YAN ABUJA HAUSA NOVEL

YAN ABUJA HAUSA NOVEL

Da saurin shi ya shigo gidan bakin shi washe kamar gonar audiga, qoqarin shi bai wuce yaje ga mahaifan shi ba da matat shi, shiga bangaren Innar mu yai yaga wayam an karo qofar ba kowa, bangaren su yai cike da doki da zumudi, durqushe ya ganta gaban ta robar da ta hada zuma da zamzam ne da taiwa fatiha qafa bakwai take sha tinda cikin ta yai wata takwas dan samun sauqin haihuwa, ta shan ye ya kai rabin robar, zufa ke karyo mata ko ta ina, sai addua take tana qarawa,” Allahu Allahu Allahu rabbi la ushrika bihi shai’an wa huwassami’ul aleem” shine abinda take fada taja maimaitawa, da sauri ya isa gare ta, ruwa ya fashe mata tana wani nishi na son ta sillubo koma meye a tattare da ita, sauri yai ya juya ta daga durquson sabida kar ta haihu a haka ta samu mummunan tsaga a gabanta, zaunar da ita yai ta gaba ya koma bayan ta yana qoqarin taimaka mata, dan yanda ya ganta, da yanda suke karantawa shi da uta a wani littafi na EVERY WOMAN ya san haihuwa ta zo, ba yanda zai ya fita da ita asibiti haka, suna haka sukaji sallamar Innar mu ta zo da kwadon zogale zata ba Juwairah, ai ko tana ganin haka itama ta duqa ta hau taimaka masu, nan take ta fara qoqarin nishi mai qarfi………..
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: ???????? ‘ YAN ABUJA ????????

      BY HAERMEEBRAERH

NA RIQE KU DAN ALLAH KU DAN QARA MIN HAKURI KADAN NAN DA KWANA BIYAR INSHAA ALLAH ZAN KAMMALA ‘YAN ABUJA ZAN MAYAR DOCUMENT YANDA DUK MAI SO ZAI SAMU. NA GODE SOSAI DA SOYYAR NOVEL DINA DA KUKE NUNAWA. ME LOVE U ALL❤

Page 28:

Kukan jaririyar da suka ji ne ya tabbatar masu da cewar Juwairah ta sauka, lfy, Yah Jabeer na gani ya na kissing wiyan Juwairah da tai zufa iyaka, shafo gefen fuskar shi tai tana murmushi, Innarmu ce ta dau Babyn tai gefe da ita tana ” Oh yarannan ba ko kunya, ji yanda kai jage2 da hawaye harda majinar kuka dan abin kunya, ita mai haihuwar ma tai jarumta ko kuka ba tai ba sai kai” cikin dakewa da alamun boye halin da ya shiga ya fara magana” a gaskiya Innar mu ba abinda zan ce dake sai ubangiji ya miki rahama, ya saki a aljanna madaukakiya, ke kuma Juwairah Allah ya maki albarka, ya biya maki dukkan buqatun ki, ni Jabeer yau na qara alqawarin riqe amanar ki har qarshen rayuwata” kallon Innar mu yai ya sake cewa” Innar mu da ace mazaje suna shiga dakin haihuwa da matan su da an rage kashe2n aure da wulaqanta mata, da maza sun daraja mata fiye da qima, Innar mu duba fa kiga irin wahalar da yarinyar nan ta sha” ya qarasa maganar cikin tsananin tausayawa da girmama matat tashi, jikin Innarmu duk yai sanyi itama, dan tabbas ta san iyaye mata sunyi matuqar qoqari na samar da mu dika, sai dai mui ta masu addu’a da qoqarin yi masu biyayya,” Jabeeru duk abinda ka fada gaskiya ne, yanzu kaga yarinyar nan tana ta bushe wa, tashi ka dora mana ruwan zafi, ka zo ka saka ganyen magaryar nan a ruwan su tafasa tare saboda ya fidda dattin jikin yarinyar sosai, Jabeeru kazo ka dauki ‘yar ma mana ka riqe mata kamar wani zai dauke ta” dariya yai yana sosa qeya ya gyarama Juwairah zama sosai yanda zata ji dadi sannan ya isa gare su, kallon yarinyar yake with so much love , ga wani irin kyau da Allah ya mata na musamman, wannan kyaun daga ina ta samo shi,juyawa yai ya samo amsar shi wajen juwairah, murmushi ya mata sannan yace” tabbas na samu amsata danake nema a zuciya ta , kyaun yarinyar nan duk naki ne Honey” ” meye wata Hamee ni ta shi ka dora ruwan ka dawo ko kuma ka gyara ruqon ta naje na kwaso na bangare na dana zuba dazu, riqe ta na dawo” yara mai ita tai ta sa kai ta fice tana ” yara ido ya bushe ba kunya, zamani duk ya canja iko sai lillahi” zuwa tai ta zuba ganyen magaryar a ruwan ya ci gaba da tafasa sannan ta kwaso bayan ta tace da rariya ta taho,yarinyar ta karba ta fara wanke wa, mamaki ne ya ishe ta ganin Jabeer na gyara Juwairah, ” kai ni fa sai na bar maku wajen ku, wannan rashin kunya har ina, wa ya koya maka yanda ake ma mai jego ni Hansai” cikin dariyar da suke mata yace” Innar mu na koya ne a wani littafin anti-natal din ta littafai ne da suka qunshi yanda ake renon ciki da haihuwa da kuma yaran kansu, da irin taimakon da uba zai ba uwa in ta haihu, ina fatan kin fahimta, baya daga cikin kyautatawa namiji ya bar mace tai ta wahala ita daya bayan tate suka samar da abinda aka haifa ko za a haifa din, yana daga cikin karamci da kyautatawa tare da soyayya namiji ya shiga dumu2 ai komai da shi, hakan na qara ma ma’aurata fahimtar juna da so da tausayi, sai kiga aure ya dade ba fafa ba yaji bare kai qarar miji gida” innar mu gyada kai kawai take , a zuciyar ta tana ayyana gaskiyar dan nata, amma to be honest ita kunya suke bata, shiru tai kawai bata ce komai ba, Jabeer ne ya kammala gyara wajen ya tallabe Juwairah suka fita tsakar gida, kujera ya bata ta zauna ya fita wajen Innar mu ya debo ruwan zafi, ya shigo da shi cikin babban bokiti, ya raba biyu, daya a babbar roba daya na wanka, kai mata yai ya koma daki ya dakko ruwan kal fari, ya zuba kamar murfi uku a ruwan da zata zauna din, ya je ya fara tayata wankan,” Yah Jabeer pls i can do it my self, Innar mu na nan fa, she may not say a word amma na san ba zata so ganin hakan ba,” ” ke ba abinda zata gani kar mu bata lokaci, mqza na gama maki kan ta gama da Babyn mu,” a haka ya kashe ta da zance ya mata wanka ta zauna a ruwan taji dadi sosai, ya qaro wani, ya saka ta a ciki, ya qara ruwan kal din a ciki( ma’ul kal na wato ruwan kal yana wanke datti shima sosai, ya fidda qarni da warin HQ sannan yana matse mace, ya gyara ta, sai dai ba a so in ba kamar yanzu da aka haihu ba a cika amfani da shi shi da bagaruwa, baya2 ake son amfani da su, dan kar su yi illa ma wajen, kuma ana son in ana amfani da su a yawaita cin fruits da veges da kuma shan zuma mai kyau da zamzam, dan su zama sun saukar da ni’ima a HQ yanda ba zata bushe ba) bayan sun gama ne ya fito kenan Nafee ta dawo daga makaranta, shigowa tai da gudun ta, sakamakoj kukan bby da ta jiyo, ai suna ido biyu da Juwairah ta kwasa da gudu ta isa wajen ta ta rungume tana murna, ” sannu matar Yayah Allah ya qara maki lfy ya raya mana abinda muka samu” ” Ameen Nafee sannu da dawowa” ” to malama sake ta haka taji da kanta” sakin ta tai amma bakin ya qi rufuwa kamar gonar audiga, gani tai ya dakko zanin haihuwar ya aje mahaifar a cikin leda zai wanke zanin, maza tai ta karbe, “Yah Jabeer barmun na wanke ni ban komai ba ai” ” A’a sis basshi yanzu kk dawo skul bana son ki wahal da kanki, kayan jini ne ke kuma baki son su dan haka zanyi, beside ni ya kamata nayi, tinda ina kusa, ta yi me wuyar da ta haifo man the queen of beauties, shiga ki ga inda ake kyau barakallah” ai ko tini ya kwadaita mata gani yarinyat da gudu tai dakin, tana isa ta zube gwaraf gaban Innar mu, ta gyara yarinyar ta sha kwalli, tai matuqar kyau, idon ta bude fes kamar haihuwar sati, cikin zumudi ta amshe ta, tana mata addu’a Juwairah ce ta shigo da sallama daki tai ta na tasbihi ga Allah tana matuqar godiya daya sauke ta lfy, Mama Bilki ta sha addu’a yau a bakin Juwairah, ta gefen idon ta ta hango tsantsar kyau irin na yarinyar, ” ikon Allah ke nan yanzu da wanne ido zani gida na kalli Mama da Abba, wai ni ce yau na haihu” shafa cikin ta tai da yai mata babba kamar bata haihu ba ga nankarwa da taji yayi, murmushi tai ta qara gode Allah, nan da nan ta hau shiri, man kade ta dauka ta shafe cikin da shi sosai ta murqe shi, dama ya sha gashi wajen Yah Jabeer, don jinin ya samu fita, bayan ta gama murje cikin ne ta kwalama Nafee kira dan ta zo ta daure mata cikin, zuwa tai ko ta tamke mata shi, tsam, ya koma kamar ba ta haihu ba, kayan ta ta saka atamfa riga da zani ya mata kyau sosai, kalar atamfar akwai pink da red a jiki, geshe jikin ta tai da turarika masu dadi ta fito, lokacin Jabeer ya gama komai yai wanka shima ya shigo, sannu tai masa da adduar Allah ya saka mai da alkairi, yai murmushi yace” is my duty love, so ki daina damun kan ki,” murmushi tai mai da tasan yana biyan komai a wajen Yayan nata, kada kai yai alamar zamu hadu ne, kina tsokana ta ko, daki yaje ya shorya ya fito ya same su dika a zaune, gyaran murya yai ya kalli Abban su ya gaida shi, dan yana shiryawa ya shigo, yai ma harinya addua, Nafee na ta masu tsiya shi da Innar mu, miqa mai ita Abban su yai shima ya mata addua, sannan ya fadi sunan da za a ana kiran ta da shi, wato Hafsat sunan Innar mu kenan, Innar mu har kukan dadi tai, sannan yace ma Juwairah “sai ku nema mata sunan ku na yan gayu da na san dole sai kun saka mata,” Nafee ce ta kalli Juwairah tace” matar yaya sai ki bamu suna” Juwairah tinani tai sannan tace” Na saka mata Abrar( mao tsoron Allah)” ” Oh ni Hansai yanzu ina ni ina iya fadan Abras” dariya suka kwashe har Abba, Abban ne yace” haba Innar su, yanzu Abrah dinne zai gagare ki?” Haba me zasui in ba dariya ba dan shima ya kwafsa, gyaran murya Jabeer yai ya fara magana cikin tsantsar farin ciki da annashuwa tare da son sanar da su abin farin cikin da ya same su yace” Abba Innar mu Juwaireren Mama and my little sis Nafeesa, ina mai farin cikin sanar damu ci gaban da ya same mu, a yau kuma a dazu dana dawo na zo da labari me dadi na samun aikin da nai, a NNPC na can Abuja in da suka ban gida dake kusa da gidan man da zan aiki, a unguwar Jabi, harda mota, sin dauken a matsayin Manager na wajen gaba daya, sanan kuma bangaren kasuwanci na yau na biya ta kasuwa, Saifullahi dana kan bari ya min jiran wajen in bana nan ya dakkon kudade masu tarin yawa, da kuma wasu jakunkunan da na saro ba su iso ba daga malaysia , to a yau suka iso, har wasu yan kasuwan sun sara, shine ya ban kudin da suka kai dubu dari biyu da talatin cif a hannuna, nan take na bashi talatin din nayo gida da sauran” juye2 ya farayi yaga ina ya wurga ledar da yazo da ita, dubawa yai ya hango ta can hanyar shigowa inda ya yar ya iso wajen matat shi mai naquda, kasa kudin yai kashi biyu, sannan ya qara kasa kashi daya biyu, miqawa Abban shi yai kashi daya, sai kuma ya dauki dubu goma ya ba Nafeesa sauran dubu arba’in ya bawa Innar mu, yace gashi su sa mai albarka,” lallai wannan yarinya ta zama mabudin alkairi a gidannan, muna ma Allah godiya, nayi murna da farin ciki sosai najin wannan abun alkairi daya same mu, Allah ya taya ka ruqo da gaskiya da amana, Allah ya qaro maka arziqi mai yawa mai albarka,” amsawa sukai gaba daya da ” Ameen” Innar mu kukan dadi take tin da aka fara maganar, dan bata taba tunanin riqe kudi rabin wannan bama dan tasan ba ta dasu bata kowa ba ajiya, yau gata da su kuma nata, ai sai murna, ta kasa magana sai kukan dadi take na daukakar da Allah yai wa danta a lokaci daya” Innar mu ki bar kuka addu’a da albarkae ki Yah Jabeer ya roqa” Juwairah ce ta fadi haka a lokacin da ta ke kurbar shayin da Nafee ta hada mata mai kauri da dumi, share hawayen ta tai tace” Jabeeru ba abinda zance sai dai nace Allah ya qara maka albarka ninkin ba ninkin akan wadda ya maka, ina alfahari da kai a matsayin ka na dana, Allah ya karen kai daga sharrin maqiya” amsawa sukai dikka, Nafeema ba a barta a baya ba wajen taya murna da godiya balle mai jego kuma, kiran sallah je ya karade wajen tare da duhun da ya bayyana hakan ya nuna masu cewar magrib ta yi, miqewa sukai bayan sun gabatar da addua, sukai alwala mazan suka tafi sallah matan sukai a gida, bayan ya dawo ne ya dakko kaza a akurkin su, ya yanka biyu, ya kaiwa Innar mu, Nafeesa ce tace ni zanyi dan nasan yanda take son ta, dauka tai ta koma bangaren Juwairah ta dakko ridin da suka daka tare , sa madarar shanun dake aje a randar sanyi, dakko kayan qamshin da suka niqo harda minannas a ciki ta gyara kayan miya ta zuba wannan kayayyakin amma banda madarar, sai da farfesun ya dahu sosai sannan ta zuva madarar shanun, tana tafasa daya biyu ta sauke ta kaima Juwairah guda dayar dan dama dayar can ta batwa Innar mu ta dafa wa kowa a gidan a ci wannan ta mai jego ce, godiya ta mata Jabeer na shigowa ya zauna zai saka hannu, Nafee ta riqe” A’a Yah ga tamu can wajen Innar mu wannan nata ne, ita fa ta haihu ba kai ba, sannan na zuba mata maganin basir a wannan ka jira tamu” dariya yai sosai har yana kama ciki,” yarinya zaki bayani ne kice kawai Nafeesa na hada maki kayan da zaki warke da wuri ki dawo na dora daga inda na tsaya ne kawai, banqi ba in an hanani ci saboda ita ta haihu tai wahala ya kamata taci tai qat amma batub ace wani basir in haka ne ai na fita bair nifa namiji ne” dariya sukai dika. Wajen jaririyar yaje ya dauke ta yana kallon ta yana mata wasa, wanj farinciki yake ji, nan take ya hau mata hotuna, yana gamawa ya danna kiran Abban su Suwaiba, lokacin duk suna tare har Goggo Sarai, duk da ba wani sake mata kowa yai ba amma sun rage gudun ta, sallama yai ya sanar da shi haihuwar, cike da murna kowa ke amsar wayar suna gaisawa, amma Juwairah sam taqi karbar wayar wai kunya take ji, dariya suke ta maya Suwaiba tace sai gobe zasu zo, dik da mamakin dake zuwatan Jabeer Juwairah Da Nafee bai hana su suma sakewa da ita aita hirarn ba, bayan sun gana ne Juwairah ta dauki pilon da aka kawo mata dan ta zauna ta jefawa Jabeer, tana.buga qafa cike da shagwaba” ni baka fadan zaka kira su ba kawai sai dai naji kana waya, kuma wai Abbana ka fadawa na haihu, wayyo ni Allah da wanne idon zan kalle su?” ” da idon da kk kallen a daki ki ka kuren su kina lumshe su a daka lokacin inaa…..” bata san sanda ta miqe da sauri ta damqe bakin shi ba, tana kallon inda Nafeesa take cike da kunya , duka ta kai mai mai zafi a qirji,ya ko yi qara, Nafeesa ce ta fita tana ta dariya” Yah Jabeer Allah mun bata” ta tashi daga jikin shi zata tashi, saurin kamo ta yai tana tirjewa” A’a faaaa ba zan iya da shagwabar nan ba bayan kin san ke ba lafiya gare ki ba, ki hakuri dan Allah ba zan sake ba kinji” kama kunnen shi yai alamun ban hakuri,murguda baki yai ta tashi ta shige daki ta dau jaririyat dake kuka ta fiddo nono zata bata, ga shi ya qura mata ido qurrrr, tura mai tai gaba “ni wannan kallon ya ishen, tinda ka gama naka turn din this is hers pls let her enjoy ita” ta qarasa tana murguda dan bakin ta, sakama bbyn nono tai a baki taji wata azabar zafi na tsotso, janyewa zatai amma jabeer ya hana ta ta hanyat kai bakin shi nata, rasa wanne zata dauka tai, zafin bada Nonon ko kuma kiss din da take karba????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button