YAN ABUJA HAUSA NOVEL

YAN ABUJA HAUSA NOVEL

Da kyar Marka ta miqe ta je ta hada wuta ta shiga ruwan dumi ta gasa jikin ta, komawa tai ta ci gaba da kwanciya, wani qaramin yaro ne shafi’u daya daga cikin yaran da Talle ke auri saki ya shigo zai kai shekara goma, baya jurar yunwa shi, dan ko da su Huwaila na baccin gajiyar iskancin su da suka sheqewa da dare, ita Marka takan tashi tai abin kari da wuri, to yau sunji shiru kowa dif a gidan, tura kai yai ta ware qafafu tana ta firfita da mafici,” Marka yunwa muke ji” da sauri ta sake zanin ta juyo kan shi,” me kace?” ” cewa nai yunwa muke ji” habaaa ina wuta na saka wannan yaron, inji Marka, kiran shi tai tace zo ka karba, yana isa data damqe shi ta hau duka, tana” sai na fashe dukana akan ka, dan uban ka, banda wannan ta’annutin da uban ka ya min, har abinci kk tambaya? Ga shi tinda ya dauke waccan jaja amaren sai da na gan shi kuma, to ko xaka ci abinci har ka qoshi, amma na duka” dim dim dim kk ji” Marka lfy me ya miki haka” cewar Haule kenan, tana qoqarin kar bar shi, wani mari itana ta karba, kai na taqaice maku duk wanda ya shiga sai ta saki wani ta kama wani haka tai tayi kamar mahaukaciya, sai da ta gaji jikin ta yau laushi sannan ta kwanta tana kuka, ita ta shiga uku, ta hada sharri kuma ya zame mata tsiya……
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: ???????? ‘ YAN ABUJA ????????

   BY HAERMEEBRAERH

Masoya novel din ‘YAN ABUJA dan Allah ku min hakurin jina da bakuyi akai2 yanda na saba, inshaa Allahu in komai yai normal zan ci gaba ba da tsaya ba har sai na gama dika. Na gode. Love u all❤

Page 17:

” wa’alaikumussalam shigo shigo yar uwa kiga me yayana ya saimin” Juwairah ke fadin hakan cikin murna da kuma zumudi, Nafeesah ce ta qara sa shiga itama cike da dokin ganin me za a nuna mata, sanda ta gani itama yar qarar murna tai ta haye kujerar da Juwairah take” kaiiiii amma Allah ya saka ma Yah Jabeer da alkairi, ya sai mana waya mun daina leqen ta qawaye” ” to malama ba wai an sai mana waya ba na dinga neman ta ina rasawa” ” hhhhhh Allah baki hakuri ai wannan wayar inna dauke ta yanda kk san jariri sai kin nema na miqo maki, ko in tana buqatar a sa mata kudi” dariya suke sosai, ” yauwa wai ni ruwan meye wancan a butar qarfe na ga kin saka a garwashi?” ” Oh ban cire ba dama je ki sauken dan Allah ki dawo na fada maki hajiya tambaya” ” ah to dan kin san in baki fadan ba baki da zaman lfy yau” fita tai ta sauke mata butar ta dora ruwan wankan ta , ta koma dakin, xama tai tare da tanqwashe qafa agaban Juwairah tace ” To malama a bamu darasi, dan zama dake akwai diban ilimi” ” ke ko, ke ko, hmmm kina raina sanin da Allah ya baki ne amma kin fini ilimi ai, kefa duba ki gani yanzu ci gaba da karatun ki kike ni fa ina zaune a gida kullum” ” kema zaki ci gaba ne komai lokaci ne sis oya ina jin ki meye wancan a butar qarfe?” Dariya Juwairah tai sosai sannan tace” ke dai ba ki mantuwa to magani ne, maganin infection musamman na masu ciki, Mama Bilki naga ta yi lokacin cikin Ammar shine nayi, Oh har naji ina son ganin yaron nan wallah” ” to naji magani ne amma ai baki fadan ya ake hada shi ba ko” haka ne, kinga dai da fari zaki samu ganyen garahuni, da ‘ya’yan hulba ki tafasa su sosai sai ki bari ya sha iska sai kina tsarki da shi, da yawan masu ciki suna fama da infection sosai, mai fidda ruwa kala2, amma da zasuna amfani da wannan zai masu magani duk da ba wai yana dauke shi dika bane kwata2 amma yana ragewa sosai, in aka hada da wasu magungunan na sanyin” ” yauwa ko ke fa ba ga shi kin qara min ilimi ba ni ina ma san wannan abun,in ba yanzu ba, yauwa rannan naji kina fadama shamsiyya wani abu lokacin na fita ban ji me kuke cewa ba game da warin gaba” ” Oh k wannan, dama muna magana ne akan macen da take fama da warin gaba na farko dai akwai na lalura, akwai wanda mace da kanta take jawo wa kanta” “hhhhhh kaji Matar yaya wai mace ta jawo wa kanta kamar yaya? Kana sane kabar jiki yaita tsami” dariya sukai sosai suka tafa, ” Allah da gaske nake, yanzu misali Nafee, ke ce kin tashi a rana kin wuni da pant daya a jikin ki, kin je fitsari kin yi fitsari baki wanke wajen sosai ba kin maka pant kin mayar, kin yi bayan gida kin maka kin mayar, sannan da jiqar da komai kk mayar wa, ki fadan pant din dan uwan ku ne da zai qi wari?” ” hhhhhhh wallahi dole yayi amma dai misalin nan dama ba dani aka buga shi ba a canja gaskiya a saka Salma” ” wulaqanci yayar tawa, Allah sarki mutan Abuja ana can ana shan dadi an manta da dangi” ” hmmm ke dai bari buri ya cika, Allah muma ya sada mu da mafi alkairi” ” Ameen dai” ” to yanzu fadan ya za ai ai maganin wannan warin dan Allah dan akwai yar makarantar mu, kin zauna kusa da ita sai kinji wannan warin, dan ba zanji kunyar fada mata ba, da azo ana ta gulmar ta tana jin haushi” ” Allah sarki, aiko gwanda ki sanar da ita, dan aboki na gari ke wayar da kan abokin shi, kina ji ba, a rana a baki canja pant a ki canja sau uku, ya zama na kina da tsimma ko towel qarami a toilet din ki wanda in kikai fitsari ko bayan gida zaki tsane wannan ruwan, sannan in kin zo tsarki ki fara da gaba ko da baki komai ba, sannan baya, karki hade wajen wajen wankewa, in kk gama kk goge wajen sai ki maida pant din ki, in rana tayi kikai wanka sai ki canja, da dare ma haka, ba yanda za a same ki da wari ko da baki shafa misk, balle a same ki kina wanke wajen da ruwa mai dumi da kk zuba zuma asalin me kyau, wannan wanke gaba da ruwan zuma ya samo asali ne daga Annabin rahama yana daga taskar magungunan daya bayar muna amfani da shi, bake ba warin gaba in dai kina wanke wa da ruwan zuma kina saka misk, kina tsanewa in kinyi bayan gida, ina fatan na amsa tambayoyin ki Hajiya tambai” ” hhhhh wallahi kin biya ni kin amsa har da wanda ban ma zata ba ke dai Allah ya barki da yaya, ya sauke ki lfy” cikin jin dadi tana shafa cikin ta ta amsa, tashi tai ta tafi bayi da butar ta a hannu, bayan ta fito ne take ce ma nafee” Nafee gobe ne kin san ranar gyaran jikina ina zan samu dankalin turawa pls na wa ya qare” karki damu zan samo maki kan gobe, ji cikin ki ya fa girma amma kk maganar gyaran jiki, ki bari ki haihu mana” ” Tab aa ni dai ki samo min, in babu ma ina da zuma da sugar kawai ki samon lemon zaqi ko daya ne ko biyu” ” to Allah ya kaimu, bari nai wanka na fita makaranta” “to Allah ya bada sa’a, bari na dan huta nima”.

” Alhj wannan itace mata ta da kuka karba min auren ta a garin kano, dama na dawo da ita nan ne dan na dinga samun kulawa, zama ni dayan ba dadi” Talle kenan ya fada yana sosa qeya, murmushi uban gidan na shi yai yace” Allah sarki ai ba damuwa, hakan da kai kayi tinani, kuma ka kyauta, ina maku fatan alkairi, Allah ya bada zuri’a dayyiba” ” Ameen” gaida shi salma tai kanta a qasa tana wasa da gyalen ta, ya amsa ba tare da ya kalli in da take ba, kudi ya qirgo dubu goma ya bata, yace gashi ta sai wasu abubuwan da take buqata, amsa tai hannu na rawa, rabon data riqe kudi haka ai ta manta, tashi sukai suka fito, suna isa daki ya miqa mata hannu, fuskar nan ba walwala,” me zan maka kuma” ta fada cikin tsiwa, ” dan uban ki ni kk tambaya me zaki min, to in baki san me zaki min ba bari na fada maki, kawo su nan” alamun da ta gani na ba wasa yasa ta miqa mai tana hawayen baqin cikin ga samu ga rashi, murmushi ya fara yi jin dumus da yai,” Ko ke fa salameme na, yanzu ai kin ga ko dari biyar na baki ai yafi na qattin qauye masu baki dari da hamsin ko” juyo wa tai cike da bala’i tana kallon shi kuma sai ta fasa dan wani tsoron shi daya kamata, gani tai yana cire kayan shi, ita ko bata shirya ba, ga ciwon jiki da take fama da shi, gashi shi in ya fara abu bai san ya bari a huta ba, sai ya gajiyar da mutum, kuka ta fara tana” ni na barma dari biyar din dan Allah ka bari sai nan da kwana uku, na gaji banda lfy” dariya yai sosai ya maida kayan shi” da kyau matar manya matar Dan Abuja kenan, ku baku da buqatar kudi ai, ni na fita to ga wannan ki leqa waje akwai shago ki siyo kwaki da sugar ki sha, ina jin har canjin gyada zaki samu ma” nera dari ya wurga mata ya fice yana wata tafiyar yan duniya a shagide, kuka ta durqusa tana yi, ” wai ni ina yan uwana ne, suna can suna jin dadin su sun manya da rayuwa ta, basu san a halin danake ciki ba,Oh Allah ka kawon dauki, na tuba, Juwairah kin huta, dabaki zabin aure ina zaki ba, gani ina cin ubana a garin da na taso da kwadayin yin aure cikin shi” kuka take mai ban tausayi, yunwar dake cin ta ce ta dawo da ita daga tinanin da take, tashi tai ta wanke fuskar ta, ta saka mayafi ta je ta siyo garin ta da sugar da gyada, hadawa tai tana sha tana kuka,ganin duk talaucin su ba su shan gari a gidan su amma yau gata da gari, share hawayen ta tai, ta jingina da katifar su, a haka baccin wuya ya dauke ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Back to top button