THE WORLD MAN (NAMIJIN DUNIYA) COMPLETE NOVEL

Ɓangaren Namijin duniya ko yana fita ya tadda su Ahmad zaune da Abbih ɗinsa suna hira murmushin gefan baki yayi tare da cewa”sannu da zuwa Abbih”.
“yauwa Son mekakeyi ne a toilet”.
zeyi magana kenan Adam yace” sabuwar Cleaner ɗinsa yike nunawa yadda zata kunna kayan toilet ɗin saboda kartayi ba daidaiba”.
saurin sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya yayu saboda banda Adam yayi saurin magana besan mezeceba zama yayi tare da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya yace”Abbih anyini lafiya”.
“lafiya ƙlau Son dama wucewa zanyi nace bara na shigo na kawomaka ziyarar bazata”.
“aiko naji daɗi nagode Abbih Allah yaƙara girma”.
“Ameen Son Allah yayimuku albarka”.
haɗa baki sukayi da “Ameen”.
suna cikin wannan hirar Inteesar tafito tindaka ƙafarta har zuwa kanta kwanne cikinsu yabita da kallo a hankali take tafiya ganin yadda hankalin kowa yike kanta yasa Namijin duniya yaji wani abu yazo ya tsayamishi a maƙogoro harta iso inda suke cikin girmamawa ta duƙa har ƙasa tace”Ina yini ranka shidaɗe”.
“lafiya ƙlau daughter ya aiki”.
“Alhamdulillah”.
tana gama faɗin haka ta miƙe da niyyar tafiya Abbih yace”ɗiyata da wanne matakin karatu kike amfani”.
zatayi magana kenan Namijin duniya daketa gumi yayi saurin cewa”batayi karatu ba tausayi tabani datazo neman aiki dankar inbarta haka yasa nabata cleaning “.
sosai tayi mamakin abinda Namijin duniya yace nan ta shiga tinanin itako meta tsaremishi a duniya da harya tsaneta haka wasu hawayene masu zafi suka zubomata tayi saurin sharewa taji Abbih yace”ka kyauta kuwa Son Allah yayimiki albarka ungo wannan”.
ya miƙamata bandir ɗin yan dubu-dubu da farko taƙi ansa hakan yasa Abbih cewa”ki ansa ki ɗaukeni tamkar mahaifinki kinji”.
“toh nagode Allah yaƙara buɗe da ɗaukaka”.
“Ameen “.
nanta fita kallonsu Namijin duniya Abbih yayi tare da cewa”amma yarinyar nan tanada nutsuwa hakanan naji ta kwantamun a rai wallahi anyako ba surukata bace ba cleaner ba kuka ɓoyemu naga kwata-kwata batayi kama da masu sharaba”.
kallon juna su Namijin duniya sukayi tare da cewa “wallahi Abbih cleaner ce”.
murmushin manya Abbih yayi tare da cewa”to ni zan wuce”.
nan suka miƙe dan yimasa rakiya seda suka fitar dashi har gurin motocinsa sannan suka juya.
Ɓangaren Inteesar ko tana fita ta saki wata nannauyar ajiyar zuciya tare da dafe ƙirji waigawar nan da zatayi sukayi ido huɗu da sakatariya nata bankamata harara tsaki Inteesar tayi tare da cewa”andaiyi asara zuwa duniya mutum yayita ɓata lokacinsa kan wanda bemasan yanayiba dama hijabinki kika fara sawa kina rifawa wannan kwantaccen ƙirjin naki da yike kamar farantin fawa asiri ƙila yasan kinayi”.
“oho dai a haka ake ganin ake sha’awa kuma ba’ah kula na masu miƙaƙƙen se inzonan in zauna kanki da ubanki inga ƙaryar fitsara “.
dafa kwankwaso Inteesar tayi a zuciyarta tace”wai wannan me ɓaka-ɓakan duwawun tazauna kaina aina shigesu”.
a fili kuma taɓe baki tayi tace”waya gayamiki dama ni inaso asoni ai abu me tsada binsa ake yana wulaƙanci abu me arha ko kullum buɗesa ake ana tallarsa kamar dai wannan ɗan silifas ɗin ƙirjin naki me kama da takalmi ɗan madina saboda taushi”.
taƙarasa zancenta tare da niyyar fita Sakatariya Feenerh ko cikin jin ɓacin ran maganganun Inteesar tace”inkin isa ki tsaya inbaga tsoro ba dasekin gane ke ƙaramar mara kunyace wallahi”.
gabda zata fita ta juya tace”Allah ya kyautamun na tsaya ina goga jiki da wannan ƙazamun jikin naki dayasha taɓawar ƴan bariki”.
taƙarasa zancenta tare da saurin ficewa da gudu dankarta cimmata tasan duka zatayimata sosai abinnan yaƙara ɓatawa Sakatariya rai taji taƙara tsanarta.
Zaune suke suna hira Ahmad ya kalli Adam tare da cewa”ammafa yarinyar nan ɗazu baƙaramun kyau tayiba kasan Allah seda ta matso nagane wacece Allah yayi halitta anan gurin”.
“gaskiya tayi kyau sosai wannanfa da a gidan hutu take zatayi yaya wallahi”.
cikin ɓacin rai Namijin duniya yace”ban kiraku nan dan kuzauna kuyita yimun surutan banza ba”.
yaƙarasa zancensa cike da ɓacin rai kallonsa Adam yayi yace”abokina lafiya naga duk ranka yaɓaci kamar wata girlfriend ɗinka abinda kakeyifa like kishifa anya abokinmu ko be zurma ba kuwa Ahmad “.
“nima tinanin da nikeyi kenan”.
cikin tsananin ɓacin rai Namijin duniya ya miƙe ya fice a fusace binsa sukayi da kallo gabaki ɗayansu sannan suka tafi suma.
4:00pm
Zaid na tsaye jikin motarsa suka fito daga cikin comphany ɗin bakinsu ɗauke da sallama suka ƙarasa inda yike murmushi yayi tare da cewa”wa’alakumus salam sannunku da aiki”.
“yauwa ina yini Uncle Zaid”.
“lafiya ƙlau Hauwa’uh”.
“ina yini”.
“lafiya ƙlau My heart ya aiki”.
“Alhamdulillah ya naka”.
“lafiya ƙlau”.
nan suka shiga motar yajasu suka nufi Suleja.
Yana gama daidaita parking suka fito gabaki ɗayansu kallon Inteesar Hauwa’uh tayi tare da cewa”sena shigo Uncle Zaid ka gaida gida mungode”.
“toh Hauwa’uh se Allah yakaimu”.
“Ameen”.
taƙarasa faɗa tanaiwa Inteesar inkiya da ido ta wuce ƙasa Inteesar tayi da idonta tana tinanin ta inda zata fara faɗawa Zaid maganar mahaifinta taji muryar mahaifinta na tunkarosu batace ƙalaba harya ƙaraso inda suke Zaid ya duƙa cikin girmamawa yace”Babah ina yini “.
“lafiya ƙlau ɗannan ya magabatanka”.
“lafiya ƙlau Babah”.
“masha Allah Inteesar ta faɗamaka saƙona kuwa?”.
“a’ah Babah”.
“aidama nasan bazata faɗamaka ba tunda ita ba auren bane a gabanta haka nace da ita indai da gaske kake ka turo iyayenka a tsaida ranar biki domin nina gaji da gulmammakin jama’ar unguwa duk inda na shiga ana nunani “.
Inteesar da kanta ke ƙasace ta share hawayenta taji Zaid yace”Babah dagaske nike son Inteesar insha Allahu gobe zan turo iyayena domin banaso na rasata”.
“to toh madallah “.
nan Abbah ya juya ze tafi Zaid yace”Babah ga wannan ayi cefane”.
ya miƙamasa bandir ɗin ƴan ɗari bibiyu saurin miƙe hannu yayi tare da cewa”angode “.
nanya shige gida cikin murna kasa ɗaga idonta tayi ta kalli Zaid ganin haka yasa Zaid be takurataba suka ɗan taɓa hira kaɗan tashiga gida tana shiga Zaid yabita da kallon tausayi lokaci ɗaya yaji soyayyarta taƙara nunkuwa fiye da da a zuciyarsa yashiga tinanin anyako wannan dagaske shine mahaifin zuciyarsa ba riƙonta yikeba ya juya zetafi kenan yaji muryar Uwar Gwarama a bayansa tace”ɗannan tsaya “.
saurin juyawa yayi jin muryar babbar mace saurin duƙawa yayi a tinaninsa itace mahaifiyar Inteesar yace”Ina yini Ummah”.
“lafiya ƙlau ɗannan miƙe kaji dama magana nazo muyi dakai bakaine me neman auren Inteesar ba?”.
cikin girmamawa Zaid yace”eh nine Ummah insha Allahu gobe zan turo “.
“yaro aiba wannan ya kawoni ba temakonka nazo inyi yaro karka sake ka auri wannan yarinyar data daɗe tana bin maza da sunan wai karatu take”.
saurin ɗagowa Zaid yayi da mamakin jin kalamanta yace”bangane bin mazaba Ummah”.
“karuwanci daka sani shi wannan yarinya takeyi itada wannan Hauwa kullum basu gun wancan ƙaton yau gobe basu gun wancan ninan shedace saboda ƴar kishiyata ce shiyasa ko kare be taɓa zuwa ƙofar gidannan da sunan yana sonta ba sekai kowa a unguwarnan yasan abinda suke aikatawa shiyasa bata da mashinshini ko ɗaya shine danaji abinda Malam yike cewa nace bari inzo insanar dakai komai amma akwai ƙanwarta Jamilah yarinyar kirkice in kana sonta nabaka ita duniya da lahira ƴatace gama tanan tana fitowa daka gida Jamilah zoku gaisa man”.
saurin ɗaga ido Zaid yayi dan yaga wacece Jamilah cikin yauƙi taƙaraso inda yike ana karairaya kamar wata riƙaƙƙar ƴar bariki tana fari tace”ina yini”.
murmushi Zaid yayi tare da cewa”lafiya ƙlau Jamilah sannunki”.
“yauwa Ummah ni zan wuce makaranta”.
” to ƴar albarka ayi karatu sosai”.
“toh Ummah se anjuma babban Yayah se anjuma”.
ta wuce tanata karairaya binta yayi da ido yana kallon ikon Allah yaji Uwar Gwarama tace”Jamilah kenan ƴan makaranta kullum aikin kenan ba dare ba rana karatu ni har cemata nike ta riƙa barin kwakwalwarta tana hutawa sede tayi murmushi ya kagani ɗana tayimaka?”.
murmushi Zaid yayi tare da ƙara bin Jamilah da kallo yace!!!!!!!!!