BABBAN YARO BOOK 3 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 3 COMPLETE NOVEL

Jiki a mace na bishi da kallo har ya shige dakin , kwanciya nayi a gurin ina zubar da hawaye ni kaina kukan da nake yi ya ishe ni..... Alwala ya dauro a gurguje ya futa k'arfe biyar da rabi ya dawo gidan kai tsaye dakin shi ya shiga ya sanya Riga da dogon wando jins shart din mai botira ce kuma bata da nauyi sosai saboda ciwon sa, a gurguje yake yin komai har ya kammala ya futo hannunsa rike da wayoyinsa yaji dad'i da ya futo ya tadda Asma'u ba tashi daga parlor baby dake bacci kan kujera ya mannawa kiss a kumatu yayi saurin futa saboda jin tsoron rigimar granny.. Yana futa Doh-doh da Ali na tsaye, take Ali ya bude masa mota ya shiga shima ya zauna kusa da doh-doh yaja motar suka futa daga gidan. Kai tsaye airport suka nufa.

[12/9, 11:02 AM] .: BABBAN YARO

79

Gabakid’aya wad’anda suke fad’a aji k’asar najeria sun hallara a d’akin meeting na fadar mai girma shugaban k’asa, Amjadu ne kawai mai k’ananun shekaru a cikinsu, duk sun girmeshi nesa ba kusa kai harda wandanda suka girmi mahaifin sa a cikinsu kuma dayawa daga cikin su k’abilu ne saboda haka suke komai cikin hikima da nutsuwa, duk wani bunkice mai girma shugaban kasa ya gama yi kuma ya tabbatar governor Alkanawi shine bashi da gaskiya duk wani dauki ba dad’i da ake da a jahar kano ya sani kuma shine ya haddasa ta, bayan yayi rantsuwa da alkur’ani gaban bainar jama’a zai yi kula da jahar sa zaiyi mulki tsakani da Allah amma ya karya doka, babu shakka a abunda yayi ba k’aramin Abu bane ya wuce gona da iri ta inda mai girma shugaban kasa yake ganin dole a hukunta shi, kuma mulki ya bar shi har abada domin a doka ta siyasar kasa duk governor da aka samu da cin amanar kasa za’a hukunta shi kuma ya bar siyasa har abada don haka ‘yan majalisa da hukumomin zab’e suka yanke shawarar juyin mulki ga mai girma governor Alkanawi domin su nawa jama’ar kano damar zab’o Wanda suke so ya mulke su daga nan zuwa wata biyu lokacin zab’e kenan…. Bayan nan kuma mai girima shugaban k’asa ya sanya dole hukumar Efcc ta tsaurara bunkice a kansa domin alamun rashin gaskiya sun bayyana a fuskarsa. Wannan shine hukunci da aka yanke ga mai girma governor Alkanawi… Bayan nan kuma Mai girma shugaban kasa da shauran k’ososhin k’asa suka jinjinawa Amjadu Young millionaire bisa ga NAMIJIN kokarin sa bisa kawo wa k’asar shi cigaba da jikinsa da kud’in sa da lafiya hak’ika idan k’asar najeria tana alfahari dashi da wannan aikin nasa. Nan mai girma shugaba ya sanya hannu a wata ta karda dake gaban shi, ya mik’awa na kusa dashi shima ya sanya hannu haka har sai dai mutum goma suka sanya hannu a wannan takarda kana takadar tazo gaban Amjadu shima ya karb’a ya sanya hannu ba tare da ya fahimci me takardar mecece ba…. K’arshe ta kardar ta koma gaban governor Alkanawi, hannu na rawa ya sanya hannu zufa suk ta jika jikinsa shaddar jikinsa duk ta jik’e yana sanya hannu wani soja dake tsaye kusa da shugaban kasa ya dauki takardar ya ajeta kusa da shugaba shi kuma ya had’ata da wasu takkadu ya rufe!!!

Ambassador Aminu Ahli shine ya kalli Amjadu cikin turanci yace.” Duk wani Abu da zaka yi a jahar kano Wanda kake ganin zai kawo cigaban kasa da talakawa mu zamu mara maka baya kaje kayi kanka tsaye zamu tallafa maka ni cikin asusuna na cire 50 Million’s na baka domin kaje ka k’ara farfad’o da harkokinka da company ka da suka rusa, take jama’ar gurin suka dinga ma Amjadu kyautar ta bangirma Shi kanshi shugaban kasa sai da ya bashi 50 Millions…..Innalillahi wa’ina ilahi raji’un wanin hanin ga Allah baiwa ne Amjadu Young millionaire Ni Binta na taya ka murna hak’ika babu abunda yafi gaskiya a duniya dad’i wani lokacin akan yi maka Abu domin a kuntata maka amma daga k’arshe sai ya zame maka alkairi, Fad’ar irin mak’udan kud’in da Amjadu ya samu a gurin b’ata lokacine. Mai girma governor Alkanawi kamar ya mace saboda bakin ciki.Take Sojoji suka tasa k’eyar Alkanawi suka futo dashi ‘yan jarida da suke zaune a reception suka mik’e dama duk abunda yake faruwa suna kallo ta CCTV Camera aikuwa suka yi caaaa! Kan alkanawi suna so suji ta bakinsa, ido jazur yace.” Sharrin shad’ain ne kawai da zugar mutane gashi sun kaini sun baro da k’arshe ina Neman afuwa ga al’umar jahar kano bisa ga abunda ya faru.”!! Daga haka yayi shiru idonsa yayi wani irin jaaa sojoji suka tasa shi a gaba.

To hakace ta kasance kan Amjadu manya manyan ‘yan jarida suka sanya shi a gaba dole sai yayi magana , babu yanda ya iya cikin turanci yace.” Hak’ika wannan ranar bani da kamar ta a duniya saboda Allah ya nuna min gaskiya ga gaskiya CE, Allah ya wanke ni bisa ga zargin da jama’a suke min Na tabbata ubangiji baya bacci kuma shi sharri d’an aike ne sunyi nufin cutata ubangji ya mayar da abun kansu saboda bani da hakki a Kansu nagode wa Allah da na tsalle ke wannan sharrin nasu kuma ina jinjina ga me girma shugaban kasa tare da mataikan sa hak’ika sun cancanci yabo da godiya a gare ni nagode k’warai da hallancin su a kaina.”
Abunda ya iya fada kenan ya wuce masaukin sa tare dasu doh-doh da Ali da yake cikin farin ciki da murna domin yana ganin dole ma ayi masa Karin girma gurin aikinsu saboda namjin kokarin da yayi.

Kafin kace kwabo garin kano ya hargitse da Sowa da murna gari ya hautsine da hayaniya kowa na fad’ar ra’ayin sa kan abunda ya faru, matasa dattijai duk sunji dadin wannan hukunci da shugaban kasa ya dauka dama sun gaji da mulkin Alkanawi don haka sai suka yanke shawarar tsayar da Amjadu a matsayin mai mulkar jahar su, take wasu suka futar da hoton shi a matsayin governor mai jiran gado nan da wata biyu suka dinga bin jikin gidaje da kan titina suna manna kasuwanni da shagunan mutane suka dinga manna hotonan amjadu a matsayin governor.

Duk abunda yake faruwa mun gani labarai Ya Aminu ya kirani a waya yana fad’amin min wai nasan abunda yake faruwa kuwa nace”Gani a labarai Ya Aminu ni bana son siyasa nan fa.” ! Yace.” Kiyi hakuri ki taya shi addu’a kinji ko.”! Ni dai shiru nayi kawai hankalina duk a tashe burina kawai ya dawo gida gashi na kira wayarsa ya kai sau ashirin bai d’aga ba….. Daki na shiga nayi kuka na mai isata na futo na tadda Granny ta jurawa TV ido inda suka nuno Amjadu lokacin da yake bayanin godiya a fadar me girima shugaban kasa. Ta kalleni idonta ya Tara k’walla tace”Zo kiyi min bayani me suke cewa ne naga sojoji sun kewaye shi, ga mutanan masu nacin tsiya sun kewaye shi da na’ura fadamin me yake ce musu jikina duk yayi sanyi..”!

Nace”Granny suna so ne ya zama governor kano babu wani damuwa sai Karin daukaka da ya samu kuma shine yake da nasara a tafiyar wannan ‘yan jaridar da kika ga sun kewaye shi duk murna suke taya shi suna so su ji ta bakinsa ne.”

Granny tace”Alhmdullahi Allah nagode maka dama nasan addu’a ta baza ta fad’i ‘kasa ba nasan ‘kato bashi da hakkin su amma ni kam bana sha’awar siyasar nan akwai zube war mutumci da dai su k’yale shi kawai.”

Nace”Wallahi nima haka granny bana so amma gashi tun bai dawo garin anji ta bakinsa ba jama’a sun fara fidda hotonan sa a matsayin d’an takara governor .” Granny ta sauke ajiyar zuciya tace”To Ubangji Allah ya dawo dashi lafiya muji ta bakinsa ni dai sanin da nayi wa ‘kato baya sha’awar siyasa ban sani ba ko yanzu.”

Shiru nayi mata zuciya ta nacan tunanin wani Abu. Mik’ewa nayi na koma bedroom dina waya ta na d’auka ina ‘kara kira shi cikin sa’a ya d’aga, ajiyar zuciya na sauke cikin damuwa nace”Abban baby sannu.”! Muryar shi bata futa sosai naji yace.” Yawwa ya gida babu matsala ko.”? Nace”Eh nayi ta kiran wayar ka kana gani ka’ki dagawa.” Ajiyar zuciya yayi yace.” Sorry sai yanzu wayar tazo hannuna mybe lokacin da kika kira tana gurin Doh-doh.”””” Shuru nayi yace.” Shikkenan ko.”!? Da sauri nace”Amma yau zaka dawo ko.”? Kai tsaye Yace.”A’a.”! ‘Kasa nayi da murya ta nace”Meyasa kasan fa ba lafiya gare ka ba.” Kwanciya yayi kan bed yana lumshe ido yace.” Menene damuwar ki da lafiya ta bayan idan ina nan d’in bakya kula ni. ” Naji wani sanyi na shigata jin yanayin yanda yayi magana nace”Baby na kuka abbanta.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button