BABBAN YARO BOOK 3 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 3 COMPLETE NOVEL

Wasu matasa ya sanya suka dauko Rambo suka sanya shi a mota Rambo saboda tsabar galabaita da yayi Sam ya kasa magana sai gumi yaki ga jikinsa yayi bud'u-bud'u!!! Shi kanshi Amjadu din Jikinsa bud'u-bud'u da k'asa saboda tumurmuson da sukayi a kasa!


 Yini nayi cikin zullumi da fargaba da fad'uwar gaba misalin biyar da kwata muna zaune a parlor ya shigo gidan, sallamarshi muka amsa dukaninmu muka bishi da kallo, wata irin fad'uwar gaba ta rikito min ganin shi cikin jini a jiki duk k'asa!! Salati nake a zuciya ta na mike zumbur!! Granny kuwa ai kafin ya karasa shigowa ta riske shi bakin kofa ta fashe da kuka tana fadin "Dama fad'uwar gaban da na yini ina kenan innalillahi wa'ina ilahi raji'un."!!! Kuka take sosai ta rirrike shi kwata-kwata ta hanashi magana "Hatsari kukayi kome!? Ooh ni jikar mutum biyu, Asma'u kinga abunda na yini ina fada miki ko watak'ila tunanin abunda kikayi masa ne ya sanya a ransa don Allah ki kula da mijin ki." Yanda Granny ta hakikance tana magana ne zaka fahimci ba a cikin hankalin ta take ba kuka take yi ya samu ya shige bedroom d'insa ba Tare da yace mana komai ba.

Kallo na bishi dashi jikina na rawa!! Granny tace”Kinyi tsaye a gurun baza ki bishi kije meya faru ba.”!? Kafin ta rufe baki har na bud’e d’akin na shiga. Yana tsaye tsakiyar dakin yana kokarin cire rigar shi na karasa gurin da sauri! Nace”Abban baby men….. Meya faru wai.”!!! Shiru yayi min. Yana cire rigar shi na fasa wani ihu! Ganin naman kirjin shi a waje fatar ta kwailaye jini jazur Ashe suit din jikinsa shine yake tsane jinin yana cire wa ya fara kwatanya a jikinsa yana d’iga k’asa.” Hawaye shab’e-shab’e a fuskata nake nuna gurin da hannuna na kasa cewa komai!

Wuce ni yayi zai shiga toilet na bishi da sauri rike hannunsa nayi nace"Kana ganin yanda jini yake zuba a jikin ka ko ka damu abban baby ba a wasa da rai kaji tausayin tsuhowa kaji tausayin baby wacce bata San meye rayuwa ba, don girman Allah ka daina wasa da ranka."!!! Cikin dauriya yace." Yanzu me kike so ayi miki."!? Ina zubar da hawaye nace "Ka bari a duba gurin nan kar ya zama matsala."!! Murmushi yayi me ciwo yace." Zanyi dressing gurin da kaina kar ki damu." Girgiza kaina nayi nace"Ka Bari a kira Jahid ya duba sosai wai kai baka ganin yanda jini yake zuba ne."!!! Kallonta yake cike da mamaki ganin yanda take hawaye duk ta tada hankalin ta yace." Mik'o min wayata gata can." Da sauri na mike na d'auko.

Jahid ya kira a waya tun kafin ya fada masa komai yace.” Ganina akan hanya Aboki duk ina da labarin komai innalillahi wa’ina ilahi raji’un. “!!? Daga haka ya kashe wayar tasa……shuru dakin yayi, k’irjinsa na zubawa ido inda ciwon yake ina ji kamar a jikina na mike da sauri ina neme-neme a dakin dankwalina na cire da sauri na d’ora kan ciwon sam bana son gani.

Wani irin d’as!d’as!d’as! K’irjinsa yake hakan ya tabbatar min Yana cikin tashin hankali da fargaba na kalleshi sai akayi sa’a shima ni yake kallo mun fi minti uku muna kallon juna daga bisani nace” Abban baby meye faru don Allah ka fad’a min. “!?

 Idonshi tsaye akaina yace." Tsautsayi ne kawai amma dai da da karar kwana da sai dai kuji mummunar labari." Naji fad'uwar gabana ya karu "Hadari kuka yi da mota."!? Girgiza min kai yayi alamun a'a! " To menene. "!? Nafada Muryata na karkarwa." Kai tsaye yace." Magauta ne suke so suga bayana."!! Kuka nasa nace"Allah ya fisu kaima ka daina biye musu idan naso kake mu rasaka ba, kamar yanda muka rasa Mimi." Shiru yayi mata kawai yana kallonta had'e da mamakinta sosai lallai yau yaga tsantsar sonsa a kwayar idonta.

[12/8, 1:16 PM] .: BABBAN YARO
78

Wallahi har ga Allah a lokacin na manta ‘yar tsamar dake tsakaninmu dashi, hankalina ya tashi da yanda naga jini na zuba a jikinsa kuma bai damu ba.. Dankwalina Dana sanya a gurin ya jike da jini na sanya hannuna na daine gurin hawaye na kwaranyo min, yace.” Wai kukan me Kikeyu ne.”? Rasa abunda zance masa nayi kuma ban fasa shashshekar kukan ba, ina jinsa ya sauke ajiyar zuciya yace.” To idan kuma akace miki na mutu yaya zakiyi ? Ki daina min wannan kukan bana so kina k’aramin zafi cikin zuciyata domin zubar hawayen ki a gabana babban tashin hankali ne.”

Shuru nayi masa dai ina kokarin maida hawaye na gefe guda kuma ina tunanin maganar da da yake cewa kukana nayi masa zafi cikin zuciyar sa…… 10 minutes Jahid ya shigo gidan iya parlor ya tsaya ya kira wayar Amjad din. Mik’ewa yayi zai fita na bishi a baya cikin mutuwar jiki. Jahid nata zayyanewa Granny abunda ya faru, ita kuma sai salati takeyi cike da tu’ajubi tace”Shikkenan da da karar kwana sai da akawo mana gawar sa, innalillahi wa’ina ilahi raji’un.” Kuka ta fashe dashi sosai da taga Amjad din ya futo duk jini a jikinsa ta dinga fadin innalillahi wa’ina ilahi raji’un.”

Zama yayi kusa da jahid din dake kokarin futo da kayan aiki yace.” Granny please wannan abun fa bana kuka bane ko na tashin hankali don Allah kiyi min addu’a na yarda dukkanin abunda ya samu bawa daga Allah ne don Allah Ku daina daga hankalin Ku.” Tace”Dole ne nayi kuka k’ato kai kadai nake gani a duniya inji dad’i narasa iyayan ka kaima bana so na rasa ka.”!! Girgiza kansa kurrum yayi, Jahid ya soma yi masa dressing din gurin ciwon yana kara kwantar wa da granny hankali.

Shuru parlor yayi minti goma ya kalleni dake tsaye kanshi, kasa nayi da kaina zuwa yanzu na fara dawowa nutsuwa ta yace.” Kunna min TV nan .” Cikin sauri naje na kunna masa kamar yanda ya umarce ni….. “Mik’o min romot d’in mu gani.” Yafad’a yana Dan ciji lips d’insa saboda yanda yake jin zafin ciwon Ga Jahid ya dage sai wanke gurun yake da magani.

Hannuna rike da romt din na karasa gurin na mik'a masa tare da matsawa daga gurin domin ji nayi tsigar jikina na wani irin tashi gani Kwata-kwata bana son ganin tashin hankali a rayuwata.  Tashar *NTA NEWS* Ya kunna dai-dai lokacin da suke yin labaransu na k'arfe shida cikin turanci suke fad'ar abunda ya faru a jahar kano tsakanin governor kano d'in da Amjadu *Young millionaire* hoton governor da Amjad  suka hasko lokaci guda suka cigaba da hasko badak'alar da ta faru a rujajjam company inda mutanan mai girma governor suka dinga b'arna da sakin harbi hade da tiyagas, da inda suke kokarin k'watar manager , kai har dambe  tsakanin Kumurci da Amjadu sai suka hasko dukanin abunda ya faru da inda Kumurci ya dab'awa Amjadu wuk'a a k'irji. Da kuma lokacin da suke dariya har suka samu nasarar guduwa bayan sun jikkta mutane tare da ragargaza gilashin motar Young millionaire. "

Tsakanin ni da granny ban San Wanda yafi wani tsurewa ba ganin hatsaniyar da ta faru lallai kam da da k’arar kwana da sai dai a kawo mana gawarshi. Iyami ce ta shigo da baby a hannunta, karb’ar yarinyar nayi na rungume a jikina ina kokarin danne hawayen da suke kokarin zubo min ayya nawa nake cikin zuciyata da ya mutu Shikkenan baby ta zama marainya gaba da baya zata taso bata San iyayen ta ba, naji tausayin tsohuwar data kwallafa ranta a kanshi…. Gabana ya fad’i cikin zuciya ta nace idan ya mutu ke wane halin zaki shiga? Ni kaina nasan ina masifar son guy mussaman yanzu na San mallakina ne kawai ina share shi saboda sanin halin shi, nake tunanin gwara in kama kaina tun wuri amma ina ganin dole in sauke nawa in kula dashi idan ba haka ba abun zai yi masa yawa ko ina babu sauki duniya ga uban makiya Allah ka tsare min shi. Abunda nake fada kenan cikin zuciyata.

Baby ta dinga yunk’urin sai ta sauka taje gurin shi ina riketa Hannunsa guda ya miko min wai in bashi…. Nace”Ta yaya zaka iya daukar ta sai ta dauje maka ciwon .”” a hankali yace.” Ke dai ki bani ita nace, kar ki bari tayi wannan kukan ranki zai b’aci. “! Gurin na karasa muka had’a ido da Jahid kunya ce ta kamani don Wallahi shaf na manta ban gaishe shi ba, nace” Jahid munyi lafiya yasu Salim.” ? Murmushi yayi kad’an yace.” Lafiya lau Salim nan lafiya zan kawo miki shi.” Nace”To ina jira.” Daga haka nayi shiru ina mik’a masa baby. Kallon fuskarsa nayi naga ta sauya karb’ar baby yayi ya rike ta da hannu d’aya, yarinyar ta dinga kokarin kai hannunta gurin ciwon tana so ta jawo bandejin da Jahid yake nad’a masa a gurin. Granny tace”Dama ganganci ne yasa ka karbeta kasan yanzu hannunta yayi ido komai kamawa take yi.”
Wasa yake da baby din bama ya sauraran abunda granny take fad’a. Duk hankalinsa na kan ‘yar tashi.


A ranar kiran gaggawa ya samu governor dashi da Amjadu daga fadar shugaban kasa, hankalin shi ya kai k’oluluwar tashi yasan halin mai girma shugaban kasa da zafi da daukar Serious ba tare da b’ata lokaci ba ya nufi babban birnin tarraya abuja, cike da ta tsantsar tashin hankali da nadama…. Lokacin da sak’on shugaban kasa ya samu Amjadu sam ba nuna wata fargaba ko tashin hankali ba, tabbas yasan gurin da zasu je ba gurin wasa bane dole yaje da shirin sa duk wasu matakan kare kansa ya tanade su hade da shaidu, yana jin jiki ya kira doh-doh a waya Wanda yake can asibitin malam Aminu yana kula da Rambo yace.” Yazo yana Neman sa, a daran aka kira Ali wannan d’an jaridar shima Dole zai zama shaida a gurin duk da ba kutu zasu shiga ba amma yana ganin tafiya dasu tana da amfani…… Nan parlor muka kwana ni dashi da baby domin babu yanda banyi dashi ba kan ya tashi mu koma daki yak’i hakanan na zaune kasan kafet shi yana saman kujera a kwance baby gefan hannun shi inda babu ciwon ko kadan ban rintsa ba kamar yanda bai rintsa ba.

K’arfe hudu na asubah ya mike yana kokarin dauke baby a jikinsa mik’ewa zaune nayi da sauri na dauke baby na kwantar kan kujera, ya mike zaune, hannun shi na rike hade da tsira masa ido… A dake yace.” Menene. “!? Hawaye ne suka fara sintiri a idona nace” Wallahi ina jin tsoron zuwan ka abuja nan.”

Tsaki ya ja k’asa-k’asa yace.” Jiya kin kwana kina kuka ga rashin barci kan abunda bai shafe ki ba, na fad’a miki tun jiya wannan kukan da kike yi bashi da amfani Sam na tsane shi.”
Hannunsa na saki na hade kaina da gwiwa sosai nake zubar da hawaye ni kadai nasan irin fargaba da take damuna akan wannan al’amarin gani nake yi idan ya tafi kamar yanda ya fada jiya za’ muji mummanan labari!!!

Shashshekar kukan ta ne ya dame shi! Dafe kansa yayi ya yunk’ura ya mike tsaye cikin k’arfin hali ya tsuguna gabanta tare da d’ago kanta suka fuskanci juna….. Kallon-kallo muke ni dashi!! Ga hawaye shab’e-shab’e a fuskata…. Fuskarsa yake matsowa da ita, nayi saurin rintse idona hawaye suka zubo, harshen shi naji kan kuncina yana lashe ruwan hawayen. Nayi saurin bude idona ina kallonsa shima ni yake kallo kuma bai fasa lashar fuskata ba. Naji wani irin Abu a jikina lokacin babu abunda nake so illah in jini a jikinsa babu hali da babu ciwo da babun abunda zai hana na rungume shi. Sai da ya lashe ruwan hawaye na tas! Sannan ya mike a nutse ya shiga toilet din parlor.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button