YAN ABUJA HAUSA NOVEL

YAN ABUJA HAUSA NOVEL

Sallama tai a cikin gidan, inda ta isko ana ta daru, ita Saudat tace bazata koma ba, Suwaiba ta shirya tsaf da shirin tafiya, Goggo ta sa su a gaba da magiyar ta daure ta koma, ba zai qara dukan ta ba, Abba ya kafe shima bazata koma ba tinda bata so, Mama Bilki ce tace” Ayya Goggo tinda ta ce bazata koma ba a barta mana in aka kwan biyu kin taushe ta sai a maida ta dakin ta” Hhhh lallai yau daya kin yu magana mai ma’ana,Allah ya kaimu ta huce a maida ta” ” Kaji Maman nan ina ruwan ki da sa mana baki? To bazan koma ba din har abada, sai dai ya biyo ni da takarda ta, ke kuma Allah ya bada saa zaki ce na fada maki” juyawa tai tai daki, Juwairah qarasawa tai cikin sake sallama,ta dan duqa ta gaida Suwaiba da ke qoqarin qota ta ta wuce, ” Malama bani waje driver na na jirana” hannu ta saka a jaka ta dakko kudi mai dan yawa ta watsa mata” ga shi nan dama na san gaisuwar kenan, shine ya sa ki zuwa da wuri kar mu tafi ba a baki rabon ki ba” ta fada tare da ficewa a gidan, cikin qunci da haushi,tare da fushi irin na masi ciki in an tabo su ta jawo hannun yayar ta ta, kamar yanda ta wurga mata kudin a jiki itama wurga mata tai a fuska” ashe har yanzu baku canja hali ba? Ban zo dan wannan stupid money din naku ba, nazo dan na ga yan uwana dana dade ban gani ba da iyaye na, na zo domin zumunci, dan haka u keep ur filthy money with u it will help u some day” tai shigewar ta ciki ta bar kowa baki sake, tabe baki Suwaiba tai daga baya ta dake kudin ta ta shiga mota tana daga ma Abban ta da Goggo hannu, suka juya birnin tarayya ABUJA.
Komawa ciki sukai in da Abba yai bangaren Mama ya isko Juwairah da Salma, Salma tana ba Juwairah hakuri akan komai da ya faru a baya, tana ganin Abbam nata ta miqe da kyar yana ta zauna amma saida ta isa gare shi, hannu ya buda yau huging din ta” Abbana nai kewar ka ba adadi” ” Juwaireren Mama nima haka da jibi muke saka rana zani ni da Salma mu gan ki” turo baki tai alamar shagwaba ” Abbaaaa” dariya sukai dika,” Oh mai hali baya fasa halin shi” inji Mama, dariya sukai dikan su, nan da nan Salma da Juwairah suka qara shaquwa, hira suka shiga yi Salma ta ba ta labarin abinda ya dawo da ita gida, Juwairah akwai tausayi da saurin kuka dama,tausayin yar uwarta ne ya cika ta tai ta kuka kamar wadda aka daka, sai da ta gama ta rungume ta tace”kar ki damu yar uwa, da kin haihu zaki samu miji na gari inshaa Allah mai kudin dai da kk so da yardar Allah” ” Aa Juwaireren Mama banni da talakan ma zan zauna” ” Kaiii Salma harda ke” ” Aa nima yau tabawa nai ai, ai baki taba jin na fada ba ko? To qara’i nai na da da ban tsokane ki ba” ” to ke kadai na yarda ki ce man Juwaireren Mama, ke ma iya na sati daya kacal” ta fada cike da nuna ita din yar farin maman ta ce, dariya sukai harda iyayen su dika, anan Ammar ya tashi, da sauri Juwairah ta isa ta dakko shi, sai kallon ta yake, wasa take mai taji yana qoqarin magana, ” Mamma” shine abin da ya furta, dadi ne ya kamata ” laaaa mama yana magana dama?” ” Aa ya dai iya barna wannan” dariya sukai. Haka Juwairah ta gama yinin ta cijin jin dadi,tare sukai girki da Salma, in da suka amu rashin mutuncin Saudat kala2, ba wanda ya kula ta,haka ta qarata,ta gaji ta koma daki.

SUWAIBA MUTAN ABUJA???? taisa a buja a gajiye kamr ita tai tuqin, tana isa wanka ta fada gidan ba kowa sai masu aiki da ke bangaren su, bayan ta gama ne ta kwanta” Wawuya, yaushe zan bar wannan daula ta wuce ni, ana ki dawo kina wani ke gida yafi gidan miji, ai ni da barin Abuja dai da ziyarar ganin dangi” a haka bacci ya dauke ta, cikin baccin taji wani zafi kadan, ko bude ido bata sake iyawa ba……….
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: ???????? ‘ YAN ABUJA. ????????

          BY HAERMEEBRAERH

Sweet Ummul (Khairee) qanwata ina mai yiwa Hamman ki fatan kasancewa cikin rahamar Allah, Allah ya yalwata mai qabarin shi da ni’ima da salama, Allah ya tashe shi cikin bayin shi muminai salihai. Dukkan victims na BOKO HARAM ina mai miqa ta’aziyya ta a wajen su, da musulmi baki daya, tabbas jiya komai ya dawo mana sabo, kamar jiyan akayi, My Sawwama Allah ya jiqan Abban ku ya mishi rahama da mu baki daya.ALLAH KA JIQAN DIKKAN MUSULMI WANDA SUKA RIGAMU DAMU IN TAMU TAZO.????

Page 22:

Yau a gidan Talle an tashi da jimami, Jummala na ta fama kwara amai, ba ko qaqqautawa, Huwaila na kwance kamar ruwa, gashi ta dashe tai wani fari fauuuu kamar Mero???? gaba daya wanda ya san ta da ya ganta yanzu ba zai gane ta ba sai an mai bayani, sai zubda yawu take a jikin gini,” wato ku qananan ‘yan iska ko, uban wa kuka bude wa qafa har gaba dayan ku ku biyu ace ciki ne da ku, yau in mahaifin ku yaji ya zanyi da raina, wannan abun kunyar ina zan kai shi a garin nan?” Marka ke magana tana share kwalla, shirun da sukai mata ya bata mata rai matuqa, sun ma mai da ta yar iska kenan ko, miqewa tai bayan Jummala ta koma daki in da Hawaila take, ta dakko mabirgin ta zankadede tai dakin ta rufe qofa, ji kake tim tim, tana jibgar su, ita Huwaila ba kwarin guduwa sai baki, nan take ta ko fara magana” Allah marka ki kyale mu ai iskanci ba kan mu farau ba, kuma naga iyayen yaran na gida ne, su bangis ne, kakan su na gidannan shima yana zuwa lalubar ki duk daren duniya baku ko gajiya ko daga wa juna qafa, mu ki daina dukan mu, dan naki bai fito ba namu ya fito bazaki kashe mu a banza ba, kk qara dukan mu sai na fada ma Baban mu in ya dawo kuna kebewa keda yayan shi” qam taji an qame mata bakin nata, rufe bakin ta Huwaila Marka tai bam tana waige2, tana kallon qofa, ko wani yaji? Jitai an banko qofar da mugun qarfi, wani tsoro ne ya kama ta ba ta san sanda wata muguwar tusa ta kwace mata ba, zama tai kusa da yaran suna ta toshe hanci dan azabar wari, Talle ne idon shi ya kada yai jawur akan na da, in aka ce xai iya kisa a wannan halin ba za.a musa ba, damqo wuyan Marka yai kamar zai kashe ta, ya jawo ta tsakar gida yaran su na biye, qananan na kuka manyan da suka ji kuma suka gane me ake suna mamakin abun, har qofar yayan nashi ya je ya wurga mai ita a jikin shi, daidai ya fito da tabarma a hannun shi zashi zaman qofar gida na safe da suke yi, janye jikin shi yai yana wani ja baya ” Subhanallah,meye haka zaka raban matar ka a jikina, bayan kasan ba muharrama ta bace” wani gigitaccen mari Talle ya hankada mai, zai magana ya qara make shi ya tintsira, ya kasa magana ma, zaman yan bori yai a wajen ya hau kuka, kuka yake suma kuka suke, gaba daya sun kasa daina shiru, wani haushi ne ya kama Talle kukan uban me suke, kuka ai shi ya kama, miqewa yai a haukace ya bisu da duka, duk wanda ya samu ya maka, har yayan nashi, bakin shi dai kam kamar wanda aka rufe, tattare wa nai nace bari nai Abuja in sun gama dake2n na dawo naji ya masu ciki?

Allurar bacci yai mata ya tsaya akanta yana qarewa qirjin ta kallo, qiji a cike a tsaye, amma haka za a je a yanke su, ya roqe su tinda yana son ta a mata yanda ba zata mutu ba, a mata kamar za ai operation ne yanda daga baya zata ji sauqi, su ci gaba da rayuwar su, hawayen tausayin ta ne ya zubo mai for d first time in his life yaji tausayin wani da zasui aiki akan shi,hawa gadon yai ya rungumo ta ya dora kan shi a qirjin ta, wasa ya shiga yi da su, kamar zai cinye, da kyar ya hakura, ya dauke ta yai mota da ita, ya fara daukan dajin su Oga Zaks. Hankalin Alhj Kalla a tashe yake ganin rashin dawowar Saudat, ya zai yi yau? Ta ina zai fara samo wadda za sui aikin akan ta, tinda ita ta gudu taqi dawowa? Anya ma zai iya kyale ta haka? In yace zai mata wani abu.asirin su ne zai tonu, duk da yana da tabbacin ba yanda za ai dasu, dan manyan qasar sun daure masu g…. a haka dai yai ta tinani sai da Alhj Salihu ya mai waya yace shifa ya dau hanya, tambayar shi yai matar shi ta dawo ne shi? Ya tabbatar mashi da dawowar ta, miqewa yai ya ce” duk wanda yaci ladan kuturu dole ya mai aski” waya ya zaro ya kira Yar Gwal, tana wani rawar kai da jiki yau da sa’a ta tashi ta san a bata samu ba zata samu dubu dari biyar, to me ta manta? Da hanzari ta tashi ta hau shirye2n fita, qawayen ta ne suka fara tambayar ta ina zuwa da safennan, bayan qa’idar su fitar dare ne? Sanar da su tai inda zata, shewa suka dauka wasu kuma suka.tabe baki, a haka ta gama shiri.ta fita, a qofar gidan ta same shi ya hadu cikin manyan kaya mai irin nasu na zuwa gidan Oga Zaks, shigewa tai ta fara mai karuwanci da shafe2, biye mata yai dan yana buqatar hakan kan su isa, a motar suka samu nutsuwa,yace “ya kamata yau na kaiki wajen shaqatawa na musamman mui satia can ba mai takura mana ko ya neme mu” wani juyi tai da mazaunan ta a kan cinyar shi ta sakko ta zauna a gefenshi amma rabin jikin ta na nashi, tana sauke nunfashi, cike da kissa, murmushi kawai take, dan Alhjn akwai kai mutum duniyar sama, gaba daya jikin ta a mace yake, haka suka dau hanyar dajin Oga Zaks, suna isa motoci ne ba iyaka, bayan su isa je taga mata kala2,maza duk shigar su daya, mata kamar guda bakwai, wasu da gani na aure ne, wasu irin ta ne, haka ta ga suna wata irin gaisuwa, sannan suka shige ciki gaba daya kamar su ake jira, harda wadan da basu zo da matan su ba ma, wani qaton waje taga sun nufa , kan su isa taga dukkan Alhzawan nan da suka zo da mata, sun dakko wani red yadi sun nuna masu suna kalla har ita sai suka zube a qasa, ita dama Suwaiba oganniya ta dade a sume, daukar su sukai suka aje a wani gadaje da aka tanadar masu, Oga zaks ne da sauran mutanen wajen kowa ya cire kayan shi, haka suka tsaya ba kaya a jikin su, aka dakko wuqa, kowa ya kama wadda ya kawo, Alhj Salihu ne ya zo gaban Suwaiba, zuciyar shi a cunkushe, ji yake kamar ya bijire ma Dodon nasu,amma tinawa da azabar da zai shiga in yau bai wannan abun ba, kawai ya saka ma nonon Suwaiba wuqa, haka suka yanke masj Nono dukkan su suka tari jinin a wasu qorai qanana da suka rine da jini, kuka Alhj Salihu ya fashe d shi da yaja hankulan mutanen wajen, kowa daya kalle shi, ga uban ciki a gaba, ga baqi da yai yana maiqon zufa, sai dariya ta kama su, suka dinga dariya, saida Oga Zaks ya daka masu tsawa suka nutsu” Me yasa ka kuka Salihu?” Oga Zaks ne yai wannan tambayar,” ina son matata Oga a san ya za ai a mata aiki a shafe wajen kar ta mutu , ka taimaka min Oga.kumin alfarmar nan oga” dariya sosai Oga Zaks yai sannan yace” karka damu i will keep my word ai , ni nace maka zamu san ya zamui matar ka baxat mutu ba, ita waccan guduwa tai ne?” Ya maida tambayar kan Kalla, ” Eh Oga, da suka tafi ganin gida qin dawo wa tai ita” ” ba damuwa yanzu dauke ta kui dakin duba marasa lfy da ita” da gudu Salihu ya dauke ta sukai can ya shimfide Doctors biyu ne suka hau kula da ita ya koma wajen tsafin nasu, jinin suka sha akai ta bayarwa wannan ya sha ya ba wannan, a haka suka gama suka rage dan kadan suka zuba a wani waje da naga sun qawata da ado suka zuba wa jinin nan danan ya tsotse kuwa,haka aka kammala komai sauran matan aka tattare su suka kai su wani daki baqi, ita ko Suwaiba da aka kammala bashi matat shi sukai ya saka kayan shi ya kaita mota, hanya suka dauka yana kuka hankalin shi tashe, Kalla na biye da shi a motar shi hankalin shi kwance, horn yai ta mai yanda suka saba in zasu rabu amma bai mayat mai ba, kada kai yai yaga ba ma amfanin komawa gida kawai bari ya tafi club, karkata motar shi yai ya tafi, sun isa gida ya dakko ta ya shiga daki da ita, kan gado ya aje ta, ya zuba mata ido yanda ta dashe tai fari alamar ba jini sosai a jikin ta, kwanta wa yai kusa da ita, ya rungume ta, a haka yai bacci, ba shi ya farka ba sai sha daya na safiya wanda ta sanadin motsin Suwaiba ne ya sa shi tashi, tash tai zata miqe taji wani sharp pain a qirjin ta , komawa tai ta kwanta cikin zubda kwallah, ji take kamar an yake naman wajen dan azaba, ni ko nace ba kama bane Suwai matar manya????
Baki ta bude tace…..
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: ???????? ‘YAN ABUJA ????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button