YAN ABUJA HAUSA NOVEL

YAN ABUJA HAUSA NOVEL

” Bbyna wai ni yaushe zaki gaida Mama ne kafin a zo ya zamana bazaki iya fita unguwa ba kuma, tinda ita tana abunnan na mutan da taqi zuwa dakin ki har yau” ” hmmmm kaidai bari abunnan na min zafi ace wai uwa ba zata je dakin yar ta ta gani ba? Ba komai, xan je ko gobe ne naji dazu Nafee tace su Adda sun zo, kuma Salma ta dade a gida” ” Eh haka ne, rand naje gaida su ma na ganta ai, Allah ya kaimu goben……….❤

Na gode maku da nuna kulawar ku akaina masoyan YAN ABUJA naji dadi sosai da yanda novel dinnan ya samu karbuwa a zuqatan jama’a masu tarin yawan da ban san iyakar su ba, ina roqon ku da ku qoqarta ku sa na samu ladan abinnan, ta hanyar aiki da abinda kuka karanta na amfani , in da kukaji nai kuskure ku yafen ku nemamin gafarar Allah, wanda yaji dadin novel dina kuma ya mafana da abinda ke ciki ya min adduar samun biyan buqatuna na alkairi. Tanx Love u all❤
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: ???????? ‘ YAN ABUJA ????????

   BY HAERMEEBRAERH

Dan Allah masu tambayar novel daga farko ina qara baku hakuri da cewar, na kusa kammalawa inshaa Allah, so ina ganin it will be better and easy for me inna kammala nai document sai mai so ya same shi. Na gode. Love u xoxo❤

Page 21:

To day is a busy day for Juwairah,amma dik da haka ta kafe yau take son ta je gida dan su gaida da yan uwanta dika, da farko Jabeer yaso hana ta ta bari sai jibi tace sam zata iya ba wani gajiyar da zatai, haka ya hakura, tana idar da sallar asuba azkar din ta dik a hanyar kitchen take yin shi, fitowa tai dan yi ma Jabeer abinda zai samu ya tafi da shi Abuja wajen interwie da aka kira su na wani aiki da ya nema a NNPC, dubawa tai taga basu da wasu kayan abinci sosai as usual, ragowar Flour da ba zata wuce gwangwani hudu ba ta dakko da dan kifin da ta siyo a jiyan, na dari, da kayan miya albasa ta yanka mai ganye sosai ta daka attaruhun ta hada da dan kifin nan, ta soya sama2, nan take ta hada flour tai meatpie cikin mintina qalilan( da ace akwai wadatar a cikin meatpie dinnan zata iya amfani da nama ko kifin ya fi wannan da veges masu yawa a ciki in ta hada sai ta soya sama2 dika amma a yanzu tinda Juwairiyyar mu na da dabara sai ta cika albasa dan ya tada kifin) bayan ta kammala me ta dakko kamun su tai mai koko, ta hada mai shi ta kai mashi, daki kafin ta gama shima yana ta shirin tafiyar, jakar shi da komai ta hada mai dama, komawa tai ta samu zobon ta da ta dafa da yamma jiya ya sha kayan qamshi ta tace ta hada mai shi, ba qaramin dadi yai ba, ta samo wata yar robar ta cika mai da ita ta daure yanda ba zai zuba ba, ta debar mashi meatpie ta rage ma surukan su da zasu zo anjima wajen neman auren Nafeesa, sannan ta koma daki, qarasa tayashi hada komai tai, dai dai da brush din shi bata manta da saka mai a jaka ba, bayan ya gama cin abincin ne ya gama komai ya janyo ta jikin shi” My princess ba abinda zan ce maki sai dai nai maki fatan shiga aljanna, tin da ance sai miji ya yarje wa matar shi shiga aljanna zata shiga My Juwairiyyah na yarje maki shiga madaukakiyar aljanna da izinin Allah, ke macen kwarai ce, macen nunawa kowa ba tare dana kunyata ba, Allah ya sauke ki lfy, ya shiryar min dake , Allah ya qara miki imani, kinga ga wannan ba yawa kwama biyu zan kamar yanda na sanar dake, ki ta tayani addua inna samu aikin nan xamu samu hutu sosai, zan jiyar da ke dadin da baki taba zato mace zata iya samu wajen mijin ta ba, Juwaireren Mama ina son ki” ba abinda take zabgawa in ba murmushi ba, amma yana cewa Juwaireren mama ta turo baki tana buga qafa,” Ni dai Yah Jabeer bana so, taso ka tafi kar ka makara, Allah ya karen kai mijina kaje lfy ka dawo lfy, Allah ya bada sa’a a abinda aka tafi nema, inshaa Allahu kai me nasara ne akan komai na alkairi da ka sa a gaba, dan haka don’t feel nervours, u will do just fine, u can do it, saboda kai din na daban ne a cikin mazaje,karka manta da karanta lahaula wala quwwata……. da hasbunallahu wa ni’imal wakeel, Allah will be at ur aid, he will guid and protect u, ina son ka Jabeerun Baba” ta fada tare da miqewa da sauri tana dariya bin ta yai ya cafko ta ya hade ta da gini, ” maimaita me kk ce” turo baki tai tace ” yo ni me nace, dan dai kawai an ga yau mijina zai tafiya sai kuma a ce za a min yar qure a ci zalina, dan irin wannan kallon da kk min ji nake kamar na dawwama da kai a haka a tsaye ba tare da duniyar ta juya ba” ta fada cikin qasa da muryar ta, wani irin farin ciki ke ziyartar zuqatan su, a cikin ran su kowa na yaba kyau irin na dan uwan shi, bakin shi ya kai saman nata, ya shiga sarrafa lips din su, cikin salon da dikkan su zuciyoyin su sai da ta narke, biye mai tai sosai suke jin dadin hakan, aka kace musu da sallama, Nafeesa ce tai sallama ta taho dan Juwairah tace ta zo sui komai da wuri zata gida yau, janye jikin shi yai a kasalance, ya riqe hannun ta ita kuma ta kwantar da kanta a jikin shi, fita sukai tare idon ta taf hawaye, yau je ranar farko da zai tafiya tin auren su,kuma har zai kwana biyu baya nan, saurin maida kwallar tai kar ya gani hankalin shi ya tashi, amma ta makara” Haba my Queen, ki kwantar da hankalin ki mana, inshaa Allah jibi da yamma kina maqale a qirjina,daga wannan tafiyar ko ina ban sake zuwa na barki qafa ta qafar ki kinji” ai kamar ya zuga ta ta bare baki irin na yaran nan ta fara kuka, rungume ta yai tai kukan sosai sannan tai shiru ta sake mai addua, ya suka fita har Nafee suka raka shi, Innar mu ke tsokanar ta” to kukan rabuwa da maso yi aka shaaaaa Hoh yan zamani, to dakko mayafi ki bishi” da gudu Juwairah ta tafi tana dariya, suma dariyar suke, sai da taje baqin qofar shiga wajen su ta juya, dan tsuke bakin shi taga yayi alamar kiss, ta waro ido ta kalli su Baba Balarabe dake gefe zasu raka shi qofar gida, rufe baki tai da hannun ta ta fada wajen nasu tana dariya, ” Allah sarki mijina,kaje lfy ka dawo lfy cikin sa’a da nasara, tare da kariyar Allah” Nafee ce tace ” Ameen masoyan asali” murmushi sukai suka shiga kitchen, lokacin takwas da rabi tayi, masarar da aka barza suka dakko nan da nan suka je suka tsinko zogalen da Juwairah ce ta shuka da hannun ta, da alayyahu, sai albasar su mai lawashi, gyarawa sukai suka dake gyada, da kayan qamshi attaruhu da maggi gishiri suka saka yanda zai isa yai dadi suka saka suka dora a wuta, nan da. Nan sai ga dambun masara mai dadi ya hadu, mai s Juwairah ta soya dayaji albasa, hadawa sukai a flask wannan zobon juye ragowar tai a wani babban jug nata sannan ta dakko meatpie dinnan ta aje Nafeesa ta ji dadi sosai tana taima yar uwar ta kuma matar yayan nata godiya har saida ta ba Juwairah haushi, godiyar tai yawa, ajewa sukai a gefe Juwairah ta sa Nafee debo wani alayyahun da albasar mai ganye, ta sa ta gyara, ta daka kayan miya wanna karon harda timatir, jelop rice mai dadi tayi wadda ta yayyanka dan naman d suka tafasa tin jiya, saboda bai da yawa yasa Juwairah tace bari su yanka qanana sai a soya sama2 su saka a abincin, har da dan carrot din su, nan da nan sai ga girkin da su suke ganin anyi a talauce ce amma wani gidan masu akwai din ma matat gidan ba zata zage tai hakan ba, wanka ta tafi tayi ta sa Nafee taya ta gyara gidan, dan bata son fita ta bar gida da datti in ta dawo ranta baya dadi, ganin dattin, sannan kuma ga gajiya, ( wasu matan taqamar fita za tai unguwa sai ta bar gidan kamar bola ta tsallake,na farko in kk dawo zaki iya baqin kunya gida kaca2, ko kuma ki dawo a gajiye,ga shi maybe miji ya kusa dawowa, shima ya dawo yaga yanda ya fita haka ya tarar wataqila harda qarin dattin ma, amma in kk gyara gidan ki fes in da haki kikai girki, da kij dawo wanka zaki fada ki fito tsaf dake,maybe sai bacci ma tinda baki da aiki, mata mu kula????????) bayan ta fito ne abincin ta da zata ci yanzu ta dauka taci ta aje na daren da ta diba ta rufe kitchen din bayan ta wanke plate din data ci abinci,kmawa tai ta shirya ta fito, bangaren Innar mu taje ta mata sallama ta dau hanyar gida cike da zumudi da doki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button