YAN ABUJA HAUSA NOVEL

YAN ABUJA HAUSA NOVEL

A yan kwanakin nan kusan kullum sai ya zo, ana haka Salma tai wani saurayi mai kudi shina ya fada mata a Abuja yake da zama, kuna shi sana’ar saida motoci yake, kullum in zai zo ya vaza uwar riga ya shigo mota mai tsada ya zo amma fa ba ko sisi, wataran ne ma zai dan samu ya siyo mata yar shawarma kamar mayya tana rawar kai saurayi ya siyo mata abu ta amshe ta shigo,itama tini ta i sahun manyan ta amsar kudin maza da basu jiki ai tabe2 , alhajin dai dake son ta shima ya matsa zai turo sanda ya turo magabatan shi sun sha mamakin ganin daya daga kayan da ya taba zuw da su da motar, amma suka basar, a tinanin su wata qila anko sukai????………
[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: ???????? YAN ABUJA. ????????

BY HAERMEEBRAERH

Page 3:

A haka aka karbi kudin auren inda gaba daya aka saka ranar auren su nan da wata daya, gori kam da baqaqen maganganu ba irin wanda Juwairah.bata karba ba wajen yan uwan ta, tin tana kuka har ta kai ta daina sai dai ta kauda kai sui tayi ranta na quna, takanji kamar ta ce Ya Jabeer ya fito ai auren. Wata rana ta na zaune tana yanka alayyahu ma Maman ta sai Adda Suwaiba ta fito ita da Salma, ” hhhhhhh Adda dan Allah ki ga yarinyar nan, a kyau dai duk gidanan albarka tafi kowa, ta tsaya ta mori kyaun na ta amma tanaiwa kanta baqin ciki tsabar mugunta , ban taba ganin irin wannan yarinya va” hmmm ina ruwan ki uwar kinibibi taje ta auri wanda ta gadama ma ba Jabeer ba, danni wallahi ba kyau ba ba ilimi ba in baka da farare bugun Abuja, sannan ba zaka auren ka kaini Abuja ba wallahi kayi kyaun banza da kyaun halin wofi, dan ba su zan ci ba” dariya sukai sina riqe baki, alamun sun ma ta rashin mutuncinnan, girgiza kai tai tace” Adda Suwai kenan, ina kyautata zaton kun manta wa keyi, sannan kun manta dawa kuke jayayya, wanda duk zai wa wani gorin talauci to y sani ba da wannan bawan yake ba da ubangijin bawan yake, beside ba fa kusan sana’ar mazajen ku ba gaba ki dayan ku damuwar ku kawai a kai ku Abuja, ku matan Abuja ne, matan manya, bana maku baqin ciki, zanfi murna ace kuna gidan hutu dan nima ina ma kaina fata, amma zan baqin ciki ace baku da alkibla saita kudi da son abun duniya, Allah ya kyauta, ammmm for ur information, ni haka nake son Ya Jabeer ba dan dukiyar shi ba ba dan komai ba , Son shi ni kaina ba zan ce ga daga in da ya fito ba, na tainci kaina da So da qaunar shi ne kawai dan haka wannan matsalar ku ce wai rashin kudin shi, tinda ya zama jinin jikina ba zan iya rayuwa ba shi ba kun ga ko ko a wanne hali yake zan iya zama da shi” Tafi taji ana yi mai cike da shauqi idon Jabeer tap kwallar dadi da murna, Mama na daka tana mamakin yar ta ta, lallai yau an kaita maqura,daga kai tai tagan shi yana qarasowa gaban.ta, wata irin kunya taji ta lullube ta da ko guduwa daga wajen ma kasawa tai, dan tinda suke bata taba zayyane mai yanda take son shi ba, wanda da damar masoya shi ke dakushe ma su amashin soyayyar su, kafadun ta ya riqe ya juya ya kalli su suwaiba, inda suka qame qam suna wurga idanu, ” Princess wadannan kalaman naki sun qara dasa man zazzafar qaunar ku da son ku akan na da, ba zan iya rayuwa ba ke ba, dan haka nake roqon Abba da ya taimaka ya auran ke nima a hada gaba daya da na wadannan fitsararrun marasa tarbiyya, ba dan komai ba sai dan a kafa tarihi tare kar muzo lissafi yana kwace mana” murguda baki Suwai tayi tana qunquni tai daki, tsugunnawa yai ya ci gaba da taya ta aikin ita dai kunya ta ishe ta a haka suka gama yiwa mama girki ko leqawa gaida maman bai ba ita kuma ta kasa fitowa dan komai akan kunnen ta akai, Abba ne ya shigo da sallama bayan sun amsa ne yace” Aa Juwaira Jabeer yau kune kuke mana abincin daren? ” yana fada yana dariya, sosa qeya yai ita kuna ta rufe fuska ta je ta amshi ledar hannun shi, tai dakin Mamar ta da yasha gyara yake qamshin tiraren wuta na tsinke, Maman ce ta zo ta wuce su da ruwa a bokiti kanta a qasa dan yai yaran sun bata kunya sosai, Jabeer ne yai dariya yace” Hajiya Maman mu yau kuma kunya ta kk ji ne? Shiyasa sai yanzu kk fitowa da kk ji Abba ko? Ai dana sani to tafiya nai da muka gama hirar tamu” sosain hannun ta ta wurga mai tana ” wannan danneman tsikannen yaron wato duk kauda kaina sai ka nunan kai dan zamani ne ko? Ai gashi kun ja min makara yin wanka sai da Abban nasu ya dawo” dariya sukai dika Abban ke tambayar me ya faru da hanzari Juwaira tace” ba…ba..komai Abba” dariya Mama da Jabeer sukai Mama ta wuce su Jabeer yace “Abba ka huta akwai magana a bakinnan nawa, ni dai in ke ba ki da abin cewa ni ina da shi” roqon shi take da ido ya bari sai gobe yau kuyar zata mata yawa, amma kanne ido daya yai yana mata kwalo sai ya fada yau, tura baki tai tai daki, bayan sun gama komai tayi wanka sunci abinci, in da wajen cin abincin ma Jabeer rashin ta ido ya so yi ta qi yarda, wai da sai dai suci a kwano daya, da taqi sai ya zauna kusa da ita, in ya faki idon kowa sai ya zura hannu a nata ya diba ya kai bakin shi yana lumshe ido, can sai yace” ke ni fa ban yarda ba ya akai naki ya fi dadi? ” Kai Ya Jabeer da rigima kk, ni duk daya ne kai ne ka ji haka” to kawo mu canjen kwano in haka ne” miqa mai nata tai ya bata nashi daya ci gaba da ci ya qara zura hannu a wancan, ” Tab in ba sai an qara canjawa ba me kk fakar idona kk sawa naki?” Yahhhhh” ta fada tana turo baki cike da shagwaba, ” wai ni da kk wannan maganar ta ya akai kasan nata yafi dadi?” Saurin tashi zatai ya danne hannun ta da nashi, ” Abba loma daidai nai a dikka” Allah yafi loma daya” ???????? ” Hmmm Abban su dan allah ka rabu da shirgin yaran nan mu ci abincin mu bana son kana wasa da cin abinci kar wani ciwon ya kama mana kai” kashe mata ido Jabeer yai ya matsa kusa da ita, daidai kunnen ta” to kinji yanda ake wa miji ko, sauran mui aure kina raba mana kwan irin haka” dariya ta gimtse,” hmmmmmm bariki, har da Yayan ake zaune ake iskanci a tsakar gida, sannan in nawa sun fita ace masu yan iska, to ai bahaushe yace, qazantar da baka gani ba tsafta ce” muryar Goggo Sarai kenan, “Subhanallahi, me kk fada ne ke ko agaban yara gasu gaba daya kin jawo su kun fito kun sani a gaba?” Eh abinda kaji na fada mana ko maimaici kk buqata na qara karanto maka?” To bari kiji mara kunya, Jabeer ya tabbatar man da auren Juwaira yake son yai, yana son a hada dana sauran ayi, dan haka wannan shirirtar taki da goregoren naki ya qare dan duk ina ji” Aiko ba wanda ya isa ya hada mana aure da wadannan yan maulan” kan ta rufe baki taji fauuu an make bakin da qarfi, saida bakin yai jini,” kan uban nan Jabeer me suwaiban tamaka zaka mata wannan dukan, ko uwar ka Hansai ba zatai ma yata hukun ci ba balle Uban ka Balarabe” wani dukan ya kaiwa Saudat dake kusa da shi sosai mai qarfi saida ta kifa, ” duk rashin kunyar da kikai ma Abba kan su zan huce ita kuma waccan hikuncin rashin kunyar da ta min ta karva” sannu uban su” inji Salma, aiko takalmin qafar shi ya cire ya murde hannun ta yaita maka mata, sai ihu take, Goggo ce taje da niyyar kwace ta, wani kallo ya mata da hantar cikin ta ta kada tai baya da sauri tana ” Allah ya isan su baqin mugu kawai” sakin ta yai ya sa takalmin shi yai waje, Abba da Mama sai Juwaira da idon ta ya cika da hawaye suka shige daki suka rufe qofa suka bar su nan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button