BABBAN YARO BOOK 3 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 3 COMPLETE NOVEL

Tsakanin Amjadu da Jahid zumunci yayi k’arfi sosai Jahid ya aje aikin gomnati ya tsayawa Amjad kan harkokinsa na kasar waje abun sai son barka a lokacin ne kuma mahaifiyar jahid din ta tabbatar da cewar Asma’u mai k’ashin arziki ce a cewar ta da ta yarda jahid din ya aure ta da tuni shine governor????


Umma ta samu wani alhaji dake nan unguwar da suke yana da mata biyu da yara bakwai sosai zuciyarta ta amice dashi ta yarda zata aure shi mutumin yasan abunda yake yi a rayuwa kuma yana tsaye akan iyalinsa sosai don haka akayi d’aurin aure Umma tq zauna cikin gidanta duk ranan girkinta Alhaji Ayuba nan yake zuwa.

Gaba d’aya iyalan Umma sunji dadin Wannan auran da tayi domin shine cikar mutumci ta a halin yanzu Ya Aminu yana da yara bakwai saboda shekata hudu da suka wuce ya kara aure Munnu ta gama boran ta ta hak’ura Yanzu suna zaman Lafiya da kishiyar ta mai suna Amina itama Aminar lallaba Munnu din take ganin yanda Ya Aminu yake kafkaf da ita.


Alina kuwa yawan bariki da shaye-shaye da take yi yasa ta zama kwarkwasino ita kad’ai sambatu take yi wai itama matar governor ce.????

Hibbah kuwa wani tsohon saurayin ta ne ya ya amunce zai aureta bayan taga yi masa magajiya da koke kike ya amunce bayan ya kafa mata sharad’ai.

Rambo da doh-doh kuwa dama tuntuni suka yi aure lokaci guda Amjadu ya mallaka musu komai na rayuwa suna zaune da iyalinsu cikin gidan gomnati.


Sai da Amjad yayi shekaru takwas kan kujerar mulki sannan ya sauka ya d’ora Wanda yake ganin zai Dora daga inda ya tsaya a jahar kano an samu cigaba iri-iri an samu sauyi mutuka a jahar kano komai yayi sauki ma’aikata da yan kasuwa suna harkokinsu yanda ya kamata jama’a sai son barka suke yi masa tare da rokansa kan ya tsaya takarar shugaban kasa. Shi dai bai amsa musu ba kawai yana binsu da abunda suka zo masa dashi.

Rayuwa kenan komai yayi farko yana da k’arshe a yanzu Amjadu da Asma’u sun haifi ‘yaya shida hudu mata biyu maza sai baby take cikin ta bakwai Idan ba fada akayi ba babu Wanda zai ce itama ba Asma’u ce ta haifeta ba saboda kulawar da take bata ma tafi ta ‘yayan da ta Haifa a cikinta.
Rayuwar gidan Amjadu sai son barka nutsuwa da kwamciyar hankali a gidan babu maganar Karin wani aure a tare dashi duk ya aje gefe guda ‘yayan shi ne kawai a. Gaban shi itama Asma’u sai tayi da gaske sannan yake saurara ta gashi yayi mata mugun sabon da baza ta iya barinsa ba.


Suna zaune Innah Suwaiba tazo ta sanar dasu d’aurin aure Hafsa Amjad yayi mamaki sosai daga bisani yace.” Duk wani Abu da ake bukata innar tayi masa magana zai tsaya akan komai aikuwa haka akayi bukin Hafsa na zuwa yayi mata hidima sosai da sosai kana ya mallaka mata k’aton gida hade da motar hawa lallai babban goro sai magogin k’arfe. Kyautar manya kenan

Bayan bukin Hafsa ne muka fara shirye-shiryen kaisu Baby da Husaini saudia domin suyi karatu a can gaba ki dayamu har granny muka nufi kasa mai girma cikin aminci da yardar AllahAllah.

Alhmdullahi
Alhmdullahi
Alhmdullahi

Nan na kawo ‘karshen wannan littafin mai suna babban yaro ina ro’kon Ubangiji Allah ya yafe min kusakuraina abunda na rubuta dai-dai Allah kamu ikon amfani dashi baki ‘daya

Na gaishe ku real fans d’ina na gruop din babban yaro yawan Ku bazai barni in rubuta sunan Ku ba ni Binta umar hak’ika INA alfahari daku wallahi nagode sosai da sosai da hadin kan da kuka bani har na kawo karshen wannan littafin nawa ubangji Allah ya sada mu da alkairin sa ameen

Sai mun had’u a sabon novel dina mai suna

MASHAHURI

Taku……BintuUm@rAbb@le

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25

Leave a Reply

Back to top button