YAN ABUJA HAUSA NOVEL

YAN ABUJA HAUSA NOVEL

    BY HAERMEEBRAERH

Page 9:

Tinani ta ke son tayi, amma kanta ya kulle sai pounding yake, nan da nan ciwon kan da take ya qaru sosai, komawa tai ta kwanta, tai qoqarin daina tinanin” Babe what us wrong?” ” kana ke ciwo sosai, so nake na tina abubuwan da suka faru a tsakanin wannan watannin da akai auren mu gaba daya ban sani ba” ” ki dena yawan tinani likita ya hana, saboda zai jawo maki ciwon kai mai tsanani, ki kwantar da hankalin ki kinji, aikin da akai maku ne yasa kuka kai wadannan watannin ba tare da sanin inda kan ku yake ba, nj dinnan da kk ganni sai da nai sati uku a asibiti, abokina kuma wata daya da sati biyu, kafin mukaji sauqi” tausayin kansu ne ya kamata, lallai ashe hatsarin babba ne? A haka bacci ya dauke ta shi kuma yai palo yana murmushin samun nasara, waya sukai da Alh Kalla, ” aboki ya ka qare da wannan ‘yan rigimar?” Komai ya tafi as planed, ban samu matsala ba, wannan shegiyar uwar tasu ce taso sawa mata ta tinani, na kawar da shi, yanzu haka bacci take” dariya suka.saka, ” ai ni tashi tai tana min shagwaba naji kamar na manta da ciwon na dan more ta kadan, dan sai ta min kyau sosai” ” shegen sama, ana halin neman yanda za ai a rufawa kai asiri kana neman kayan dadi” dariya sukai tayi” anyway na mata dabaru irin namu na manya ta bar zance fatan ta Allah ya bata lfy, kasan har yanzu maganin bai gama.sakin su ba, bacci take tayi” ” haka ne, to sai dare in mun hade a gidan Oga, yau akwai meeting” k to ba damuwa sai daren” kashe wayar sukai kowa na jinndadin samun nasarar da sukai, yanzu tinanin su bai wuce yanda zasuna samun jini da aka ce suna kawo wa duk wata ba daga matan nasu, dan su ba sa son suna satar yayan mutane, ana tsafi da su, aikin zai basu wahala, kuma kar wataran a kama su, dabara ce ta fado mai na yanda zasu na samun jinin daga wajen su, murmushi yai sosai, ” dan ta rashin haihuwa me sauqi ne, tunda ba ni aka cirewa mahaifa ba bare na damu, ‘ya’ya dama takura ne, sanda na so haihuwa na nemo matar da zan haihu da ita, dariya.ya dingayi kamar mahaukaci sabon kamu. Ni ko nace hmmmmm kwadayi mabudin wahala. ” Ni dai marka na gani da yin abinci kullum nai na talla nai na gida ?” ” nima haka gaskiya, wannan yar rainin kullum sai dai mu dafa mu bata, ga Baban ma ya tafi har yau bai dawo ba ” tab ai ko yau ita zatai tuwon dare ko taji a jikin ta, ni hutu ya samen, dan ba zai yu.na nemo na tuqa kuma na bata ba inaaaa” “sai Markaaaa, uwar gidan Talle, an buga an barki” yaran suka fada cikin hada baki da dariya da shewa, ita kuma ta wani dage qafa tana zaune a qasa ta turo dankwali gaba, tana kada qafarta da tai fururu, ” je ki kiran ita Huwaila” da hanzari ta miqe tana gyara daurin qirjin ta, tana tafe tana banqaro qirji, qugun kamar an daurawa tabarya zani, ” Amarya ki zo Marka na son magana da ke” kamar ba zata amsa ba da dan duk.tana jin su, ga wani mugun tsoron su da take ji yanzu, dan duk wani rashin mutunci da yake faruwa a kunnen ta, yau da gobe duk tana jin su, fitowa tai dan ta tsira da jikin ta, dan yanda suke ikirarin dukan ta kullum tasan za su aikata, ” kinzo ba zaki magana ba ma?” ” gani” ” to ki bude kunne da kyau ki ji, daga yanzu ke zaki dinga girkin gida, su yaran sj ji da na siyarwa, ba zai yu nai ta wahala ba a gidannan, ke kina nade a gado, saidai na dafa na miqa maki, ki cinye ki gyara daki ki wanka ki koma ki kwanta, ai ba abinda ya kawo ki kenan ba, bautar aure kika zo, dan haka kula da yaran tsakar gidannan ma yana ciki, tsarkin kashin su da masu wanki, duk naki ne yanzu, in dai hutun amarci ne sati daya budurwa, bazawara kwana uku, ke ko ban san ame zan saki ba, tsabar adalci irin nawa wata biyar da kwana hudu na baki kika huta, dan haka daga yanzunnaj ba sai anjima ba ki dau aikin ki” ” wo ke wo ke markan Talle” yaran suka dauka suna ta mata kirari tana kada qafa tana hura hanci su kuma suna dariya, ” banji kin amsa ba ” ” to” ta ce ta juya zata tafi taji wani daga yaran yana ” Naaa gaaamaaa” wani kuka ne ya taso mata, tinawa da tai tinda take bata taba daukan Ammar ba balle ta kai ta ga mai tsarki, gashi yau za taiwa dan wasu, kuma an maida hakan aikin ta, ” bakiji bane sai kin gama qamar da dan mutane?” Sim sim sim ta wuce zata wanke amai,Haule ce tace” Aunty bar shi na wanke mai” ” ke uwar kitifi uwae kinibibi, ina ruwan ki da hukuncin dana yanke? To a hir din ki kar kina min haka ranki zai mummunan baci, ita na ga dama ita zata wanke” ” na gode Haule zan masa kije kawai” wanke mai tai zuciyar ta na matuqar tashi, tanafitowa suka kwashe da dariya har uwar suka tafa, murhu ta nufa, ta hura wuta ta dora ruwan tuwo, ranar dai na taqaice maku ba ita ta kwanta ba sai goman dare, jikin ta ba inda baya mata ciwo, tuwo ta tuqa yan kwano biyu, dan haka tana kwanciya ta hau bacci kamar matacciya.

” Dan Allah Juwairah ki sauri mana, duk wannan wankan naki na qa’ida sai ya sa ba mu fita da wuri ba” Nafeesa ke jiran Juwaora da ta gama girkin rana wajejen qarfe sha daya na safe,ta kammala gyaran gidan tsaf tana son yau taje ganin Maman ta , Nafee tace zata, ita har ta shirya amma Juwairah na wanka ne ma, can bayan kamar minti takwas ta bude ta fito daga bayin” kin san Allah, ba dan kina jirana ba sai na qara five minutes, ya zan nai wanka jikina bai fita ba, kowanne bangare a jikin mace fa ana son amai wanki mai kyau, musammab lunguna da saqon jikin mace ke har kunne da cikin kunne sai na wanke ni haka kurum Yah yazo min soyayya a kunne yaji dacin datti” “iyyee iyayen love, aiko ba zan gangancin wanke kunne na ba ruwa ya shige min a banza a barni da zuwa asibiti da jin azaba” ” hhhhhh dadina dake komai baki iya ba, in zaki ai dabara zaki, tinda kinga yawan goge kunnen nan likitoci na ta hanawa bai da kyau, to saiki samu ki karkata kunnen ki gefe daya, ki wanke ta baki bakin da lungu da saqon shi, in kk gama kk dauraye saiki saka towel ko zani ki tsane ruwan tas, in kk gama da bari daya sai ki wa bari dayan ma haka, kinga ba ruwan da zai shiga kuma kin wanke shi fesss” ” kaiii Juwairah wayon ki da sanin yaiamatan ki na ban mamaki, dan na kula wataran Mama Bilki ma mamakin ki take sosai akan halayyar ki” hmmm tashi to mu wuce na gama” tashi sukai suka tafi bayan sun leqa sum ma Su Innarmu sallama ita da Baba Balarabe, qara masu kudin mota yai yace su gaida mutan gidan in sunje, kar sui magariba a can, amsawa sukai sukau godiya suka tafi.

Da sallama suka shiga gidan, cikin zumudi ta fada dakin nasu, Mama Bilki ce ta fito dauke da fara’ a sakamakon gane mai sallamar da tai, a hanya suka hade suka rungume juna suna ta murna, Ammar ne a gefen maman, da sauri ta dauke shi tna mai kisses ko ta ina,” i missed u so much my bby broth, how ar u doing dear?” Dariya yake tayi kamar ya gane ta yana ta surutai irin na yara masu son yin magana, dariya tai ta aje shi a cinyar ta suka hau gaisawa, Nafee ma gaida su tai, tana mai jin dadin yanda taga soyayyar ‘ya da uwa, da kuna dan uwa, ” Aa mutanen kano ta dabo ci gari jalla babbar hausa, ne a gidan namu” Goggo ce ta fafa tana dariya,” Kano ko da me kazo an fika ba, in mutum ya fadi alkairi yanzu mu bashi amsa dan gidan ya tarar amma in ya kuskure nan ma sai muje maqota mui aron rashin mutunci mu bashi amsa” Nafee ce tai maganar, ” kul Nafeesa, ai uwa ce Goggo a wajen ku, kome zatai karku tanka, ku barni da ita nice daidai ita” Hahaiiiiiiiiii Casssssss a hakan? A hakan ne kk daidai ni? Dga shekaran jiya da yarana suka min waya zuwa yanzu kudin da suka shigo mun ta akawun ( account) ba qanana bane, ke kuma fa? Me ta kawo maki, tuwon dusa muyar lalle?” Dariya ta kwashe da shi sosai harda riqe ciki” kedai anyi sallamammiyar mace, yanzu me kk kenan? Kin tsaya kina rashin mutunci gaban yara, ke da baki da kamun kai, baki son a zauna a gidannan lfy, kullum sai kin nemi tijara ina sane, yauma ba zaki sawa kanki salama ba kenan” Abban su Juwairah kenan da ya dawo lokacin da take masifa, ” oyoyo Abba da gudu taje wajen shi, ta rungume shi, shima rungume ta yai ya kama hannun ta suka zauna, qasa ta duqa ta gaishe shi, Nafee ma haka amsawa yau cikin nishadi” Ehhhhh lallau ne yau yar so ta zo, ka balbale ni da bala’i a gaban su mana, yarana tunda suka tafi baka neme su ba, amma wannan nunar ranar kullum sai ka tambaye ta, yau kuma ji yanda kk rungumar yar cikin ka kamar a gidab qabila” ke malama in baki da abin fada mai kyau fita ki ban waje, Jahila kawai wadda bata san e ake kira da musulunci ba balle ta san abin cikin shi” magana za tai ya daka mata tsawa, fita tai tana qunquni, ci gaba da gaisawa sukai sosai sukai ta hira, a haka dai har lokacin tafiyar su yayi, Mama ta tashi ta hau dan har hada mata wasu abubuwan iya qarfin ta dai, sallama sukai tana kuka suna lallashin ta suka koma gida, suna isa sun zaci Innar mu ta dora girkin dare amma inaaa, murmushi Juwairah tai ta shiga ta canja kaya, ta hura wuta ta dora taliya a cikin kayan da mama ta basu, ta hada da ganyen alayyahu da albasa, ta daka yar daddawa kadan dan ba isasshen maggi to daddawar zata taimaka abincin yai dadi , nan da nan ta kammala ta fada wanka , (Hikima r gyara daki kenan a wajen mace kan ta fita, in kk gyara gidan ki tsaf in da hali ma ki girki kan ku fita, da kin dawo to wanka zaki ki zauna ki huta, ba ruwan ki da zama cikin qazanta, da kuma taraddadin aiki a gaban ki) tana fitowa daga wanka Jabeer ya dawo, fita tai ta amshi ledar hannun shi ta ajiye sukai barka da dawo war su yanda suka saba, sannan ta ja shi bayi, sabon wanka ta sake domin cewa yai bata fita ba sai ya sake mata, tana dariyar gano wayon shi da tai tace” to shikenan ka gama nima sai na maka naka muje muci abinci dan na gaji yau da wuri zan kwanta” ” tab yarinya ku daina zancen vacci ma in zaki bari” yana yi yana matsa cinyoyin ta da yake wankewa, yar qara tai ta shagwaba ta fada jikin shi, tana goga cinyar ta a jikin shi,” Yah Jabeer akwai zafi fa” yanda tai maganar a saitin kunnen shi wani abu yaji har tsakiyar kanshi da qafat shi, janye ta yai ya kiqa mata soson” yi sauri ki wanke ni, nima ba zan iya jira ba, dariya tai ta amsa tana mai wankan cikin wani salon da ya amshe soson ya aje gefe ni dai ganin halin da yake neman jefasu yasa ji fecewa ????????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀
[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: ???????? ‘YAN ABUJA ????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button