YAN ABUJA HAUSA NOVEL

YAN ABUJA HAUSA NOVEL

Qarfe hudu na asuba suka fito sukai wanka tare da alwala mai kyau suka koma, bayan sun shirya ne suka fara habatar da nawafeel, kowa ya fara addu’ar shi, Jabeer ne ke hango baqi, a gefen shi dan ba wuta sai ta wayar shi suka kunna, miqa hannu yai yaga meye, dagawar nan da zai yaga shinkafar da Innarmu ta bashi ce jiya a dafa mata, ” Ya salam ! Tab lallai da safe na shiga magana wajen innarmu, aiko ni tai na kawo ki dafa mata wai yunwa take ji, tin safe bata ci komai ba, bata cin faten wake, shine gaba daya na manta” ” haba Yah Jabeer bai kamata ka manta da wannan mahimmin abu ba kuwa, domin yunwa ba ta da mahadi” a qasan ranta kuwa jinjina wa Innar mu take wajen iya hada makirci, matar da taci ta tande kwano, har ta aiko wai a dada mata in akwai, tace babu shine take cewa ba ta ci, ikon Allah, lallai Allah mai jin qan bawan sa mai tinawa da shi a kiwanne hali yake, da bata zama mai neman taimakon Allah a kimai ba da bai taimaka mata jiya ba da bama ta san me ake shirin kulla mata ba, kiran sallar asuba ne ya katse su ya fita masjid an yi sallah, ya dawo, ita kuma tayi tata a gida tai azkar tai karatun asuba da take yi kullum ba fashi komai aikin da ke gaban ta sai tayi ko rabin shafi ne kan ta tashi, tana rufe qur’ani ya shigo, lokacin gari ya dan waye, miqewa sukai akan zasu maida bacci, dan Nafeesa ke abin karyawa a gidan, in ba arziqin abin karyawan ma da dama koko kawai zasu dama su sha, sallama sukaji anyi……….

…………
….
[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: ???????? ‘YAN ABUJA. ????????

 BY HAERMEEBRAERH

Page 8:

Nafeesa ce ta shigo,” Yah Jabeer Innarmu tace ka bada shinkafar tin da tayi wuyar dahuwa” ???? ” inna lillahi, ni gaba daya mantawa nai shaf dana shigo, dan Allah ki bata hakuri kice yanzu za a dafa” tace in ka fadi haka na amso ka bata ta fasa wataran an dafa” “My goodness, yau ya zan na je gaida Innar mu, yq kk ga fuskar ta tai fushi ko?” ???? ” hmmmm ba kadan ba kuwa Yah, amma tace kar na fada maka tai fushi” Juwairah a ranta tace” ina fa zata so ya sani tinda tana son nakasani ta qarqashin qasa”???? dauka yai ya miqa mata, yace ta bata hakuri sosai kan ya shigo, fita tai da ita tana mai dariyar zaka amsa ne in ka shigo.
Bayan sun taba baccin su ne sun tashi wanka sukai sukai brush su ka shirya, hijab ta dora akan kayan ta matsattsu da tai ma mijin ta kwalliya da su kan ya fita, sun shiga bangaren na su Innar mu lokacin ta gama.raba abin karyawa, tace akai masu sai ga su sun shigo, duqawa Juwairah tai har qasa suka gaisa,” Ya jikin Nafeesa tace bakiji dadi bane yasa ya aje bai baki ba” zare ido tai cikin duqar da kai,” da sauqi Innarmu na ji dama sosai” to Allah ya qara lfy, yasa amarya za ai min ko ango, danni na gaji da lfy sa banga qaho ba aure wata na biyar kenan shiru ba magana” ta fada in a form of wasa take, amma duk wanda ya kula ya san magana take fada mata, murmushi tai sosai tace” Innar mu karki damu komai lokaci ne amare za a samo maki masu yawa da masu kawo cefane har sai kince sun isa haka” tana fada ta miqe tai wajen Baba Balarabe ta gaida shi, sake baki Innar mu tai, shiko gogan be gane magana suka sakar wa juna ba, dadi yake ji wai Innar shi da matar shi akwai shaquwa, har suna magana irin wannan a gaban shi, matsawa yai yana” akwai abinda zan taya ki ne Innata?” Murmushin qarfin hali tai ta ce eh ba a rasa ba, dan dai kawai kar ya koma wajen da matar shi take, ” Baba ina kwana?” Lfy qalaou diyar albarka, kina lf” ” lfy qalaou babana” ” to madallah, Juwairah ina son ki ta hakuri da wannan Innar taku, wani hali ta dakko d ni kaina ta canja min kwata2 ba kamar yanda na santa ba, dan haka kema sai kinyi hakuri, abotakar ta da Goggon ku ba abu ne mai kyau ba, na yi nayi na raba su amma abun yaqi” ” Ba komai Baba , ai uwa ce a wajena Innar mu ko da ba matar ka bace, mahaifiyar Yah Jabeer uwa ce a wajena, tinda ita ta haife shi, kuma shi din mijina ne, in ban so mahaifiyar shi a tawa ba ni kaina ba zan samu kwanciyar hankalin gidan aure ba, rikicin yawa zai min, da mahaifiya ma ana samun sabani dan haka ita ma a hakan na dauke ta, watarana ba zatai ba” ” Allah ya miki albarka , halayyar mahaifin ki da mahaifiyar ki ba wanda kk bari” murmushi sukai dik, bayan sun gama gaishe2n su suka koma suka karya ,” to ni zan wuce sai na dawo, ki kular min da kanki, kar ki wahal da kanki ” tasowa tai ta zagaye hannayen ta a wuyan shi shi kuma ya zagaye qugun ta sukai ma juna kiss sosai, da kyar ta kwace kanta, sai wani shinshina ta yake???? ” Yah zaka makara fa, ka tafi cikin amincin Allah, Allah ya bada kasuwa mai yawa mai albarka, ya kare ka daga haramun komai qanqantar ta, Allah ya hada ka da halal komai qanqantar ta, ka kular min da kan ka, ka tsaida sallah akan lokaci, in kaji yunwa ka taimakeni kaci abinci, kaga yanzu ba da bane ba abubuwan da sai na ci gaba da dafa maka kana tafiya da shi, karka barmin kan ka da yunwa kaji?” ” Karki damu an gama ur higness” ya dan duqa alamar gaisuwa, dariya sukai ta raka shi har waje, ta dawo daki ta hau gyara wajen da suka ci abinci.

” kai jama’a wai dan tsabar baqin ciki na aje flask din nan anan an kai min shi can, ko uban wa ya ce a tavan kaya oho, shikenan mutum in yana haushin talaucin da yai mai katutu sai ya dinga taba kayan da ba nashi ba yana canja masu waje? Oh ni sarai na ga abin da ya ishen yau” kamar ba zata amsa ta ba amma taga dacewar bata amsar” Hmmmm Allah nawa inji bamaguje, to ai dai har yau wata kusan biyar ban ga daya daga YAN ABUJAN sun yi koda waya bane balle nace ko an yi maki wani aike na azo a gani, ana nan dai yanda ake, ba wani hura hanci da za ai mana kuma ” haba kamar ta ari baki dan masifat da ta taso mata lokaci daya ta yunquro,sai bala’i take tana gore2n ai abinci ma wataran ita ke taimakawa, Mama tace daga yau in ta haifu karta qara taimakawar taga in bazata rayu ba ita da danta? Ammar ne ya kama hannun maman shi yana kuka, dan baya son hayaniya shi sam, daukar shi tai sukai daki sika bar Goggo na kumfar baki.

Oga Zaks na gani sun fito daga wani daki mai duhu sosai, Alh Kalla dauke da Saudat
Alh Salihu dauke da Suwaiba, suna fitiwa, ” to ku maida masu sabbin kayan da kuka zo da su kuyi gida,nan da awa uku zasu farka, kuma ku kwanta gefen su a matsayin bacci kukai, domin wannan magungunan da sukai ta sha zasu sa masu kasala da ciwon jiki, na kammala duk wani aiki da za ai akan su, kudi kuma sai kun ce sun ishe ku, dan mahaifar su na da kyau sosai, Dodo yayi farincikin samun ta, ba a taba kawo mata irin wannan ba, nima kuma shaida ne????, hahhahaahhha” godiya sukai suka canja masu kaya sukai mota da su sai cikin.garin.Abuja, kowa ya dau hanyar gidan shi, fadar kyau da tsaruwar gidajen nasu bata baki ne kawai, readers ku hango kowanne gida mai kyau kawai a idon ku, a gado suka aje su suka kwanta gefen su sukai ta baccin asara, basu suka farka ba sai wajen lq’asar, miqa Suwaiba tai, tana hamma, tana kallon dakin nata, ko ta ina dakin ya ruda ta, ko tunanin komai ba tai ba sai na bari taga wannan gidan na ta mai dimbin kyau, tashi tazo yi taji wani.ciwo a cikin ta komawa tai.ta zauna, tana “wasssshhhhhh Allahna, me ya samen a ciki kum? Duk jikina ciwo yake” kamar a tare suke wannan maganar da Saudat domin tafi Suwaiba raki harda kuka, a rude mazan suka tashi kamar ba abinda ya faru” me ya same ki Sweetheart?” Cikina” dagawa yai ya gani,” Ayya kiyi hakuri zai warke a hankali hatsari muka samu a hanya, ke da yar uwar ki kwalbar cup din da kuke shan drinks ta cake ku a ciki, amma mun kaiku babban asibiti an dinke wajen, so a hankali zamu jira ya warke mu ci gaba da shan amarcin mu ko” ya fada tare sa jawo ta jikin shi yana shafa ta, kwantar da kanta tai a jikin shi kamar ba ita ba, tashi yai ya je ya hado mata abinci tana daga gadon ya aje mata, ya zauna yana bata a baki, wani dadi ne ya lillibe Suwaiba yau mafarkin su ya zama gaske, tana gama wa ta dau waya ta kira Goggon ta, wayar a kashe take ta kunna ta tanakiran ta ko bugu daya ta dauka kamar jira take, ” haba yar nan yau wata biyar da kwana uku, kun tafi shiru ba magana ba aike” wata biyar da kwana uku??????…………
[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: ???????? ‘YAN ABUJA ????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button