BABBAN YARO BOOK 3 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 3 COMPLETE NOVEL

13/12/2019
[12/13, 10:27 PM] .: BABBAN YARO
88

Haka suka tashi da safe ita dashi kowa na d’acin rai! Tunda ta gaishe shi bata ‘kara kula shi ba shine ma yake janta da hira tana basar dashi haka suka had’u suka yi breakfast har shi uban gayaar ya d’ora baby a cinyar sa sai shirme suke yi shi da ita ya koma kamar wani ‘k’aramin yaro yana biye mata sai faman dariya suke kyalkyalawa.

Granny bayan tagama karyawa mi’kewa tayi ta nufi d’akin da take suka bita da kallo Sam basu kawo komai ba, minti biyar tsakani sai gata ta futo cikin shiri ta yafe jikinta da mayafi kirif tayi hanyar futa ba tare da tacewa kowa komai ba.”

Da sauri na mike naje na tari gabanta ina marairaice fuska nace”Granny ina zakije inace jiya mun gama magana dake kince kin fasa tafiya.”

Jin abunda Asma’u take fada ne yasa shi mik’ewa da sauri ya karaso gurin yana tambayar menene.”?

Granny tace”Dama yau na shirya tafi gidana.” Amjad ya ‘boye dariyar da take ‘kokarin subce masa yace.” Wani abu aka miki a gidan. ” ? Gyada kai Tayi tace”Ba’ayi min komai ba kawai zan baku guri Ku wataya.”

Dariya yasa ya kama hannunta guda yace.” Rayuwata baza ta tafi dai-dai ba idan babu ke a gidan uwargidana ta kaina idan mun yi miki laifi ki hak’ura. “

Granny tace” babu laifin da kuka yi ‘k’ato nice naga ya dace in tafi.” Amjad yace.” Ni kuma ban sallame ki ba sai kiyi hakuri idan kuma kika ce dole sai kin tafi kin San kina futa zan sanya a saki karnuka sai muga ta inda zaku tafi.”

Cikin sababi! Granny tace.” Sai kace zaman nawa dole ne iyi yanzu nace nafi son zama a gidana nagaji da jin iface-iface! Cikin dare.”

Saurin barin gurin nayi ina mamaki tsohuwar ko me take nufi oho.! Ina Juyawa Inna Suwaiba ta watsa min mugun kallo tana gyada kanta… Bedroom dina na shige ina fadin”Allah Yayi min gatangar k’arfe da sharrin ki.”

Kwanciya nayi kan bed din ina sa’kawa da kwance wa har bacci me nauyi ya d’auke ni…..a takaice dai ban San sanda su Inna Suwaiba suka bar gidan ba domin bacci na shirga sai daf da sallahar azahar na tashi a gurguje nayi wanka da alwala na futo simple make up nayi na zura doguwar Riga mai hula humra na shafa a jikina sannan na hau dadduma na tada sallah

Ko da na futa parlor granny kad’ai na gani zaune suna hira da Iyami na saki wata irin ajiyar zuciya mai sanyi, yanzu na tabbata Innah Suwaiba sun bar gidan cikin zuciyata nace mata ‘yar bala’i kurrum tazo zata d’aga mana hankalin gida. Zama nayi cikin kujera cikin sakin fuska na dinga sanya musu baki a hirar tasu kafin mu zauna cin abunci granny kam cewa tayi Iyami ta had’a mata ta kawo mata inda take domin baza ta iya zaman daining ba. A cewar ta ‘kafar ta tsami take ni da Iyami muka sanya mata dariya… Yanzu wani irin nishadi nake ji a zuciya idan na tuna cewar me takura min tabar gidan wallahi d’an zaman da Tayi na kwana biyu jina nake yi a takutey gefe guda kuma idan na tuna al’kawarin da Abban baby ya daukar mata sai gabana ya dunga fad’uwa.


Al’amura sun tsananta ga me girma governor gobe wato Amjadu AbulAbbas mainasara Yanzu kwata-kwata baya zama a gida kullum suna can suns taron siyasa ya tsai da mataimakin sa Engineer Jabir Hamid shine ya yarda da alkairin sa da kulawar sa kana da yanda ya tsaya tsayin daka akan jam’iyyarsu tabbas Engineer Jabir Hamid tsohon d’an siyasa ne Wanda yake da a ‘kida Amjad tun yana da ‘kananun shekaru yasan da mutumin domin. A haife ya haife shi idan kididdiga ma za’ayi ya girmi mahaifin shi, to dashi ya yarda ra’ayin shi shi jama’ar jahar kano suke bi lokaci guda al’amura suka dai-dai ta yayin da ‘yan bakin ciki da hassada suka ‘kara yawaita sharri kullum yin sa ake yi ga amjadu amma yak’i tasiri jama’ar jahar kano sun Riga sunyi nisa a ‘kaunar sa, Nima nace tabbas zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shawo sai yayi Amjadu sai dai fatan alkairi

Kullum zai dawo gida cikin dare a gajiye amma saboda tsabar futuna komai baccin da Asma’u take yi sai ya turme she ta ita kuma tayi ta masa sangarta da shagwab’a salo-salo abunda yake ‘kara gigitashi kenan yake ‘kara dilmiya cikin kogin sonta, sun ringa sun saba ita dashi kullum sai sunyi sex kuma basa tab’a yin sau d’aya a rana duk rintsi kafin ya futa sai ‘kara wani da safe ko da asubah…..aikuwa Asma’u tayi wata irin lafiyayyar ‘kiba fatar ta murje sosai Sam bakye ce mata baka saboda tana samun kulawa kullum oga nayi mata feshi tayi ‘kiba sosai ta samu Lafiya ita dashi duk sun mance da wani zancan Inna rayuwar su suke yi tsaftacciya….Asma’u da kanta ta fuskanci tana da ciki domun wata biyu kenan bata yi al’ada ba kunya ta hanata fad’a masa, shi kam gogon NAKU hankalinsa ya d’auke gurin harkokinsa Sam bai fahimci komai ba tabbas yasan dai Ta ‘karayin Sugar ta inda Idan yana sex da yake iface-ifecn da ya saba Wanda Granny take ‘k’orafi akai Asma’u ce take rufe masa bakin sa wani sa’in amma Amjadu hauka ne kurrum baya yi mata a gado.


Granny ce ta fahimci abunda yake faruwa aikuwa farin ciki duk ya isheta shiga futa d’ari sai tayi zancan ciki motsi kad’an Asma’u zata yi zata hau fad’a wai ta dinga yin komai a hankali da nutsuwa ita dai sai dai tayi dariya kurrum…cikin wannan yanayin za’be yazo gari ya hargitse ya hautsine ko ina ka duba police ne sosai aka sanya matakan tsaro a garin na kano, ana ya gobe za’be Alhaji Hashimu da Yarshi Hibbah suka shiga gidan redio domin ayi hira dasu.

Dama tun safe ake maganar cewar za’ayi hira da tsohon d’an kasuwar nan Wanda yaga jiya yaga yau a fannin kasuwanci wato Alhaji Hashimu mai citta mutanan gari suka dinga dariya suna fadin ko me zai fad’a oho kowa ya ‘kaugauta lokaci yayi ya saurari hirar har shi kanshi Amjadu wayar sa na hannun Rambo yana jiran lokaci ya kunna masa.

Alhaji Hashimu mai citta ya zage yana shirya karya kan Amjadu har da fad’in cewar mahaifin sa da bashin mutane ya mutu kuma bayan haka shi ba d’an gari bane yazo gari zai mulke su yana da kyau jama’ar kano su farka kar su zab’i bara gurbi Wanda zai tarwatsa jahar kano daga k’arshe ya koma garin su na gado maganar ‘k’arshe da ta girgiza mutane shine abunda Alhaji Hashimu yace.”Amjadu yayi wa yarshi ciki gashinan wata hudu a jikinta suna da shadar haka koda jama’ar gari zasu karya ta…… Wannan zancan ya jawo kace nace a garin inda kowa yake fad’ar ra’ayin da akan Amjadu dim wasu suna ganin hakan zata iya faruwa tunda dama tsohon Dan bariki ne yana da hotel har guda biyu tabbas ba asan iya adadin matan da ya lalata ba……wasu kuwa a take suka karya ta maganar tare da cin alwashin sai sun ragargaji mai citta shi da shegiyar yar tasa sai ta fada musu Wanda yayi mata ciki da bakinta, a rake su ka dauki gorori cikin shirin ko ta kwana suka nufi titin gidan redio na Komai da ruwan ka lamfu suka yi daga nesa suka hango motar Mai citta ta futo daga cikin gidan redio aikuwa suka futo da gudu suka tsaya kan titi… Cike da tsoro mai citta ya ci birki hankali a tashe! Yake kokarin bude motar ya futo Hibbah kuwa har ta saki futsari a wando tsabar furgita da tayi kafin su Ankara suka ji taratsatsa!!!! Gilashin motar ya fashe d’aya daga cikin matasan ne yake dukan gilashin motar yana fad’in “Futo tsohon banza da shegiyar kilakin ‘yarka ogon namu zakuyi wa ‘azafi duk bakin cikin Ku k sai ya zama governor!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button