YAN ABUJA HAUSA NOVEL

YAN ABUJA HAUSA NOVEL

Saudat ce na hango ita da angon ta suna ta zagaye gidan suna guje2 cikin tsantsar so da qauna tare da begen junan su, wani irin shaquwa ce ta musamman a tsakanin su,tare da tausayawa juna, dan suna cikin gudun ne santsin tiles ya kusa kwasa Saudat a qasa, amma da ikon Allah sai bata fadin ba, ta dai tsorata ne kawai, da hanzari ya isa gare ta,yana wani juya ta” Sweet one baki ji ciwo ba,ta ina kk bige??” Kamo fuskar shi tai gaba daya a hannun ta, ta matso lips din shi irin yanda mutum zai iyayi da hannu ko da bakin shi ya tsuke su sui tsini, haka ta mai itama, sannan ta kai nata bakin tai kissing din shi, sai da taga suna neman faduwa ta tsaya” me ma kk tambaya ta dazu?” Ta fada cikin qunshe dariya,da daga gira,cikin in-ina ya fara bata amsa” Ammmmm….. immmm…. damaaa… cewa… nai…. imm…. can u pls kiss me again” dariya suka saka sosai har tana riqe ciki,daga ta yai ta bayan ta cikin nata suka samu wajen zama a kujerun nasu, bayan ya kwantar da ita a kujerar ne ya kwanta ta bayan ta,ya rungumo ta ta ciki,suna ci gaba da dariya, a hankali sukai shiru yana mata wasa da gashin ta” Babe me yasa baka damuwa da batun rashin haihuwar da kasan ba zan yi ba, saboda rashin mahaifa, bayan kai baka taba aure ba, ar u planning to have another wife ne nan gaba?” ” My dear ina so ki san cewa da auren da haihuwar duk nufin Allah ne, tayu a baki da mahaifan mu haihu, ta yu ba za mu haihun ba, to ina son ki sani, haihuwa is a blessing that everyone will love to have it, amma ni bana daga cikin wadan da suke ganin in mace bata haihuwa bata da amfani,to ina soyayyar da yake mata? Dama dan Yara kawai ya aure ta? Ita ce take ba kanta? Idan zan maki kishiya saboda baki haihuwa tabbas na zama daga cikin azzalumai, na kuma zama daga cikin masu butulci ga Allah, domin ya min kyauta countless, to me zai sa dan akan abu daya danaoe so ban samu ba na mai butulci? Ba zai yu ba, daga ranar da kk ji na qara aure Saudat ban qara shi dan baki haihuwa ba ne, sai dan itama ina son ta,kuma Allah ne ya halatta mana qara auren, dan haka ki kwantar da hankalin ki ni ba mai ra’ayin tara mata bane, bana.son hayaniya, bqn son takura, mata da yawa na saka ni damuwa dan bana son raba fada kullum,” ya qarasa ta yanda tabbas yasan hankalin ta ya kwanta da maganganun shi, amma hawayen dadi sun kasa tsaya mata, tabbas Allah ya azurta ta da namijin gaske, Allah ya qara mai hakuri da juriya akan hakan ta ayyana a ranta, ci gaba da shafa wuyan ta zuwa bayan ta yai ita kuma tana wani miqewa tana juya jikin ta anashi, tini ta burgita shi,ni kuma na ja sayyarar qafata na waje a 100????

“Ki taho da fidar yarannan, da tissue love” amsawa tai shi kuma ya zauna yana masu wasa, bayan ta iso ne ta zauna kusa da su,” ni dai gaskiya ban yarda ba nima sai an min wajen zama a nan, dan wayo kullum ni a qasa ko gefe su a cinya”ta fada tana turo baki,dariya ce ta kama shi, sai ya dauki Muhammad ya dora a wuya, sannan ya dago ta ya saka a cinyar shi,murna ta saka tana mai kiss a kumatun shi, ” Na gode na zaci ai ce min za ai nai hakuri yaran su zauna da ba zan yarda ba sai dai a maida su daki ni na hau” ta fada tana sauka, dariya yake sosai, dan Salma ba dai kishi ba, kishi take da yaran nan sosai , dan gani take gaba daya ya kwashe soyayyar ta ya basu, lokacin shi gaba daya nasu ne in yana gida, amma a qasan ranta ba qaramin dadi take ji ba, hankalin ta a kwance yake dan bata tsammaci hakan a wajen saurayi da bai san ya zai gama kula da kan shi ba bare wasu yaran har biyu, kujerar basu abinci ya saka su,ya dorawa kowa a gaban shi, ya basu cokula a hannun su na dama,sa kyar suke riqewa saboda rashin iya hakan, amma yana tsaye in zasu karkace ya gyra masu, ta baya ta ziro hannun ta ta tsugunna itama ta kwantar da kanta a bayan shi ta furta”I love u” shima waiwayar da kan shi yai suka hada ido yace mata” i love u more” kiss ya mata a goshi ya juya ga yaran su( da na kowa ne, baka san wa zai more shi ba, dan haka bahaushe yace, da da dukiya ba a masu mugunta, in ka lalata wataqila kai zaka amfana a gaba,ka bata to da me zakai amfani, in ka gyara kuwa ka amfana, wani ma sai ya gama gyarawar ya zamana ba shi zai mora ba ya gyarawa al’umma ne, ladan shi na a wajen Allah, wani kuma sai ya bata ya mutu ya barwa al’umma annoba, yana qasa ana rubuta mai zunubin mummunan upbringing da ya ba wani,mu gyra duniyat mu lahirar mu ta amfane mi)

Talle ne ya shirya tsaf da yar jaka a hannun shi, wadda ta qunshi kayan yara mace da namiji dan bai san me Salma ta haifa ba, incase ko wace gender ta haifa za a samu na ta kayan, sallama suke da Marka inda qasan ranta kishi ne danqare, amma yanzu halin ta mai kyau data koya ya danne kishin, miqamai leda tai da ta daka kuka daddawa, sa kubewa, tace ya kai masu, godiya yai mata,Huwaila ce ta leqo da gyada soyayya itama dan sana’ar ta kenan yanzu, tq bashi tace ya gaida su ya nema masu gafar ta, amsa yai ya sa kai……

To masu karatu Talle fa yai shiri, wa zai bishi ya fada mai bata gidan kar yai wahalar banza????
[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: ???????? ‘YAN ABUJA ????????

        BY HAERMEEBRAERH

Page 35:

Talle ne ke ta kwada Sallamah a qofar gidan su Salma, da ga can Ammar ne ya fara leqowa, like a big bo he is, da tsamin bakin shi yake tambayar wa ake nema, yaro yana da kaifin hankali, shekara biyu da watanni amma akwai qoqari ga karatun qur’ani a bakin shi tar, na bokon iyakar shi A B C D, sai counting da Mama Biliki ke dan koya mai, komai akai yana sane da shi kuma yana ganewa, murmushi talle yai, aranshi yace wannan yaro da ya dan da Salame zata haifan ya kai shekarun shi ai sai nace dana ne suna kama, ” Yaro ina malam,” ” faya nan” ( Baya nan), Talle ne yaga yaron ya kalli gaban.shi yana dariya ya fita da gudu yana ” Abbana Oyoyo” shima wajen ya kalla sai yaga ashe Abbam su Salame ne ya dawo, saurin isa yai wajen shi, inda gaba daya Abbam ya sauya fuska, daga fara’a zuwa bacin rai, ” me ya kawo ka?” Tambayar da ya wulla mai kenan” Abba dan Allah dan son Annabin rahama kai hakuri, ka yafeni, tabbas na kasance daga cikin jahilai, marasa sanin Allah a baya, sakamakon jahilcin da ya mamayi zuciyata, kuma naqi na nemi sanin Allah da dokokin shi, ina jin girman kai, da ganin na wuce wajen ai, hakan tasa na aikata munanan abubuwa a rayuwata, kala2 wadan da naga isharar su Abba, babbar isharar shine mutuwar ‘ya ta, kama dan uwana yaya na da mata ta suna zina, daya ‘yar tawa ga ta can da dan gaba da fatiha, ga abinda ke dagan hankali rabuwa da Salame d nai, ta tafi da cikina na rabunda ita rabuwa cikin rashin tausayi da imani, a yanzu nayi nadama, na koma islamiyya ni da iyalina dika, ka yafe min ba dan halaye na ba sai domin Allah” kalaman shi sun saka jikin Abba yai sanyi amma ya wuce cikin gida kamar bai ji shi ba, yana shiga Mama Bilki ta sauke shi da ruwa da abinci, ga kuma ruwan wanka ta kai mashi,tana goge masa zufa ne tare da jera mishi sannu da zuwa cikin rattausan lafazi, umartar ta yai ta kira yayar tata,miqewa tai ta tafi, ta kira Goggo Sarai da tai zurfin a cikin tinanin baya, yanzu da hankali ke qara shigar ta, ba qaramin kunyar Mama Bilki take ba, tasowa tai kamar wadda kwai ya fashe ma a cik, ta biyo ta, ” Gamu Abban su” dagowa yai ya kalle su cikin sha’awar yanda suka koma a nitse ba hayaniya ko mummunan kishinnan, Ammar ne yaje wajen Goggo Sarai ya zauna a cinyar ta, shafa kanshi tai tana mai murmushi, Abba labar ta masu komai yai sannaj ya sanar da su Tallen na qofar gida ma yanzu, haquri ya ba Goggo Sarai da yaga ranta ya baci, yama juyawa yaga fuskar Mama Bilki ma a bace, domin shi mijin Salma shima ba qaramin azzalumi bane kwantar masi hankali tai da dadadan kalamai sannan suka hakura, aika Ammar yai yace yaje ya shigo da baqon nan, tafiya yai ya sanar da shi, Talle ya shigo qafa duk ta sage mai saboda tsaiwa, waje Abba ya matsa mai kan tabarma, tayin abincin ya mai Goggo Sarai ce ta qaro ruwan sha da wani abincin, ci sukai suka qoshi, sannan Abba ya kira su again, ” da farko dai ina son sanar da kai dukkan mu nan iyayen Salma mun yafe maka, kuma muna saka ran itama ta yafe maka, tabbas ka cutar mana da yarinya, ka zalumce ta, amma duba da cewar muma masu zunubi ne a wajen Allah kuma mu roqe shi ya yafe mana, banga dalilin qin yafe maka da zamui ba, daga qarshe ina mai sanar maka yanzu haka Salma na Abuja gidan kudi gidan hutu ita da yaran ka dan biyu ta haifa, kuma ta samu miji saurayi ya dauki yaran kamar mallakin shi, ni ba zan sanar da kai ina Salma take ba a yanzu dan ta fara samun farin…….” ” ban katsi nunfashin ka ba Abba, amma tabbas nima ba zan so abinda zai hana ta farin ciki ba a daidai wannan lokacin, tabbas, na amince su ci gaba da rainon yara na, lokaci zuwa lokaci zan dinga zuwa nan din, ana gaisawa,ga address dina saboda wataran ko za a buqaci hakan,” takardardaya rubuto tun a gida ya zaro ya miqa ma Abba, idon shi ya kada yai jawurr, tabbas har yanzu akwai son Salma a ran shi, wanda tin da ya dauka sha’awa ce kawai, miqawa Abba ledar Hannun shi yai ya mai sallama dan komai dare gida yai, ya ma yaran shi addua, an nuna mai hotunan su, inda Mama Bilki ta dakko mai wasu ajiyayyu tin na jarirantar su,har randa zasu tafi, hawaye kawai yake sharewa, duk yaran shi ba mai kyaun wadannan da ya koro, dan duk macen da ya aura in zata tafi sai ta dire mai da ko yar shi, ko in taje gida ta haihu zata dawo mai da shi, Haule ce kawai take itama kyakkyawa saboda uwar ta, yana tina ta sai zuciyar shi ta qara tsinkewa,ya kula yara uku ya bari yanzu, amma wannan na daga cikin horon da Allah zai masa ya raba shi da yaran da yafi qauna, tashi yai bayan ya sake masu sallama ya isar da saqon su Huwaila,godiya suma sukai masa, ya kama hanya sai qauyen su.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button