YAN ABUJA HAUSA NOVEL

YAN ABUJA HAUSA NOVEL

Cikin dare Salma taji kamar buga qofa ake, a hankali ta miqe ba tare da tai wanai kwakkwaran motsi ba, dan tare suke kwana da Haule yanzu, leqawa tau ta qaramar qofa ta bular ta hango wan mijin nasu na waige2 yana kwankwasa qofar Marka, mamaki ne fak cikin ra dan duk yan kwanakin nan mark ke zuwa, yau fushi take da shi, daren jiya ya hana ta dari da hamsin da ta roqa yace bai da su, shine tace yau ba za ta ba, shi kuma gashi a mugun matse yake, hannun shi na kan wandon shi, haka yake kwankwasa qofar, budewa tai tana magana qasa2″ Dalla can sai ka tada yaran ma sun gan ka, ni shigo kayi ka gana ka tafi” jawo shi ciki tai ta wandon shi, aiko akan idon salma, kame baki tai tana fadin ” tab ashe wannan matar munafuka ce? Ba ta da maqiyi da rana kuma bata da masoyi da dare da ya wuce Babam bangis, lallai ran da Su Badamasin suka sani akwai case” tana cikin wannan tinani ta fara jiyo qarar dan qaramin gadon na Marka irin na qarfen nan, sannan ga sambatun ta nan da bata iya shiru ita sai ta tona masu asiri, yaran akwai nauyin baccin tsiya, to an wuni shiririta kuma anyi bacci late dole in sun kwanta kamar gawwaku, Marka a wayon ta hade yaran take dika daki daya saboda irin haka, kafin Salma ta zo ne dakin ta yake na Yammatan, amma kawo ta yasa aka hade su, motsin qofa Salma ta ji zai fito sai da ya fito Marka ta biyo shi tana miqa tana gantsaro girji, shi kuma yana qara shafawa” kamar na koma mui ta yi sai asuba na tafi” ” lallai Yaya kaima a gaida ka, duk wannan aikin da garar da ka diba bai ishe ka ba, in kana son ka koma ciki qaron nera daru kacal” murmushi yai haqoran shi jajaye suka bayyana” Aaaa dari tab na gama baki dari ukun yau, ni dai gaskiya ban da su” ” to kuwa kama gaban ka ka wuce ya ishe ka haka a barwa gobe” yana qarasa fitowa gaba daya Salma ta fito da buta a hannu ita ma , hankalin su ne ya tashi, gaba daya da ganin ta” Salame dan Allah ki rufa mana asiri, kar kowa yaji labarin nan” suna hada baki suka fada” a nawa zan shiru ko ko haka nan zan rufe bakin nawa kuke nufin” kudi ya dakko dari biyar guda biyu ya miqa mata” sauran naki kema, da sauri ta shiga daki ta dakko dari biyar ta hada dana hanun ta ta bata, ” sannan ina son ki sani Talle ya kusa dawo wa dan jiya baki nan kina yawon ta xubar Badamasi ya fada sun yi waya, in ya dawo kk kuskura na ganku tare har kk hada jiki da shi warin ki ta mannu a jikin shi saina fada mai, dan ba zaki sa yanda ni na tsare aure na ba ina juran ya dawo mu raya sunna ki ja min amai ba kuma ba biyan buqata, kinji ni ko, wani yawu ta hadiya na yau ta shiga uku an raba ta da gwarxon maza, tace” na gane kiyi wa Allah ki rufa mana asiri” ” baku da matsala in ma komawa zakui sau asuba din zan iya maku gadi” Aaaaa ni na ma ta fi yannan” fakam fakam Yayan Talle ya bar sashen nasu, ita kuma ta koma daki ta bar Marka da cizon yatsa an amshe yan kudaden kuma ba wai itama ta qoshi da abun bane, yau tayi biyu babu, tura qofar tai ta koma, Salma me zatai ba dariya ba yanzu sun dawo hannun ta kenan da taji tana son kudi zata neme su kuma dole su bayar ko ta tona su, wani muna tai ta dale gadon ta ta miqe.

Yau shamsiyya qawar su Juwairah da Nafee ta kawo ma Juwairah ziyara dan tana son ta qara bata wasu shawarwarin game da yanda zata gyara nonon ta da suka lamushe kamar an yi gobara ta ciki an yashe komai sai fata, sannan ga kanta dake yawan karyewa gashin ta na zuba, abu mafi mahimmanci da zai kaita ta taya su murna dan Nafeesa ta bata labarin samun cinkin da tai, murna take sosai itama da jin hakan. Shiryawa tai bayan ta gyara gidan ta tsaf kamar ba ita ba ta fito ta hau abin hawa har gidn su Juwairah da Nafeesa bayan ta sauka ta sallami mai adaidaita sahun ne ta shiga ciki, bangaren innar mu ta fara shiga, bayan sun gaisa ta mata murna ne ta shiga ciki , wajen Juwairah, a can ta hango Nafeesa tana alwalar la’asar, Juwairah na daka tana gabatar da sallah………
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: ???????? ‘ YAN ABUJA ????????

   BY HAERMEEBRAERH

This page is for u SWEETHEART, Sis Juwairiyyah, u ar d best sister that one could ever ask for, i love u so so very much dear, u ar d best.❤❤❤❤❤❤❤❤

Page 14:

Itama sallah tai domin da alwala ta baro gidan ta, tasan lokaci zai mata hakan, bayan sun idar ne suka hau gaishe gaishe, Juwairah na tsokanar Farha akan ta girma ta isa yaye,” hmmm ke dai bari sis abinda na ke son ki ban shawara akai sis, ya zan dan nan da sati uku nake son yaye ta, nono gaba daya ya koma slipas b kyaun gani, ya barni da fata, duk nankarwa a jiki, ga cikina ma nankarwa tun na haihuwa, dan ma Allah ya san Abban su mutum ne mai kawaici baya son ya bata raina amma ba namijin da zai so hakan, dan kan ya koma hakan na kula yana matuqar son wajen” ” sister kin ko kawo kuka wajen maganin ki” dariya suka saka Juwairah tace” Nafee kina ban matsayin da bai kai nawa ba Allah” ” no ba haka bane dear a gaskiya kina burge ni wajen hangen nesa wallahi na san ba komai bane ya jawo sai mai da hankali da kikai kk koya wajen Mama Biliki da muna ganin kina ‘yar ta amma tana baki wahala ke ke komai a gidan gashi yana maki amfani” haka ne kam, dan ko ni a da watarab sai naji na gaji bana son taimaka mata, data fahimci haka bata mun fada amsa take tayi takan ce jiki da jini, ti tanzu dai kin san me zaki yar uwa na farko ki nemo wadannan garin maganin ki fake su waje daya ki samu alkama ji qarin ta kina kunu kuna zubawa ko da madara ko ba madara, zaki iya sha, ke ko a ruwa xaki iya sha amma yafi kyau a alkama da madarar musamman ta shanu, magungunan sune kamar haka, NONON KURCIYA, GANYEN BAFULATANA, GADALIN NONO, su ne abubuwan ana samu a wajen masu saida maganin mata, sai kuna na biyu mai sauqi kuma yana yi sosai shima, wanda zaki samu farar shinkafa, ki wanke ki jiqa akai markade ta zama kamu, sai ki daka bagaruwa da ake tsarki da ita, ki na dibar kadan ba mak yawa ba kina yin kunu kina sha, zaki iya saka madarar shanu ko ta ruwa in babu zaki iya shan shi haka, banbancin su wancan in ya karbi mace yana dadewa a jikin ta, sosai, sannan kuma ba a son qiwa kiyi yau kiqi gobe sannann ana son ayi kamar na wata daya, zuwa yanda nonon ki ya lalace, bangaren nankarwa kuma ki samu, man kade(wanda ake shafawa faso ko kaushi) sai kina shafawa a cikin ki da kuma nonon da dai in da kk san akwai nankarwar(stretch marks) kinji wadannan a sauqaqe kenan”” kaiiiii amma wallahi yar uwa na gode sosai, Allah ya saka miki da alkairi, Allah ya sauke ki lfy, ya bamu bby mai albarka,” sunkuyar da kai tai a ranta ta amsa, ” Dalla in zaki amsa ki amsa ba ma son gulma kikai cikin ma” ” sannu Nafeesa sarkin rashin kunya na gode dani kk wannan maganar tin da ni nayi” cikin kaduwa Nafee ta hau zare ido, tama kasa magana, su kuma dariya da kunya ce ta kama su musamman ma Juwairah ashe Yayan ta duk yana jin su, tashi tai ta ja labulen ta fita wajen shi kai a qasa” sannu da zuwa mine” ” yawwa princess, how ar u feeling,now?” ” i am kind of k, amma fa kaina yanajuyawa kuma cikina na motsawa sai nai ta jin tsoro kuma abin na min daban haka” ” ki ta hakuri kinji princess u will be fyn inshaa Allah, kawai hakurin nan naki dana san ki dashi zaki ci gaba zamu iya komai we can get thiugh it all” murmushi tai, shima haka yai kissing bayan kunnen ta a hankali, sai da yasa tsigar jikin ta tashi, ” yanzu tinda shamsiyya ta zo bari na je wajen Innar mu na yi hirata nima” gai da shi shamsiyya tai ya yi ma Farha wasa ya tafi, Nafeesa ta aika da abincin shi da komai, da kyar ta karba dan kunya da tsoron Yayan nata, dariya suko sukai ta mata,bayan ta dawo ne ta ce” laaa Matar Yayah na hada mana zogalen da ramar?” ” kaiii amma Allah ya miki albarka, pls do” ta shi tai suka je Nafee na hadawa suna hira ta saka komai zata yanka albasa kenan, Juwairah ta dakatar da ita” Nafeesa kar ku sa mana albasa sai dai a naki dan mu muna da masu shinshinar bakunan mu, ehe, baki san ba a son in yamma tai mace ta ci albasa ba? Dan haka ki kiyaye ko ke zaki in miji na gida ki hakura da albasa,in ko kinci ki tabbatar kin wanke bakin ki tass yanda ba yanda za ai ya ji warin ta” godiya suka sake mata dikkan su shamsiyya tace” lallai zan yawai ta zuwa gidannan don na samu sirrin da yasa baki taba fada da mijin ki ba kuma kk iya controlling din shi haka” ” hhhh haba shamsiyya ai mace bata controlling miji sai dai ya zamar mata bawa a lokacin da itama ta zamar mai baiwa, na miji ba ya sanin ya zama maki bawa sai dai yaji mutane na cewa ya zama mijin hajiya, ko mijin kan tace, da sauran su, babban abinda ke jawo ma mace hakan kuwa shine, neman soyayyar Allah makadaici, in mace ta nemi soyayyar Allah, ta kuma samu ta gana da na miji, wanda hakan yai qaranci a cikin mu mata, daga wajen boka sai dora rai akan, maganin mata, bayan ba su kadai ne ke riqe zaman aure ba, wallahi in Allah ya so mace ta gama samun dacewar duniya da lahira, dan haka ni sirrina na zaman gidan aure shine son Allah da neman Allah ya so ki, saka soyayyar namiji a saman ta Allah shi ke saka mata fadawa halaka, daga zuwa wajen boka, zuwa zinace2, da dikkan abin da ya kauce hanya dan haka ina horon ku da neman soyayyar Allah, wani irin dadi ne ke ratsa su dikkan su, musamman Jabeer da ya kawo kwanuka da niyyar yin alwala yai tafi masjid, wani irin dadi yaji yakuma godewa Allah a zuciyar shi sosai da samun mace kamar Juwairah, suma sallah sukai, suka raka ta ta hau abin hawa ta tafi, tana cike da farin cikin samun qawa kamar Juwairiyya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button