BABBAN YARO BOOK 3 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 3 COMPLETE NOVEL

Amjad yayi shiru na tsawon mintina biyar kana ya sauke ajiyar zuciya yace.” Wannan maganar da kayi ba gaskiya bace, babu shakka akwai abunda yake rufe Wanda ni dakai da su da kuma ita wife dina bamu sani ba, So nasan dai gidan da suke ciki cikin unguwar Gigiginyu na company ne Wanda ya mallakawa mahaifin ta tun yana raye had’e da shaidu da sa hannu yau shekara goma sha hudu kenan da rasuwar sa wannan shine abunda na sani, amma dole zan bukince kan maganar taka.”

‘Dan jaridar yace.” To babu komai Yallab’ai mungode mutuka da samun damar hallatar mu da kayi muna maka fatan alkairi a rayuwan ka Allah yayi maka jagora ya taya ka rik’o.” Amjad yace.” Amin suma amin.”

Nan D’an jaridar yayi sallama kana ya rufe kayan aikinsa…….. Amjadu tun a mota zuciyarsa take masa wani irin ciwo ranshi ya gama ‘abaci da abunda Asma’u tayi masa domin shi yana ganin duk laifin ta ne har akazo wannan jalli tabbas ya Dade da sanin mecece siyasa a rayuwa babu sauki a al’amarin duk inda zaka wa mutum baza ka futa ba dole sai ya San yanda yayi ya bata maka rai! Yana mamakin Gidan haya Asma’u suke zaune amma bata ta’ba fada masa ba dole ya nuna mata ‘bacin ransa..

12/12/2019
[12/11, 10:37 PM] .: BABBAN YARO
84

Sai wajan ‘karfe goma ya isa gida, Parlor babu kowa duk sun gaji sun tashi mussaman Hafsa da akaci Uwar kwalliya kamar matar gida ana jiran sa ya dawo ya gani k’arshe sai ta ‘buge da gyangyadi, gefe guda kuma ‘konar ta na yi mata zugi da rad’ad’i! Babu arziki taje ta kwanta, Inna ta bita a baya tana mita……granny kuwa Dariya take musu tare da fad’in kwaji dashi haka kurrum saboda daukar dala ba gammo Ku gayyato jiki Ku dawo gidan mutane nima barin gidan zanyi sai ku ‘k’arata Ku kad’ai.”

Asma’u kuwa komai cikin d’aki Tayi shi saboda yanayin da take tafiya babu sauki shiyasa ta kulle kanta Har baby ta gaji da kukan ta ta ha’kura…. Yini tayi babu abunda yake cikinta sai yughot da granny ta tilas ta mata dole tasha kwata-kwata bata jin test a bakin ta…. Sallah ma da k’yar! Tayi ta jikinta ciwo kawai yake yi cikin wannan halin ya shigo ya same ta.

Tana kwance kan dadduma da ta idar da sallahr Isha’i ya shigo ya same ta, sama-sama taji muryar shi ta bud’e idonta da suke cike da bacci…. Mik’ewa tayi zaune tana mutsike ido zatayi magana ya Riga ta ta hanyar fad’in.

“Tashi zamu yi magana.” Yanayin yanda ya fad’i maganar ne yasa ta bud’e idonta sosai tana kallon fuskarsa taga ya wani murtuke fuska, gabanta ya fad’i sunkuyar da kanta tayi ‘kasa.

A hasale yace.” A rayuwata na tsani rufa-rufa Asma’u a yanda na d’auke ki a zuciyata Sam bai kamata ki rufe min sirrin cikin gidan Ku ba yau da tun farko kin Sanar dani cewar gidan da kuke ciki ba naku bane ni mai mallaka mu gidane tun kafin azo ga jallin tonan asiri! Ina fatan kin saurari hirar da akayi dani a tashar freedom redio.”

Cikin rashin fahimta nace”Abban baby ban fahimci maganar ka nifa tunda ka futa ina kwance ina bacci in banda yanzu da na tashi nayi sallahr Isha’i wallahi ban saurari komai ba, kuma naji kana wata magana kamar ta cikin gidanmu ka Sanar dani kome ye.”!? Baba walwala a fuskar shi yace.” E maganar cikin gidanku ce ko bata shafe ni bane.”!? Ya fad’i maganar cikin gatse! Kallonsa nayi naga ya tsura min ido cike kamar wacce tayi masa sata!!! Gyada kaina kurrum nayi takaicin halayen sa ya soma damuna Sam shi baya daukar Abu da sauki! Sai yayi dakawa mutane tsawa! Mik’ewa nayi ba tare da nace masa komai ba. Na cire hijab jikina toilet na nufa cikin yanayin tafiya kamar me koyo….. Muryar shi a sama! Yace.” Ko bakya ji ne wato ina miki magana kina tafiya kamar wani sa’an ki, ki bar ganin jiya na kwanta dake Wallahi kika raina ni sai na baki mamaki.”!
Cikin fada yake maganar

Hawayen dake kokarin zubo min nake mayar wa a zuciya nace wai dame zanji ne Da bala’in sa ko da haibaicin da Innah sa ta yini tana yi min ko kuma da ciwon jikina zanji…. “Abban baby Allah ya baka hakuri maganar da kake wallahi ban San da ita ba.” Toilet din na shige ban San saurari abunda zai ce min ba… Ruwan zafi na hada na kara shiga tsawon minti goma sha biyar na futo daga ciki, wanka nayi tsaf na futo daure da towel na rofu jikina da wani jin wani irin sanyi na shiga ta Nasan zazzab’i ne har yanzu bai tafi ba.

Yana zaune inda yake na jikina babu kwari na lalubo kayan bacci cikin Kayana gaban dressing mirror na tsaya na shafa mai sama-sama humrar gurin aunt Hauwa na shafe jikina da ita sannan na zura kayan baccin masu Riga da wando rigar mai siririn hannu ce shi kuma wando iya gwiwa yaje gashin kaina na tubke sai na d’aura d’ankwalin abaya a kaina… Kai tsaye bed din na nufa…. Amjad da tunda ta futo daga toilet yake binta da wani irin kallo sai da yaga ta juyo ne yasa ya dauke kansa da sauri hade da kara hade fuskar sa, sai da ya bari ta kusa karasowa ya sanya k’afarsa ya tade tata ta fado kansa

‘Dankwanlin a bayar ya cire ya jefar kasa ya rike tarin gashin ta da tayi parking dinshi tsakiyar ka, jansa yayi da k’arfi yace.” Ina a matsayin mjinki kina kin daukar magana ta da muhimamci Asma’u magana ta dake ta farko ta k’arshe shine ki kira Yayan ki Aminu cewar insha Allah gobe yazo ina Neman sa maganar zaman gidan haya ta ‘kare in dai ina Raye a duniya.”

Cikin kuka nace”A rayuwata na tsani mutum mai saurin daukar zafi da rashin fahimta nifa Wannan maganganun naka Sam ban fahimce su ba kamata yayi daga shigo sai ka warware min kome cikin ruwan sanyi amma kazo kana tayi min masifa ko tunanin halin da nake ciki baka yi.”

Sassauta rik’on gashin yayi yace.” Kece kika jawa kanki da ki’ki tsayawa ki saurari maganata.” Nace’ta yaya zan saurare ka kazo kana yimin hayaniya.!” Duk ina hawaye nake maganar tsira min idonsa yayi yana kallona yace.” Kiyi kokarin hana hawayen ki zubowa bana son ganin su.” Jikina na fuzge da k’arfi nace”Ni ka k’yaleni ko waye yace maka haya muke yi a gidanmu karya yake yi.”

Yace.” Nine makaryaci kenan.” Banza nayi masa na shiga cikin bargon ina share hawaye…. Mik’ewa yayi ya futa daga d’akin, ni kuma na shiga tunanin maganganun shi.

Amjad na futa parlor ya tadda Hafsa a zaune ta k’urawa kofar dakin Asma’u ido, cikin mamaki yace.” Ke Lafiya me kike yi bakiyi bacci ba.”? Furgitt Hafsa ta dawo hayyacin ta. Sai ta hau ya ‘ke da kame-kame yace.” Tashi kije ki kwanta dallah.” Cikin tsare gira yayi maganar! Hafsa ta mike simi-simi ta shige daki gwiwar ta duk ta sage, Amjad yana yi mata mugun kwarjini a rayuwar ta ta inda ko muryar shi taji sai taji gabanta ya fad’i kusa da mahaifiyar ta ta kwanta cikin sarewa dà al’amarin shi ta fashe da kuka me cin zuciya.

Bedroom dinshi ya bude ya shiga yana Jan tsaki in banda abun Innah yana da Asma’u a gidan sa me zaiyi da wata Hafsa a halin yanzu Sam babu maganar aure a tare dashi domun yana ganin Asma’u shi ta Tara dukanin abubuwan da yake so matar auran shi ta kasance dasu.
A gurguje Yayi ya wanka yana tunani k’amshin jikin Asma’u da yanda yake jin wani sihirtaccan kamshi na futa daga sumar kanta. Lumshe idonsa yayi ya nufi d’akinta cikin karsashi da k’warin gwiwa.
[12/12, 10:04 AM] .: BABBAN YARO
85

Cikin bargon ya shiga yana laluben ta… Hannunsa na ture lokacin Dana ji yana ‘kokarin kama Brest dina tsigar jikina duk ta mike saboda yanayin jikinshi sanyi ruwan da yayi wanka take na fara sauke ajiyar zuciya.. Birkitoni yayi muka fuskanci juna dashi ya kura min idanunsa masu mugun kashe min jiki sai wani lumshe so yake yana cizar lips d’insa, nagane shi mutukar zai yi futuna zai dinga lumshe min ido yana lasar leb’e kamar wani yaro…. Cikin wani irin voice yace.” Ki d’auka a ranki kin zama ni na zama ke a duniya bani da wacce zan kawo wa matsalata sai ke ina so kema idan wani Abu na damun ki naki ko na cikin gidanku ki fad’a min insha Allah zanyi iya iyawa ta akai, ina fatan kin fahimta.” Duk wannan maganar da yake yi yana yi yana shafa min jiki da hannunsa hade da goga min fuskarsa a wuyana, bakina na rawa nace”Nima ban ‘b’oye maka komai ba wallahi abunda kake tuhumata dashi ban sani ba ina jin bayan barina gidan abun ya faru, amma mungode sosai da wannan karamcin naka ubangji Allah ya kara maka suttura.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button