarne oho stupid kawai ji da Allah wata irin tafiya da yike kamar wani wahainiya waishi isashe”.
jin abinda take cewa ne yasashi sakin murmushin dabe shirya yinsa ba ya girgiza kai tare da wucewa yayi kamar bejitaba buɗe ƙofar yayi ya anshi wasu leda guda biyu na store sannan ya mayar ya rife a hankali seda yazo gabda Inteesar yace”heey you ƙasƙantacciyar cleaner ga kaya nan wa’inda ba’ah taɓa sawaba sede a gansu a t.v ko a jarida asa nasandai kan wa’innan kika ɓatamun kujera base kin nunamun kin balaga ba har kin fara period ba”.
yana gama faɗin haka ya wani watsamata kayan a jikinta ya buga tsaki ya nufi can cikin toilet ɗinsa yana murmushin gefan baki domin yasa ya gama da ita.

Wasu zafafan hawayene suka zubomata saboda tinda take ba’ah taɓa cin mutuncinta kamar yadda Namijin duniya yaciba ko wanda Uwar Gwarama take musu bekai wanda yayimata ba saboda ba wanda ya taɓa kiranta da ƙasƙantacciya se Namijin duniya gashi ba yadda za’ayi tabar aikinnan Abbansu ya kyaleta a fili ta furta “wallahi bazakaci banzaba indai nice sena rama mara tarbiyya kawai inbanda tsabar jahilci meyakawo maganar wani period banda ɗan iska neshi banda kayana sun ɓaci wallahi da bazansa wa’innan ƴan iskan kayan ba da har akemun gori kansu “.
ta daɗe tana wannan maganar taji buɗe ƙofarshi dukda taji haushi cin zarafinta dayayi amma hakan besa ta ɗago ta kalleshiba sema ƙasa data ƙarayi da kanta saboda tinda yaga jinin nan taji tana masifar jin kunyarsa ko rashin kunya zata yimasa bata yadda su haɗa ido har yazo dafda ita bata ɗagoba sema wasa data riƙayi da zara-zaran ƴan yatsunta taji muryarsa cike da rashin mutunci yace”saura kuma idan kin gama ƙazantar taki kiƙi wanken toilet kinji”.
yanayin yadda yayi maganar kamar yaga kashi hakan baƙaramun ƙara sosa zuciyar Inteesar yayiba ya fara tafiya abinsa bazato yaji tayi tsaki ta wuce fuuu cikin inda ya fito murmushi yayi danyasan ya ɓatamata rai ya fice.

Ɓangaren Inteesar ko tana shiga wanka taji ta tsaftace jikinta sannan ta buɗa ledar daya jefeta da ita pad tagani dozen se pant dozen da breziya dozen se kuma wata haɗaɗɗiyar abaya maroon taɓe baki tace “kome zakayimun kayimun lokacinka ne maratarbiyya kawai oh ni Aishatu wannan mutumi shiya yankewa iskanci cibi banda ƙasurgumin ɗan bariki ne meye na wani haɗowa da breziya “,.
ɗaukae pant tayi guda ɗaya da pad tasa ta da bra ɗaya ta shirya jikinta tsaf cikin haɗaɗiyar abayarta data sha adon stone se walwali take baƙaramun ansar jikinta kayan sukayiba tayi rolling da ɗan kwalin abayar sosai farar fatarta tafito tayi wani mugun kyau tamkar balarabiya kallonta a madubi tayi taga tayi kyau sosai tinowa datayi da waye ya siyo kayan yasata jin wani ɓacin rai lokaci ɗaya ta haɗe rai tayi tsaki tace”shegun kayanma da akemun gori kansu ko kyau basu dashi”.
tatattara sauran ta zubamasa kayansa tashiga wanke toilet ɗin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button