BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

27/11/2019
[11/28, 7:55 AM] BintuUmarAbbale: BABBAN YARO
MALLAKAR_ BINTA UMAR
LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI
66
Mujahid ya cigaba da rarrashin Momyn sa har sai da tayi shiru tukkuna ya kalleta a nutsu yace.”Momy wai ina kika ga Asma’u da har tayi miki rashin kunya nifa abun nan ya bani mamaki.”! Cikin fusata Momy tace”Naga kamar kana shakka ne Jahid har kana titsiyeni ka tambaye ni, to gidansu nasa aka kaini domin in gargade ta ta fita harkar ka domin naga mayu ne kana zaune da matar ka ta kirki ka je ka kwasowa kanka kaska shine fa ta yi mana wankin babban bargo nida Hajiya Fatima.” Mujahid yayi kasa da dansa cikin mamaki jin wai momy gidansu Asma’u taje to in hakane Ashe itace ta jawowa kanta raina yasan halin Momyn sa da zubda girma mybe taje tayi wulakancin da ta saba ne. Tace “Saboda haka in dai nice mahaifiyar ka ban yarda k auri yarinyar ba, shida shiru yayi mata har sanda ta kare fad’an ta yayi mata sallama ya tafi gida. To ko da yaje gida ma matarshi kasa gane kansa tayi dama ‘yan kwanakin nan haka yake mata duk ya sauya kwayenta nace mata dama idan namiji zai kara aure canza hali yake, ita dai tunda ta hada masa abunci sai ta shige d’akinta domin ta lura kamar zamanta a kusa dashu baya so. Jahid kuwa ba wani ci abunci da yawa ba, ta kwanta duguwar kujera yana tunanin ala’amri lokacin yi wayar su nayi ya kirata. Lokacin ina zaune ina yin game a wayata naga kiransa dama na tsammaci haka, Muka gaisa kamar yanda muka saba kana ya d’ora da maganar shi kamar haka” Asma’u wai da gaske Momyna tazo gidanmu.”? Nace”Babu wai Mujahid Momynka tazo gidanmu. ” shiru yayi na minti biyu yace.”Ki fada mun gaskiyar Abunda ya faru.” Nace”Jahid Momyn ka tazo tayi mana cin mutumci sosai takai har sai da na mayar mata da martani a rashin sani sai daga baya da ta fad’i cewar itace Momynka sannan naji kunya don Allah kayi hakuri nasan duk zata fada maka abunda ya faru tsakaminmu amma ni abunda nayi mata a rashin sanine.” Jahid yaji ya kara kaunar Asma’u yana ganin ba zai iya janye kudirinsa akanta ba zai lallaba Momysa ta hak’ura ta barshi ya aure ta A halin yanzu ita kurrum yake gani yaji sanyi Asma’u tw zame masa wani b’angare na jikinshi, take ya manta da b’acin ran Momyna suka cigaba da hira shi da Asma’u Cikin shaukin so Sam! Ya manta ma cewar a cikin gidan shi yake kuma a patlor Maman Salim zata iya jinshi, Aikuwa tana daki tana tik’ar kukan takaici a zuciyarta tana ji ta tsani Asma’u tunda ta shiga tsakanin ta da mijinta da suka Gina rayuwar su cikin aminci da yardar juna.
Mujahid ya nunawa Momynsa kamar ya janye maganar auran sa da Asma’u a b’oye kuwa sun hada baki da mahaifin sa, har anje gidan su Asma’u ankai kud’in aure da sadaki lokaci kurrum ake jira kuma kullum suna tare domin shakuwar su ta yanzu tafi ta da waya kullum babu dare babu rana haka suke yi.
Watan Amjadu Biyu a chana komai ya kammala nan ya wuce Ingila domin can ma akwai bukatar yaje din domin duba company shi da ganin irin cigaban da aka samu. A shkekarar kullum suna tare da granny a waya maganar guda ce Babu Aysha tayi kaza kaza wani lokacin sai dai granny ta kashe wayar ta kyaleshi ko kuma ta kara wayar bakin baby Aysha tayi ta gwalantu shi kuma yana kyalkyala dariya sai Granny ts karb’i wayar sannan zai ce da ita wai tana fad’a masa ne tayi missing d’insa sosai. Granny tsabar haushi sai ta kashe wayar tana fadin’Kai da ita kuka San wannan.”
Muna a dai-dai sahu nida Munnu tace”Ke Wallahi yau sai munje gidan Young millionaire mun dauko baby Aysha ta kwana biyu a hannun mu tunda kince ai mahaifin nata bayanan ko.”?Nace ” Bayan nan yayi tafiya lallai Munnu ke ‘yar rigima ce ni kam babu ruwana Wallahi. ” Munnu tace”Ki sa wasa ki gani, mai a dai-dai muje Jambulo.” Aikuwa Mai a dai-dai ta ya Karya kwana , nace “Munnu sai dai in ki shiga ke ni kam bazan shiga ba.” Tace”Wallahi sai mun shiga tare “Dariya NASA Nace ” Zakiyi kaffara kuwa. Muna isa Munnu ta biyashi kudinsa muka tsaya bakin gate din, take masu gadi suka bude mu din ba bakin bane a gidan, Jan hannuna take wai dole sai na shiga ganin kar abun ya zama da zargi yasa na bi bayanta gabana na fad’uwa ni yanzu Sam bana kaunar abunda zai hada ni da guy nan tunda yace s k’yale masa ‘yar sa to sai a k’yaleta domin a zauna lafiya.
Granny da Iyami na zaune a parlor suna kallon shirin dadin kowa tashar Arewa24 muka yi sallama. Granny ta amsa tana fad’in “Lale maraba da manya baki lallai yau Baby Aysha na da baki domin dai nasan domin ita kuka zo gidanan.” Murmushi nayi na zauna Cikin kujera a nutse muka gaisa sosai tace”Shikkenan saboda babu Aisha sai Ku yanke zumunci damu har Umman taku ma ai wallahi bata kyauta ba.” Hakuri na dinga bata INA fad’in”Bana samun lokacin zuwa ne saboda makaranta. Granny tace” Yau watan baby Hudu a duniya ace kuna a matsayin iyayenta babu Wanda yazo duba ta ai gaskiya naji haushin wannan Abu.” Mu dai hakuri muke bata, sannan muka gaisa da Iyami dake kallon tana dariyar durmarmu d Granny tace”Iyami Kawu musu abunci.” Duk da ina jin yunwa sai da nace “Granny a koshe muke Wallahi.” Hararata tayi tace”Wato kinanan da halin ki na cutar kai ko? Dubi bakin Ku a bushe kice min a koshe kuke ai nasan daga makaranta kuka dawo.” Shiru nayi kawai domin nasan dukanin abunda zan fada Granny ba yarda zata yi ba. Munnu tace”Ina baby Aysha ne? Domin munzo aba mu aronta.” Granny tace”Yanzu kuwa tayi bacci wallahi ai kun fi k’arfin abaku Aron ta idan ma kyauta kuka je a baku za’a baku ita kyauta.” Munnu tace”Granny da gaske nake wallahi zamuje da ita ta kwana biyu sai mu dawo da ita.” Granny tace “Nima ai da gaske nake.” Iyami ce ta shigo da k’aton tire cike da nau’ikan abunci da abunsha ta aje kan dogun tebur din da yake gabanmu. Granny tace “Iyami maza hada kayan baby Iyayenta zasu je da ita su ta kwana biyu.” Iyami tace”To Hajiya amma fa zamu sha kewa da yawa.” Granny tace”Zamu huta da rigima dai kinga zamuyi bacci harda munshari musamman ke.” Dariya muka yi harda Iyami ta nufi wani daki da sauri tana fad’in “Baby Aysha rigima kenan. Sosai muka saki jiki muka ci muka koshi mana hira da granny Cikin barkwanci ni kam Allah-Allah nake a fito da baby Aysha na ganta. Aikuwa sai ga Iyami ta fito da ita a kafadar ta daya hannun NATA kuma k’aramin akwatu ne. Ni da Munnu rige-rige karb’ar ta mukayi Allah ya bani sa’a ina karb’ar ta na manna mata kiss a kumatu ina dariya ganin yanda take motsa bakinta tana tsotsar hannunta, da alama yunwa take ji. Granny tace” oh! Oh oh!! Wai meye amfanin abunda kuke yi ne, kuyi ta tsotsar kumatun yarinya shima haka wancan sakaran yake yi, mata har bakinta tsotsa yake.” Ni da Munnu muka dariya nace”Ni kam sumbatar kumatun ta kawai nayi granny gaskiya Iyami ta iya raino naji dadin ganin baby Aysha haa duna granny kamar ba bakwai ni ba.”
Tana dariya tace”Yanzu zata nuna muka halin nata na k’uya Iyami kadai ta sani saboda ita take bata abunci ni kaina wani lokacin sai taga dama take yarda dani.” Aikuwa sai ta fara tab’e baki tana so tasa kuka, rungume ta nayi ina rarrashin ta, granny kuwa sai dariya take mana, Iyami ta shigo da fidar ta da sauri ta sanya mata a baki ta kama tana tsotsa sosai, Dan kanta ta cire bakinta sannan ta fara daga hannu wai zataje gurin Iyami aikuwa Munnu tace”Baki isa ba kuwa kin bar hannunta da sauri ta karb’a ta a hannuna ta dauki towel dinta ta goya ta a bayan ta, mik’ewa nayi da sauri Iyami ta mik’o min duk abunda zamu bukata nata, nace “Granny zamu tafi gida.” Tace”To Ku gaida min Ummanku da kyau kuce ta kyauta.” Nace insha Allah kuwa. “Har waje Iyami ta rako mu tana d’agawa baby hannu ita kuwa sai dariya take bangala mata tana daga bayan Munnu.” Ganin rana ta kwalle nace dama zanga su Rambo da sun kaimu gida. Wata zuciyar tace min lallai Asma’u kina da samun shiga. Ni kaina dariya nayiwa kaina. A dai-dai sahu muka shiga nace”Munnu muje gida yau Umma taga baby inyaso sai ki tafi da ita ko.”? Munnu tace “Shikkenan muje.””‘ Wasa nake ma baby daga bayan Munnu ita kuma sai bangale min baki take, nace”Laa Munnu kinga har ta soma hakori wallahi. ” Munnu tace”Da gaske ne.” Nace sakkota ki gani.’ Aikuwa ta fara kokarin saukota tana dubawa, Kuka ta fara yi da alama tafi son goyon nace”Munnu mai da ita bayan baki ji yanda nake jin zafin Ku kanta Cikin raina ba.” Kokarin mai da ita take, naji kira ya shigo waya ta, hankalina na can gurin rarrashinta ban duba waye me kiran ba na d’aga wayar hade da sallama.
Kukan Sweet heart dinshi ne yayi masa sallama, ranshi ya kara b’aci a fusace! Yace.” Wai ke wace irin mayya ce ne? Meye alak’ar ki da baby da zakiji har gida ki dauke ta, OK naji kamar alamu kuna cikin abun hawa ne ana min gwajab-gwajab da yarinya tana kuka na rashin sabo. Maza ki mai da ita inda kika daukota tun wuri.”! Hannuna ne yake rawa bakina na motsi na rasa abunda zan ce masa, Munnu dake kusa dani duk taji abunda yake cewa, hannu ta mik’a min wai in bata wayar , domin in fidda kaina a gurin shi nayi saurin bata wayar ta karb’a a nutse tace”Yallab’ai barka da rana.” Jin muryar da bata Asma’u ba ya amsa da ” Barka dai wacece ke.”? Munnu ta tsorata jin muryar sa a kausashe!! Tace.” Munnubiya ce, dama umm! Dama…. Babanmu ne yace muzo humm nazo in d’aukar masa baby Aysha yana so ya ganta………. Sam bai gane Abunda take nufi domin shi har ga Allah ya mance da Kawun Mimi wato babban su Munnu, yace.” Ke! Bana son shashanci dallah!Ku mai da min da yarinya wato wayar ta baki domin Ku shirya karya ni sa’anku ne.”!? Cikin tsawa ya fad’i maganar! Nan Munnu ta kara daburcewa tace”Da gaske ne kayi hakuri Wallahi an turo ni daga gidan profesor Muktar Gyaranya ne ni ‘yar shi CE” sai da ta fadin sunan Profesor Muktar sannan ya tuna da Mutumin , kashe wayar yayi ba tare da yace komai ba .Munnu ta kalleni tana dafe k’irji tace”Bala’i wannan guy anyi masifafe irin sune suke rigima da matayen su akan ‘yaya gaskiya yana do son “yaya tab!!!!!!!