YAN ABUJA HAUSA NOVEL

YAN ABUJA HAUSA NOVEL

  BY HAERMEEBRAEH

Page 7:

Bata qarasa mamaki ba taji innar mu na cewa, ” shegiyar yarinya, daga zuwa komai na mu ya fara tabarbarewa, gaba daya Jabeeru ya tare a qasan ta, ko shigowa gida yai da mun gaisa wuf ta tafi wajen ta, ya dan zauna mui hira ma yanda muka saba amma inaaaa an janye mai hankali, to ni ba zaki mulkar min da kamar yanda uwar ki tai ba, in dai ina raye, hqka kawai, ke na haifarwa dan? To mu zuba shege ka fasa” kuka ne ya kusa kwace ma Juwairah jin kalaman surikar ta, wannan wace irin rayuwace kuma?” Ya Allah help me” abinda ta iya furtawa kenan ta share hawayen ta ta koma ban garen ta, qarasa gyara wajen tai tai wanka, tai brush, ta gyara gashin ta da ta wanke, ta daure bayan ta shafa mai mai ta taje, ponytail tai ma gashin, ta dakko daga qanan kayan ta da, Inna Deejee ce ta siyo mata su yan gwanjo ne, amma masu mayuqar kyau, tin da basu da halin siyan sabbi, kalar shigar ta, kalar pink da black ne, riga da wando pencil, sun amshe ta ba kadan ba, fita tai ta debo garwashi ta saka tiraren wuta, sannan ta fesa jikin ta da tiraren, ta shafa humra, kyautar Goggon ta Kareema kenan, kafin kace me da ka kalle ta zaka dauka yar wani hamshaqin me kudin ne, ko matar wani attajirin, Nafeesa ce ta shigo” dadina da matat Yaya kina burgeni, ko ta wacce gaba aka latsa ki kina nan, a shekarun mu kina da kaifin hankalin da babba ma bai da shi, duba kiga yanda kikai mana dabara dazu, Innar mu da ta koma daki da ta ga abincin ban san me ya razana ta ba, dan naji harda ashar ta baza mana a dakin dazun” ta qarasa cikin dariya, ” kai sisto irin wannan fasa kai haka, in kk fashe man kan nawa yayan ki ya dawo kin masa bayani ai” Sallamar shi suka ji da sauri Nafeesa ta fito zata bar wajen, tsayawa tai ta gaida shi sannan ta wuce, tana jin Nafee ta fita ta taso cikin yauqi da tafiya mai daukan hankalin masoyi, wani lumshe ido naga tana yi kamar mai jin bacci( duk a cikin salon daukan hankalin Yah Jabeer ne????) tana isa wajen shi, ledar hannun shi ta karba, sannan ta jawo hannun shi zuwa daki, suna shiga kamar jira yake duk yar qibar nan tata da manyan duwais dinnan baya jin nauyin su, dagata yai ya manna ta da jikin bango,dariya take mai sanyin sauti, ta zagaye wuyan shi da hannayen ta , dora fuskar ta tai a kan tashi, tare da hade bakin su waje daya, sai da tai mai kiss mai tsayawa a rai, sannan ta kai bakin ta wajen kunnen shi tana mai sannu da zuwa, ” Jarimin maza ina maka barka da dawowa, ina fatan yau kasuwa da mutanen cikin ta basu wahal min da kai ba ko? Dan in haka ta faru akwai hukunci mai tsanani akan su daga wajena” hura mai iskar bakin ta tai a kunnen tare da yin kiss a ciki ba shiri ya nemi wajen zama da ita a hannun shi, ” a gaskiya samun mace kamar ki Juwairiyyana akwai wahala, u ar one in billions, samun kamar ki ancikin mata million zai wahala, ke ce daya tamkar da dubu, in zance zan tsaya fadan wacece ke bakina zai running out of words, so kawai ke kadai ce , kuna ke daya Yah Jabeer din ki ke so” wani irin dadi ne ya lullube ta, kamar yanda kullum take son faranta mashi, shima qoqarin shi kenan, basu da arziqi, ba su da abubuwan more rayuwa, amma suna da junan su, tashi zatai daga cinyar shi amma sai da ta goga mazaunan ta a jikin shi da yasa shi sakin yar qara, gwalo ta mai ta tafi da sauri zatai daki, binta yai a baya yana” ai baki isa ba, ki tsokanen ki gudu, haba yarinya, tsayawa zaki ki qarasa ladan ki kawai” dariya take tana bashi hakuri ” dan Allah Babe ka bari kaci abinci kai wanka, sai namaka tausa kamar kullum, in yaso in ka samu qarfin jiki yau till down zamui” tana kaiwa nan ta rufe fuska tana dariya ta zagaye shi ta fita da sauri, zuwa tai ta hada mai ruwan wankan, ta dawo shi kuma ya shirya wanka, shiga sukai bandakin a tare bayan ta je ta rufe qofar bangaren su, wanka ta mai da kyau ta sa mai toothpast a brush din shi( mata da yawa suna cewa wai mijin su yana warin baki baya son yin brush da sauran su, shawara gare ki sister mai wannan matsala shine, ba a ce ma na miji je kai brush ko wani abu makamancin haka, dik da akwai mijin da in shaquwar ku ta kai qololuwa kina iya sanar da shi kuma ba zai damu ba dan yasan duk amfanjn ku ne ke da shi, so in ba irin mijin nan gare ki ba dabara zaki, ki hada maku ruwan wanka tare kafin wankan ki tabbatar kin gama gigita shi yanda ba zai maki musu a komai ba, daga nan sai kui wankan tare, in ba kui tare ba saboda maybe yanayin gidan naku, sai saka mai ruwan ki kai masa da kayan wanka, sannan ki saka mai toothpast a brush ki aje mai a kusa, ba yanda za ai ya qi musammab yaga kin saka maku tare, kinga ba zai zargi kina jin wari bane daga wajen shi, har yai feeling bad kuzo kuna samun sabani) bayan ta mai wankan yayi brush daki suka koma, ta gyara mai jiki tare sa feshe shi da tirare, palo ta dawo da shi yana biye da ita kamar raqumu da akala, abinci ta zaunar da shi ta bashi, yana ta santi” kaiiiii amma ba qaramin birge ni kkai ba, kin san rabona da faten wake har na manta kuwa?” ” naji dadi da yabawar ka Hubby” ” kusa da ita ya matso” ke din ta daban ce, komai naki daban ne,Allah ya barmu tare” murmushi sukai dika, kiran sallar magrib ne ya katse su suka tsaya suka saurara sannan suka bi suma, bayan an idar ne sukai adduar da ake yi ba yan idar da kiran sallah, Allahumma rabba hadhihidda’awatittammah, wassalatil qa’ima, a ti muhammadal wasilata wal fadeela waddarajatirrafee’a wab’athhu maqamam mahmudan lladhi wa adtah, innaka la tukhliful mi’ad, sannan suka dora da salatin annabi ingantacce, addua suka daga hannayen su sama sukai a tare ita da shi, suna idarwa suka tashi sukai alwala, shi ya tafi masjid ita tai a gida, bayan ta idar ne tayi azkar din bayan kowacce sallah ne, sai ta samu tai kuma azkar din yamma, tana idar wa ta miqe ta je tai wanka ta dawo dan ragowar abincin nasu ta juyo masu ta kawo ta hado da ruwa da komai ta aje a gefe, daki taje ta saka rigar baccin ta mai matuqar kyau da daukan hankali, sai ta dora zani akai, da hijab tana jiran sallar isha’i bayan tayi sallar ne da minti 15 ya shigo, sai da ya biya wajen Innar mu ya gaida su, baban shi na ta sa mai albarka, ita ko ta cinkishe fuska tana hura hanci, daya tambaye ta sai tai qaryar kanta ke ciwo, dan yau wuni tai da yunwa, can sai ta saki fuska ” kasan da yake bana son faten wake, kuma bana son bawa yar albarkar nan aiki shiyasa, amma da shinkafa zan bata ko gwangwani dayar nan ne ta dafa min, tinda Nafee ita har yau bata iya tsantseni irin na Juwairah ba” ba komai Inmar mu kawo na kai mata za tai maki ai, ba zai yu ku kwan da yunwa ba” da sallama ya isa daidai Juwairah ta fito daga daki ta cire zanin ta da hijab din ta, tana qarasa shafa mai a cinyar ta, ko da ya higo tini ta sauya salon shafawar, sake baki yai kamar dolo yana kallon ta, qarasa shigowa yai ya aje ledar still idon shi a kanta, juyawa tai ta koma daki tana tafe tana juya bayan ta tana waigowa tana mai wani kallo da murmushi, ni dai tin da ya shiga suka ja qofar bam qara ganin me suke aikatawa ba sai dai kunnuwa na sun jiyo man Jabeer na sambatu da bana gane yaren da yake, sayyarar qafa ta na ja nai waje????????‍♀????????‍♀

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button