YAN ABUJA HAUSA NOVEL

YAN ABUJA HAUSA NOVEL

Suwaiba ta tare da mijin ta,kuma kasuwanci ba laifi wataran a samu ya siyar da kayan dika, ribar dubu biyu ko ukuma, wataran kuma su ragu, a haka shi da ya fara da capital na five thousand yanzu ya kai seven thousand, ai an samu, kuma a ciki yake qoqarin ci da su.

Salma da Huwaila kusan ta tare suka haihu, Salma ta haifi Yaran ta biyu masu matuqar kama, da kyau, ita kuma Huwaila ta haifi namiji, mai kama da Bangis sak, kwana tara ne a tsakanin su,yaran Salma sun girmi na suwaiba, an yi suna in da akai suna ba komai a dukka gidajen sai to gwanda na Salma ma, dan anci an sha,mutane ne dai ba su zo ba sosai, ita ko Huwaila , komqi qayau sikai sunan nasu, ga habaici da suke sha wajen yan gulmar da ke zuwar masu barka da kuma wanda suka zo sunan, yaron Salma na mijin An sama mai Muhammad, macen Fateema,a hakan suke kiran su, sai yaron Huwaila da aka sama suna, Umar, rayuwa tai ta juyawa wadannan bayin Allah da dadi ba dadi duk haka ake ta fama, wanda kusan ko ina ne dama yanzu a wannan lokacin haka ake ta fama, in da gidan Baba Balarabe ya bunqasa da arziqi dan Salihu ya shiga gwanjo da sa’a sosai, yanzu har dila biyu yake budewa, Juwairere kam arziqi ba a magana sai godiya, gidan su mai kyau daki biyu da dinning, sai babban palo, mai dauke da manyan kujeru da kayan kallo, yarinyar ta sai wayo take.

Shirye2n bikin Nafeesa ne ya kama gadan gadan, in da Saudat kuma sauran kwana uku kenan ta fita takaba, a yau din ne su Juwairah da Jabeer tare da diyar su Abrar za su zo, Jabeer ba qaramin qoqari yai ba a yan watanni biyun, dan ita Juwairah bama ta sani ba tinani take in sun je ina zasu sauka, bangaren su yanzu Adda Suwaiba ne a ciki, bata da masaniyat daki daya da bandaki da palo madaidaicin da Jabeer ya masu a filin dake gefen gidan su wanda yake kamar kango je a da, sai yar tsakar gidan qarama sosai ba wani fili sosai, ba laifi a irin gidajen cikin gari a kano wannan yayi kyau, sai wajen azahar suka iso, wajen Innar mu ta shiga, Nafee da gudu ta je ta rungume ta suka hau murna, bayan sun natsu ne ta miqe aka hau gyara amarya da ita…..

Juwaireren mama na gayyatar dukkan fans din novel din ‘YAN ABUJA zuwa wajen bikin Nafeesa, Allah ya bada ikon zuwa ameen????
[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: ???????? ‘YAN ABUJA ????????

   BY HAERMEEBRAERH

Page 31:

A yanzu hankalin Talle ba qaramin tashi yai akan ya nemo Salma ya bata hakuri akan abinda ya mata, dan yasan tinda ya sake ta, ga ciki tabbas tana nan qullace da abinda ya aikata mata, kuma baya fatan ma.yace zai maida ta, saboda ba zai iya riqe ta ba yanda ya kamata, ba irin rayuwae sa salma ke.mafarki ba kenan, ” Ya Allah ka bata ikon yafe min a duk sanda na bayyana a gaban ta ina mai neman yafiyar, ko bam samu zuwa ba na mutu.Allah ka wakilci ce ni a zuciyar Salma ta yafe min” ” Haba Talle, sai yaushe zaka daina zubda hawaye ne? Na baka shawara mu kama akuya daya mu siyar, ka samu na mta dana guzuri, kaje wajen yarinyar nan ka nemi yafiyar ta, amma ka kafe kace a’a to taya kudin zasu samu? In aka siyar nima ba sai na samu na kafa wani jarin ba? Ko dari dari biyu muke samu a rana a matsayin riba ai zamu toshe wata gabar, balle nasan zamu samu yafi haka, ga tashin hankalin batan Haule, duk da ina kyautata zaton gajiya tai da halayen mu ta gudu wajen mahaifiyar ta, amma abun na matuqar damuna” ” ta zancen Haule kwantar da hankalin ki, ta na wajen mahaifiyar ta, da kyar suka amshe ta, amma yanzu baki ga gatan da take sha ba, abokina da yamin hanyat auren babar ta ta ne ya ke sanar sani hakan, yana mun godiyar kyautawa da nai na barta tazo taga mahaifiyar ta” ” Allah sarki, a gaskiya mun tafka babban kuskure a rayuwar mu Allah ya bamu ikon gyarawa, me zai hana ka samu a islamiyyat malam Sallau kaga ana karatu kyauta, awa biyu zamu bayar a a kwana uku kawai, dan akwai jahilci mai tarin yawa a rayuwar mu, kai kuma ka na zuwa ta bayan isha’i kai da Yaya” ” gaskiya kin kawi shawara dan abubuwan da muka tafka da da ilimi a tattare damu musamman na addini da bamui ba, Allah ya yafe mana” ” Ameen” ” ina yarinyar nan Hawaila? Ki taran su har Baban gidan zuwa anjima za ai maganar auren ta, gobe juma’a, suna da daki, a bangaren su, da katifa dan haka ban ga dalilin ta ci gaba da zama a gaban mu ba ko me kk ce, kin ga a hankali muka samu sai mu mata kayan daki kamar kowa” ” wannan shawarar tayi, tin da ga yaron su nan Umar Allah ya bayar gwanda ai auren gobe komai ya wuce,Allah ya sanya mana albarka dikkan mu, ya yafe mana” ” Ameen, na gode maki da kk canja halaye daga munana zuwa kyawawa, yanzu kyaun ki ya fito matata, nima ina fatan kin ji dadin canjawa ta?”ya fada yana mai matsawa kusa da ita, ita kuma tana wani sissine kai, wai kunya????” naji dadi mana Talle sosai, nan gaba ma swatyn nima zan dinga kiran ka irin yanda kk cewa Salame” dariya ya kwashe da ita ta gane inda ta dosa ( Sweety) shine abinda take son cewa.

Da yamma za a tafi dinner kowa ya sha gaye hae ya gaji, ba a cika wa Nafee irin kwalliyar nan ta yanzu ba,ta dai sha powder da kyaran jikin da ya fito da kyaun ta, ( aikin Juwaireren mama kenan) ba qaramin kyau tai ba, sun so kwarai a aske mata gira ai shaping din ta amma Juwaireren mama ta hana, domin hakan haramun ne, tinda akwai abinda ake yi a danyi dabara kamar an yi shaping din, to gwanda ayu hakan, aiko nan take Adda Suwai nonoless aka dauk ma Nafee kwalliya, ta yi matuqar kyau, haka Saudat sa Salma maman yan biyu, Yaran su ma sun sha gayu, ga qamshi dake tashi a jikin su mai ni’ima kowa son daukan su yake, Shamsiyya, Innarmu, Goggo Sarai Mama Bilki da sauran dangi sun sha kwalliya suma, amma ance ba za a je sa iyaye ba, nan fa Goggo Sarai za a fidda halin “ni dai gaskiya ko su Bilki ba zasu ba ni a tafi dani, dan nasan irin wajejen nan akwai kwalama” wani kallo Suwaiba ta mata, ” Haba Goggo har zuwa yaushe zaki daina wannan halayen ne?” Sinne kai tai tace” Yannan wasa dama nake ina ni ina zuwa wajen matasa” kuma a qasan rai dai ana son zuwa????fita tai daga dakin tai wajen masu soyawa amarya kaji da za a tafi kaita garin Kebbi, dan hanya akwai nisa, ba tsaywa siyan abu a hanya zasui ba, kuma a cikin garar ta Jabeer yace a saka harda kajin, can ta nufa tace” wannan biki nanarziqi ne in ban ci a wajen ninner din ba na ci anan”( dinner). Kada kai Salma tai da taji me take fada, mai hali baya sake hali sai dai ya lafa,in dai abun ya shige shi.
A wajen dinner wajen ya qayatu angon Nafee ba dai kyau ba shima, sai dai Nafee ta fishi kyau da dan haske, tin da suka isa yaran Salma na wajen Suwaiba nonoless, Salma sai ta fito kamar budurwa ba mai jego ba, kyaun Saudat kuwa itama ba a magana, anan abokan ango da suke zaune kusa da shi suka qura masu ido kamar zasu sace su gudu, ana tsaka da rawa da shagalin biki ne suka taso, da dukkan alamu gidan su daya, dan kamannin da suke da shi, Sallama sukai, su kuma sika amsa, Juwairere da Adda Suwaiba tashi sukai,suna masu murmushi, su kuma suka zauna a wajen da suka.tashi din, Saudat jikin ta har rawa yake tana son barin wajen, dan a zuciyar ta nan take ta tino da Kalla, dayan e yace” Haba sarauniyat kyawawan duniya ina zaki, bayan ga sarkin ki ya iso domin ya dauke ki ya kai ki masarautar masoya?” Murmushi tayi, she us so nervous, ji take kamar ta zura da gudu, Oh duniya yau Saudat ke jin nauyin maza????????komawa tai ta zauna, tana ta wasa da hanun ta, dayan ne yace ma Salma,” Angel, da farko ni suna na Salmanu,kuma aboki ga ango, wannan yaya na ne, farouq, tin da kuka zauna anan muka sa idon mu ana ku mukaji ba zamu iya barin ku tafi ba tare da mun isar da manufar mu ba, dan da dikkan alamu ku yan uwan amarya ne ko,” cikin nuna kulawa Salma ta kalle shi dan itama sai taji ya mata,” Eh mu yayun ta ne, amma bayin Allah ba ku sammu ba baku san ya muke ko rayuwae mu take ba kawa sai ku fara isar da manufar ku, to da farko dai ku duba kuga wadan can yaran na hannun yayata”duban su suka kai wajen suka ga kyawawan yaran, sannan suka dawo da kallon su suka fada mata sun gani, ci gaba tai da magana dan bata son abinda zai karya masu zuciya gaba dayan su gwanda ai maganar gaskiya,dan ta kula dikkan au samari ne basu taba aure ba,” to yam biyun nawa ne ni na haife su, amma aure na ya mutu, ita kuma wannan yayar tawa, mijin ta Allah yai mai rasuwa ne,a yau ta fita takaba,” cikin mamaki da tausaya wa suke kallon su,dan duk yanda akai mijin daya saki Salma na da tabin hankali ko shafar aljanu, hauka ne kawai zai sa kana da mace kamar wannan ka sake ta, nan take sukai wa Saudat ta’aziyya sannan farouq yace” a gaskiya ni har yanzu ina ciki kaifa dan uwa? Dan ba zan taba barin wannan tsaleliyar ta wuce ni ba zan a sara mai yawa, domin da dikkan alamu akwai tarbiyya awajen ku” a sannan Saudat tai magana” yanzu dai kui hakuri zuwa a gama biki da komai sai kuje gida ku samu mahaifin mu akan komai, dan as for me kam wanda na san haka yar uwata ma, sai abinda mahaifin mu ya zaba mana” godiya sukai sosai kuma suka qara tabbatar da taebiyyar su, karbar No wayar su sukai, sukai sallama suka tafi, Adda Suwaiba ce ta dawo ita da Juwairah, suna zama Salma ta labarta masu komai, suna cikin addu’ar neman zabin Allah ne Muhammad din Salma ya hau kuka, kuka yake sosai har Salma ta rude kamar za tai kukan itama,miqo masu hannu suka ga anyi”hey little buddy come here” Salmanu ne ya karbe shi kamar yaron da aka bawa chocolate nan da nan yai shiru, jijjiga shi yai ya tafi wajen yayan su suna ta hira da sauran abokai, wannan ya karbe shi wannan ya karbe shi, a haka daga baya Salmanu ya karbe shi, har yai bacci a kafadar shi,cike da so Salma da yan uwan ta ke kallon shi,an gama komai za a tafi gida ne ya iso, ya miqa mata shi, godiya tai ta mai, yace” ya kk man godiya ne dan uba ya kula da yar shi ai ba wani abu bane” murmushin jin dadi tai idon ta cike da kwalla ta gyada kai tai gaba, bayan sun fita ne suka fuskanci basu da abin hawa zuwa sukai kowa da motar shi, ya zo ya faka, Yaha Jabeer ya iso dan daukar matar shi da su ne ya samu labarin komai wajen Juwairah, murmushi yai yai fatan alkairi yace mata shige to mu mu tafi dan kinga sun isa gare su nasan kuma gida zasu kai su, nima a gajiye nake, wanka nake so mai dumi,ko na murmure” murmushi tai tace “Hmmm Abu Abrar kenan na gane in da ka dosa, to yau kam a very big N-O to u saboda i am so exchausted” dariya yai yace “we shall see then, i know u can’t resist my charm”yana wani kashe mata ido daya, kauda kai tai tana muemushi, dan tabbas ta bakin nashi ne, ya san abubuwan da yake ya kwace mata dikkan lissafan da take da shi…….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button